ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Tattauna Da Boko Haram Don Sako Mana Mutane 416 Da Aka Kama – Ƙungiya A Borno

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Boko Haram

Ƙungiyar Borno South Youth Alliance (BOSYA) ta buƙaci gwamnatin tarayya da manyan jami’an gwamnati su shiga tattaunawa domin ceto mutane 416 da aka sace a Ngoshe, Jihar Borno, bayan da aka fitar da bidiyon da ke nuna cewa har yanzu suna raye.

A cikin wata sanarwa da shugabanta, Samaila Ibrahim Kaigama, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce ta shiga tattaunawa cikin sirri da masu garkuwa da mutanen bayan farmakin da suka kai wa yankin. Ta ƙara da cewa an tabbatar mata cewa mutane 416 na nan da rai, saɓanin wasu rahotannin da aka riƙa yaɗawa a baya.

  • EFCC Ta Bankaɗo Makarantar Koyar Da Damfara A Intanet A Abuja, Ta Kama Mutane 31
  • Arsenal Ta Kammala Ɗaukar Riccardo Calafiori Daga Bologna

Ƙungiyar ta bayyana kanta a matsayin muryar matasan Kudancin Borno, tana mai cewa za ta ci gaba da bin dukkan hanyoyin da suka dace, ciki har da sasanci da kira ga gwamnati domin ganin an sako waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.

ADVERTISEMENT

Sai dai BOSYA ta jaddada cewa ba ta goyon bayan ta’addanci ko garkuwa da mutane, amma tana ɗaukar wannan mataki ne domin ceton rayukan al’ummar yankin. Ta kuma buƙaci shugabanni ciki har da Bola Ahmed Tinubu, Kashim Shettima da Sanata Mohammed Ali Ndume su ɗauki matakin gaggawa.

Ƙungiyar ta kuma yi nuni da yadda aka taɓa samun nasarar sako mutane a jihohin Sokoto, da Zamfara, da Katsina da Kebbi ta hanyar shiga tsakani da wasu mutane kamar Ahmad Gumi, tana mai kira ga a nuna irin wannan himma a lamarin Ngoshe, tare da buƙatar haɗin kan ƙasa da ƙasa domin tabbatar da sakin dukkan waɗanda aka sace.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Boko Haram
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
INEC Na Yunƙurin Hana Mu Fitar Da Ƴan Takara – ADC

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.