ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Na Yunƙurin Hana Mu Fitar Da Ƴan Takara – ADC

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
INEC

Jam’iyyar ADC ta nuna damuwarta game da abin da ta kira yunƙurin hana ta fitar da ƴan takara a zaɓe 2027 daga ɓangaren hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Wannan na zuwa ne yayin da INEC, a ranar Laraba da ta gabata, ta shaida wa ADC cewa ba za ta sa ido kan babban taronta na ƙasa ba, wanda ya fara tun daga ranar 7 ga Afrilu 2026, tare da tantance masu neman muƙamai, har zuwa lokacin yanke hukunci kan ƙarar da ke gaban babban kotun tarayya.

  • INEC Ta Gargaɗi Jam’iyyu Kan Gudanar Da Babban Taro Ba Tare Da Sanin Ta Ba
  • Rikicin PDP: Kotun Koli Ce Kadai Za Ta Warware Lamarin Ba INEC Ba –Bangaren Turaki

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya kuma kare shawarar hukumar zaɓe na rashin sa ido kan gudanar babban taron jam’iyyar a ranar Jumma’a, inda ya yi gargaɗin cewa yin watsi da bin shari’a na iya haifar da mummunan sakamako, wanda jam’iyyun siyasa na iya rasa nasarorin zaɓe saboda rashin bin doka.

ADVERTISEMENT

Duk da haka, jam’iyyar a ranar Juma’a ta ce aikin zai ci gaba duk da abin da ta kira haramtacciyar ayyukan INEC, tana bayyana matsayar hukumar zaɓe a matsayin wasa da umarnin kotun ɗaukaka ƙara na kiyaye matsayin da ake ciki, wanda ke nufin rashin mutunta kotu da ƙoƙarin bin hanyoyin da suka saɓa wa doka da kuma wace gona da iri wajen gudanar da aikinta.

Sai dai kuma a ranar Alhamis, shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Sanata Daɓid Mark, yayin da yake jawabi a taron manema labarai a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso da Rotimi Amaechi suka halarta, ya buƙaci shugaban hukumar zaɓe ya yi murabus nan take ko a kori shi da kuma dukka kwamishinonin zaɓe.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

Jawabinsa ya biyo bayan matakin da INEC ta ɗauka na cire sunayen kwamitin gudanarwa na jam’iyya ADC da Sanata Daɓid Mark ke jagoranta daga shafinta na intanet da dakatar da amincewa da dukkanin ɓangarorin masu hamayya a jam’iyyar, har sai an kammala shari’ar shugabanci da ke gudana a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya sa mata hannu, ta bayyana cewa a tsakiyar wannan rikici da ke tasowa shi ne matsayin INEC na cewa ba zai sake karɓar kowanne wasiƙa daga ADC ba har sai an yanke hukunci kan shari’ar da ke gaban babban kotun tarayya.

Abdullahi ya ce, a bayyane lamarin na iya bayyana kamar na tsarin aiki ne, amma a zahiri, yana haifar da rikici kai tsaye kuma mai haɗari ga jaddawalin dokar zaɓe ta shekara ta 2026, wadda ta shimfiɗa ƙa’idoji ciki har da wajabcin sanarwa na kwanaki 21 ga jam’iyyun siyasa na cewa dole ne su kammala muhimman ayyuka na zaɓe.

ADC ta ce ta hanyar shigar da lamarin da ke gaban kotu da kuma yi wa doka karan tsaye, hukumar zaɓe ta raunana kanta kan aikin da take iƙirarin karewa.

Mai magana da yawun jam’iyya ya ce abin da ya fi damunsu shi ne, cewa wannan matsayin ya saba wa yadda INEC ta gudanar da ayyukanta a baya da kuma yadda doka ta tanada.

Ya ce wannan hukuma da ke sa ido, ta tabbatar da shugabancin ADC tun da farko, amma yanzu tana aiki a wata hanya da ta saɓa wa matsayinta na farko.

Saboda haka, jam’iyyar tana kira ga hukumar zaɓe da ta dakatar da wannan matsayi nan take, ta ci gaba da karɓar duk wata wasiƙa ta doka daga ADC kuma ta kiyaye nauyin da tsarin mulki ya tabbatar mata wajen daidaita dukkan jam’iyyun siyasa.

Haka nan kuma ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su yi hattara su kasance masu sa ido game da waɗannan mummun mataki na karkatar da dimokuraɗiyyar Nijeriya da tilasta yin mulkin kama-karya a ƙasar nan.

ADC ta tsara gudanar da tantance masu neman muƙami a ranar 7 ga Afrilu 2026 da ɗaukaka ƙara kan aikin tantancewa a 8 ga Afrilu 2026 da gudanar da babban taronta na mazaɓu da na ƙananan hukumomi a 9 ga Afrilu 2026 da ɗaukaka ƙara kan babban taron a ranar 10 ga Afrilu 2026 da babban taronta na jihohi a ranar 11 ga Afrilu 2026 da ɗaukaka ƙara kan babban taronta na jihohi a ranar 12 ga Afrilu 2026 da babban taronta na ƙasa a ranar 14 ga Afrilu 2026.

 

INEC
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
Ƙarin Farashin Man Fetur: TUC Ta Shawarci Gwamnati Ta Tallafawa Matatun Mai Na Cikin Gida

Ƙarin Farashin Man Fetur: TUC Ta Shawarci Gwamnati Ta Tallafawa Matatun Mai Na Cikin Gida

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.