ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Ko Arsenal Za Ta Mamaye Duniya?

by Sulaiman and Abba Ibrahim Wada
4 months ago
Arsenal

Abin mamaki ne yadda Arsenal ta fada cikin mawuyacin hali a baya-bayan nan, amma sai ga shi a yanzu ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai ta Champions Leagu.

Matsi ya tattaru a kan Mikel Arteta domin ganin ya kawo karshen shekara 22 da kungiyar ta yi tana kamfar kofi.

Kokarin da suka nuna na kauce wa rashin yin nasara a dukkanin wasan da suka buga na Chamiopns League abu ne da har yanzu bai samu yabon da ya cancanta ba.

ADVERTISEMENT

Kwallon da Bukayo Saka ya jefa a raga kafin zuwa hutun rabin lokaci shi ne ya bai wa Arsenal nasarar da ta samu 1-0 a kan Atletico Madrid a daren ranar Talata, wanda hakan ke nufin an tashi da jimillar kwallaye Arsenal 2-1 Atletico Madrid daga wasa biyu da kungiyoyin suka buga.

A gaskiyar lamari, duk da cewa wasan da suka buga a filin wasa na Emirate bai kayatar sosai ba, Arsenal din ta yi kokari sosai a wasanninta na gasar Turai.

LABARAI MASU NASABA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Arsenal ce kungiyar da har yanzu ba ta yi rashin nasara ba a gasar tun daga farkon wannan kaka, inda ta lallasa kungiyoyi kamar Bayern Munich da Inter Milan da kuma Sporting kafin kawowa wannan matsayi.

Kuma za a iya cewa Arsenal ta nuna rashin tausayi a wasanninta na gasar, kusan za a iya cewa babu wani lokaci da ta shiga wani babban hadarin da za a ce tana fargabar za a fitar da ita.

“Ba na tunanin wani zai raina kokarin da muka yi a wannan gasa har zuwa wannan lokaci,” in ji dan wasan tsakiya na kungiyar Declan Rice lokacin tattaunawarsa da Amazom Prime.

“Muna da hujjar da za mu yi murna a wannan lokaci. Gasa mafi daraja a kwallon kafa.”

“Gabanin fara wasan mun san irin hadarin da muke fuskanta, idan ba mu tunkare shi ba, to ba za ka iya tunkarar kowane wasan kwallon kafa ba.

Lokacin da muka ci kwallo ta farko, na san cewa za mu yi nasara. Na ji a jikina cewa wani muhimmin abu ya tunkaro mu.”

Magoya bayan Arsenal sun tarbi motar bas din da ta dauko ‘yan wasan da wasan tartsatsin wuta da sowa, wani abu da ba a saba gani ba – wani abu da mai horarwa Mikel Arteta ya bayyana a matsayin dare na musamman.

“Mun kafa tarihi gaba dayanmu,” in ji Arteta. “Na yi matukar farin ciki kuma ina alfahari da duk wanda ya taimaka wa wannan kungiya. Yadda aka tarbe mu a lokacin da muka iso abu ne na mausamman.

“Goyon bayan da aka nuna mana ya kara mana kuzari, ban taba ganin irin wannan lamari ba.”

“Mun san yadda kowa ke ji game da haka, ‘yan wasan sun yi duk abin da ya dace, kuma ga shi bayan shekara 20 a karo na biyu mun je wasan karashe na gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Kokarin Arsenal a faifai

A ‘yan makonnin nan, Arsenal na ta kokarin samun nasarori a karshen kakar wasanni ta bana.

Bayan nasarar doke Fulham da ci uku da nema a karshen makon jiya, Arsenal ta da magoya bayanta sun bayyana farin ciki.

Wannan nasarar ta zo a daidai lokacin da ake nemanta, wato kafin wasan kungiyar na kusa da karshe. Sai kuma nasarar da ta samu ta zuwa wasan karshe na gasar Zakarun Turai. Wani karin arashin shi ne kwallo shida kawai aka zura a ragar kungiyar.

Da aka tambaye shi ko yana alfahari da nasarar da kungiyar ke samu, Arteta ya ce, “kwarai da gaske domin mun san karfin kungiyoyin da muka fafata da su a kowane mataki.”

“Atletico babbar kungiya ce kuma tana da karfi sosai. Mun san irin kokarin da take yi da irin rawar ganin da take nuna.”

 Ga yadda Arsenal ta kai wasan karshe:

Wasa 14 ta buga kuma ba a doke ta a ko daya ba a Zakarun na Turai. Wannan lokaci mafi tsawo da kungiyar ta yi ba tare da rashin nasara ba bayan wasa 13 da ta yi ba tare da rashin nasara ba a tsakanin watan Maris na 2005 zuwa Afrilun 2006.

Arsenal ta kai wasan karshe na Zakarun Turai a karon farko tun shekarar 2006. Wannan lokaci mafi tsawo da kungiya za ta kai wasan karshe a gasannin Turai manya biyu – Europa da Zakarun Turai – bayan Atletico da ta kai shekara 40 kafin ta kai wasan karshe a 2014.

A wasa 14 da Arsenal ta buga, ba a zura mata kwallo ba a guda tara.

Yiwuwar lashe kofuna biyu

Canjaras da Man City ta yi da Eberton ya kara ba Arsenal damar sa rai wajen lashe kofin Premier din ta bana.

City ta barar da babbar damar ce mako biyu bayan Arsenal ta yi rashin nasara a gasar, inda aka fara tunanin tamkar ta watsar da damar lashe gasar premier ta bana bayan dogon dako da ta yi.

Amma bayan doke Atlatico da kuma zama derere a saman teburin premier din da maki biyar, yanzu kusan za a iya cewa ta fi kusa da nasara.

“Irin kokarin da kungiyar nan take ta yi a cikin shekarun nan abin lura ne,” in ji Rice a lokacin da yake bayyana irin rawar da kungiyar ta taka a kaka uku da suka gaba da take karewa a ta biyu.

“Muna ta hakuri, muna ta aiki tukuru tare da goyon bayan kocinmu.”

Arteta ya ba mutane mamaki ganin yadda ya fara wasan da Myles Lewis-Skelly mai shekara 19 a tsakiya.

Haka kuma dan wasan gaba Biktor Gyokeres, wanda ya zura kwallo biyu a karshen makon jiya, ya nuna bajinta matuka, domin wasan na cikin wasannin da ya fi kwazo.

Rice na cikin ‘yanwasan da suka taimakon Arsenal a kakar bana, inda ko a wasan Atletico shi ne ya zama gwarzon danwasa.

Yanzu kallo ya fara komawa filin wasa na Emirate, inda ake sa ran watakila Arteta ya samu nasarar share wa magoya bayan Arsenal hawaye na samun kofi babba a kakar bana.

Arsenal
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
Arsenal
Abba Ibrahim Wada
Website |  + posts Bio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai
Wasanni

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Next Post
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada

2027: Bukatar Zaben Shugabanni Na Gari

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.