ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Alƙawarin Wa’adi Ɗaya Na Peter Obi Ya Raba Kawunan Ƴan Arewa

by Yusuf Shuaibu
3 months ago

An samu rarrabuwar kawuna a cikin harkokin siyasa a arewacin Nijeriya game da alƙawarin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar NDC, Mista Peter Obi, ya yi na yi wa’adin ɗaya idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Wasu masu ruwa da tsaki da dama sun bayyana wannan tayin a matsayin dabarar siyasa, amma za iyi wuya a aiwatar da alƙawarin, yayin da wasu kuma suke ganin cewa zai iya cikawa ba dabarar siyasa ba ce.

Obi kwanan nan ya sake bayyana cewa zai yi wa’adin shekara huɗu kawai idan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, ya gabatar da wannan alƙawarin da nufin kwantar da hankalin masu siyasar a arewa da kuma daidaita yanayin mulki a ƙasar nan.

ADVERTISEMENT

Ya yi wannan alƙawarin ne bayan da jam’iyyar NDC ta ware wa yankin kudu manyan ofisoshi, yayin da ta ware wa arewa mataimakin shugaban ƙasa bayan ya bar jam’iyyar ADC.

Ya dai nuna sha’awar yin takara da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yake shi ɗan asalin Jihar Kano ne a arewacin Nijeriya, wanda ake sa ran zai tafi tare da shi a matsayin mataimakin shugaba.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Sakamakon hakan, tattaunawa a tsakanin ƴan siyasar arewa ya nuna cewa mafi yawan martini da ke fitowa shi ne, a yi taka-tsannan maimakon amincewa kai tsaye.

Yawancin ƴan siyasan arewa da masu sharhi kan harkokin siyasa suna fassara wannan alƙawarin a matsayin dabarar siyasa wadda take nufin inganta karɓuwar Obi a yankin a lokacin da ake sake tsara haɗin kan ƴan adawa kafin shekarar 2027.

Suna ganin wannan alƙawari a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin samun goyon bayan ƴan arewa a zaɓen 2027 da zai haɗa manyan ƴan siyasar arewa masu tasiri.

Babban abin damuwa da masu ruwa da tsaki na arewa suke ciki dai shi ne, batun riƙe amana. Wasu ƴan siyasa da aka yi hira da su sun ambaci abubuwan da suka biyo baya bayan mutuwar tsohon Shugaba Umaru Musa Yar’Adua a shekarar 2010 da kuma matakin da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya yanke na tsayawa takara don wani wa’adi a shekarar 2011.

Mafi yawancin ƴan siyasa da dama na arewa, wannan lamari har yanzu yana nan a ranasu, shi ya sa suke shakku kan wannan alƙawari na Obi sakamakon cewa ba a yi shi a rubuce ba.

Yawancin fitattun mutane daga arewacin cikin jam’iyyar APC mai mulki suna ganin cewa alƙawarin Obi ba zai iya wuce tanade-tanaden kunɗin tsarin mulki ba.

A cewarsu, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shugaban ƙasa damar neman sake zaɓe wa’adi na biyu bayan kammala wa’adin farko, ba tare da la’akari da cika alƙawari lokacin yaƙin neman zaɓe ba. Suna jaddada cewa da zarar an kama mulki, lissafin siyasa yakan canza.

Masanin siyasa kuma jagoran matasa, Murtala Abubakar, ya bayyana alƙawarin Obi na wa’adin ɗaya a matsayin wata dabara ta siyasa da aka tsara don samun nasarar zaɓe. A cewarsa, wannan alƙawari ba shi da tushe a tsarin doka, saboda babu kundin tsarin mulki ba tilasta haka ba.

Ya yi iƙirarin cewa yankin arewacin Nijeriya ya ɗauki darasi sosai bayan abin da ya gani a mulkin Jonathan.

A cewar Abubakar, masu kaɗa ƙuri’a na arewa yanzu sun fi sha’awar tabbataccen tsarin mulki fiye da alƙawari ta fatar baki.

“Abin da muke nema ba yarjejeniya ta wucin gadi ba ce, amma shugabanci wanda ke mutunta adalci kuma ƙoƙarin ganin an bi tsarin karɓa-karɓa,” in ji shi.

Haka shi ma shugaban ƙungiyar ci gaban matasan arewacin Nijeriya, Isah Abubakar, ya ce arewacin Nijeriya a yanzu yana kallon irin waɗannan alƙawaruka da idon basira.

Ya yi muhawara cewa tunanin sauyin siyasa na 2011 har yanzu yana tasiri a tsakanin ƴan arewawa waɗanda ke ganin cewa yankin ya kasance cikin rashin samun ribar siyasa bayan mutuwar Yar’Adua.

A cewarsa, babban raunin alƙawarin Obi shi ne, a ko da yaushe yana yin alƙawarin da ya ci karo da tsarin mulki, wannan alƙawarin siyasa ne na fatar baki.

Ya ce da zarar an rantsar da shi a ofis, shugaban ƙasa na da haƙƙin neman wani wa’adin kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yayin da manyan  siyasa da ke kewaye da shugaban ƙasa za su iya matsa lamba ga wanda ke riƙe da muƙamin don ya ci gaba da zama a ofis bayan alƙawarin farko.

A ganinsa, amincewa da shugabancin wa’adi guda na shekaru huɗu ba tare da kariyar tsarin mulki ba na iya jefa yankin arewa cikin rashin tabbas idan alƙawarin ya zama an yi watsi da shi bayan an hau mulki.

A yankin arewa maso yamma, musamman a tsakanin magoya bayan Kwankwaso, ra’ayoyi sun rabu.

Wasu mabiya Kwankwasiyya sun ce suna ganin wannan shirin a matsayin wata hanya don mayar da ikon shugabancin ƙasa a yankin arewa a 2031 ta hanyar tsarin haɗin gwiwa da aka gudanar.

Shugaban ƙungiyar samar wa matasa aiki yi ta arewa kuma shugaban ƙungiyar ‘yaƴan jam’iyyar APC na jihohin arewa 19, Dakta Maina Gimba, ya faɗi matsayarsu.

Yayin da yake amincewa da alƙawarin Obi, ya yi iƙirarin cewa nasara ko gazawar irin wannan tsarin zai dogara ne kan tattaunawar siyasa, ciki har da sanin wanda zai kasance mataimakin Obi da takamaiman sharuɗɗan da masu ruwa da tsaki na arewa za su iya buƙata a matsayin wani ɓangare na kowace haɗin gwiwa.

Gimba ya kuma ba da shawarar cewa yawancin ƴan siyasar arewa suna nan cikin taka tsantsan game da niyyar siyasar Obi na dogon lokaci.

A cewarsa, ƴan siyasar arewa suna nazarin kan manufofin Obi sosai kafin su ɗauki kowace irin mataki gaban zaɓen 2027.

Daga cikin APC, Bala Ibrahim ya ƙi amincewa da wannan alƙawari gaba ɗaya, yana jaddada cewa ƴan Nijeriya su kasance cikin shakku game da wannan alƙawari saboda tsarin mulki ya fi kowanne alƙawari muhimmanci.

Ya iƙirarin cewa masu ba da shawara na siyasa da magoya baya za su iya tantance alƙawarin Obi don ya yi amfani da haƙƙanin abin da tsarin mulki ya zo da shi na neman sake zaɓe idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Jigon jam’iyyar ADC, Faisal Kabir, ya kuma bayyana shakku game da amincin alƙawarin wa’adi guda, yana mai jayayya cewa ƴan Nijeriya har yanzu suna shakkar alƙawuran ƴan siyasa.

Shi kuwa mai goyon bayan Obi, Ibrahim Hussaini Abdulkarin, ya musanta cewa duk da cewa ana zargin ƴan siyasa da rashin cika alƙawari, ya kamata a ba Obi dama. Ya jaddada cewa Obi ya nuna daidaito wajen cika alƙawuran siyasa a baya kuma zai girmama alƙawarin yin wa’adi guda idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban Nijeriya.

Haka kuma shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya da ke ƙasashen ƙetare na Jihar Kano, Dakta Muhammad Hamisu, ya bayyana amincewarsa da alƙawarin Obi. A cewarsa, mutane da dama daga arewa suna ganin Obi ɗan siyasa ne wanda zai cika alƙawarinsa na yin wa’adi ɗaya idan aka zaɓe shi.

Ko yake, masana suna cewa nasarar wannan alƙawari na iya dogara kan manyan ƴan siyasa masu tasiri daga arewa idan har suka amince kuma suka ba da halalcin tsarin kafin zaɓen shugaban ƙasa na shekara mai zuwa.

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Sin Da EU Na Tattaunawa Dangane Da Kafa Tsarin Tuntuba Game Da Batutuwan Cinikayya Da Zuba Jari

Sin Da EU Na Tattaunawa Dangane Da Kafa Tsarin Tuntuba Game Da Batutuwan Cinikayya Da Zuba Jari

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.