ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Amurka

Marco Rubio, a ranar Talata ya ce Amurka tana kokarin ganin an samu mafitar adala mai dorewa wajen kawo karshen yakin da Rasha ta shafe kimanin shekaru uku ta na yi a Yukiren, sai dai dole ne Rashar da Yukiren, kowaccen su, ta hakura da wani abu, kafin a iya cimma zaman lafiya.

Manyan jami’an Amurka da Rasha sun kamala tattauwar sulhun da suka yi a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a ranar Talata, inda suka tattauna akan samo mafita ga yakin Yukiren, kwanaki gabanin sarki mai jiran gado, Yarima Muhammad ibn Salman ya kira wani taro da shugabannin Misra, Jordan,katar da Hadaddiyar Daular Larabawa su tattauna akan martanin kasashen Larabawa ga alkawrin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa zai karbe ikon Gaza.

  • Kalaman Trump Marasa Kan-gado Game Da Gaza Za Su Kara Tsananta Halin Da Ake Ciki A Gabas Ta tsakiya
  • Trump Na Son Karbe Ikon Gaza Domin Sauya Wa Falasdinawa Matsuguni

Tattaunawar 2 da basu da alaka, ya nuna irin rawar da yariman take takawa a yunkurin ganin Trump ya cika alkawarin da ya yi wa magoya bayansa a lokacin gangamin yakin neman zabe na kawo karshen yakin Yukiren da na Gaza.

ADVERTISEMENT

Shugaba Trump ya sake bayyana cewa zai gaggauta kawo karshen yakin.

Rubio ya yi wannan bayanin ne, bayan da shi da sauran manyan jami’an Amurka su ka gana ta tsawon sama da sa’o’i hudu a kasar Saudiyya da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergy Labrob da hadimansa, a wani yunkurin farko na kawo karshen yakin, da kuma inganta dangantakar Amurka da Rasha da ta yi tsami.

LABARAI MASU NASABA

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar.

A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba.

Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni.

Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da zai samar da zaman lafiya.

A ci gaba da rangadin da Marco Rubio yake a Gabas ta Tsakiya tuni ya je Isra’ila da Sudiyya.

Amurka
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

MASU ALAKA

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya
Kasashen Ketare

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

June 23, 2026
Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya
Kasashen Ketare

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

June 22, 2026
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran
Kasashen Ketare

Iran Ta Ce Shirinta Na Makamai Masu Linzami Ba Ya Cikin Tattaunawa Da Amurka

June 18, 2026
Next Post
Abubuwan Sha Domin Ƙarin Ni’ima Ga Mata

Abubuwan Sha Domin Ƙarin Ni’ima Ga Mata

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Mataimakin Babban Sakataren MDD Ya Yaba Wa Dabarun Sin Kan Mulkin Kasa

Tsohon Mataimakin Babban Sakataren MDD Ya Yaba Wa Dabarun Sin Kan Mulkin Kasa

June 26, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Sabbin Matakan Dakile Haɗura A  Titin Bypass

Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Sabbin Matakan Dakile Haɗura A Titin Bypass

June 26, 2026
Disu

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Sin Ta Habaka Karfin Soja Ne Don Kare Ikon Mallakar Kasa Da Muradun Ci Gaba

Sin Ta Habaka Karfin Soja Ne Don Kare Ikon Mallakar Kasa Da Muradun Ci Gaba

June 26, 2026
Amurka

Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Fara Aikin Gina Mayankar Zamani A Garin Jos

June 26, 2026
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Amfani Da Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Ta Fakewa Da Zargin “Kwadagon Tilas”

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Amfani Da Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Ta Fakewa Da Zargin “Kwadagon Tilas”

June 26, 2026
NDC Ta Ce Za Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Rajistarta

NDC Ta Ce Za Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Rajistarta

June 26, 2026
An Fitar da Jadawalin Wasannin Zagayen Farko Na Gasar Carabao Cup ta 2026/2027

An Fitar da Jadawalin Wasannin Zagayen Farko Na Gasar Carabao Cup ta 2026/2027

June 26, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ba Ta Da Hujjar Umartar INEC Ta Soke Rajistar Jam’iyyu —Uban Doman Lafiya

June 26, 2026
Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

Xi Ya Mika Jaje Kan Mummunar Girgizar Kasar Venezuela

June 26, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.