ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Bukaci Manoman Nijeriya Da Kar Su Yi Watsi  Da Fanni Saboda Tsadar Kayan Aiki

by Abubakar Abba
4 months ago
IFAD

Biyo bayan asarar da wasu manoma a fadin kasar nan suka tabka a kakar noman bara, da fuskantar tsadar kayan noma da kuma kalubalen rashin tsaro, wani kwararre a fannin tattalin arziki da ke Jihar Kaduna, Alhaji Sabi’u Sani Sama’ila, ya shawarci manoman da suka fuskanci wadannan matsaloli, musamman kananan manoma, da kada su yi watsi da fannin na noma.

Sama’ila, ya bayar da wannan shawara ce, a hirarsa da manema labarai a Kaduna, inda ya shawarci manoman, maimakon su yi watsi da fannin, su zuba kudaden da suka tsara za su yi amfani da su wajen noman bana, a fannin kamar kiwon kifi, kajin gidan gona, kiwon zuma da kuma sauran fannonin na kiwo.

A cewarsa, bai kamata su yi watsi da fannin ba, musamman duba da cewa; su ma wadannan fannonin na kiwo, za su iya samar masu da kudaden shiga kamar yadda ya bayar da shawarar a hirarsa da manema labarai a Kaduna.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, ya yi nuni da cewa; a duk wata sana’a a fadin duniya, ba wai aikin noma kadai ba, dole ne mutum ya kwana da sanin cewa, yau kana iya samun riba ko kuma mai sana’ar ya yi asara. Sai dai, Sama’ila ya kuma yi kira ga gwamnati, da ta samarwa da manoma kayan aikin noma a cikin rahusa tare da kuma samar da cikakken tsaro domin manoman kasar, musamman wadanda ke  Arewacin kasar, su koma gonakinsu, su ci gaba da yin noma.

Sama’ila, wanda kuma manomi ne, ya bukaci gwamnatin tarayyaidan, idan za ta raba wa manoman kayan aikin noma, ta rika raba musu a kan lokaci, musamman ma takin zamani.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Ya kuma yi kira ga daukacin matasan da ke fadin kasar nan, da su rungumi aikin noma, mai makon jiran samun aikin yi daga wurin gwamnati.

Ya kara da cewa, ta hanyar rungumar aikin noma ko kiwo, hakan zai ba su damar inganta rayuwarsu da kuma zamowa masu dogaro tare da tsayawa da kafafunsu.

Manoma
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Manoma

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.