ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Daure Mutum Biyu Shekara 24 Saboda Kashe Wani Dan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Nijeriya

An yanke wa wasu maza biyu hukuncin daurin shekaru 24 da watanni biyar gaba daya saboda rawar da suka taka a wani mummunan hadarin mota da ya yi sanadin mutuwar wani dan Nijeriya mazaunin Birtaniya, Sylbester Abayomi, a birnin Manchester.

Wadanda aka samu da laifin, Uways Hussain mai shekaru 20 da Usmon Mahmood mai shekaru 23, an yanke musu hukunci bayan an same su da laifi kan hadarin da ya faru a watan Maris na shekarar 2026 a titin Kingsway da ke Manchester, wanda ya yi sanadin mutuwar Abayomi.

Rahotanni sun nuna cewa Hussain ya samu hukuncin daurin shekaru 11 da watanni takwas, yayin da Mahmood ya samu shekaru 12 da watanni tara a gidan yari.

ADVERTISEMENT

Sanarwar da ‘yansandan Greater Manchester suka fitar ta bayyana cewa hukuncin Mahmood na daga cikin na farko a Birtaniya inda aka samu wani fasinja da laifin taimakawa da karfafa aikata laifin haddasa mutuwa ta hanyar tuki cikin hadari.

Binciken ‘yansanda ya nuna cewa mutanen biyu sun kwashe daren kafin hadarin suna yawo a Kudancin Manchester cikin ganganci da gudun wuce kima, tare da daukar bidiyon kansu yayin da suke tuki.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

‘Yansandan sun ce motar da aka yi hadarin da ita mallakin Mahmood ce, wanda ya ba Hussain damar tuka ta tsawon daren.

An kuma gano daga bidiyon wayoyin hannu da aka kwato cewa su biyun suna tuki da gudun da ya haura mil 100 a awa (100mph) a hanyoyin da iyakar gudu ta kasance mil 30 a awa (30mph).

Bidiyon ya kuma nuna suna karya jan fitilar hanya tare da kutsa kai tsakanin motocin da ke tafiya ba tare da la’akari da lafiyar sauran masu amfani da hanya ba.

Sanarwar ta ce: “Mutanen biyu sun kasance suna tafiya da gudun da ya wuce mil 100 a awa a hanyoyin da aka kayyade mil 30 a awa. A wasu lokuta sun kai gudun sama da mil 130 a awa, kuma dakiku kadan kafin hadarin an rubuta gudunsu ya kai mil 139 a awa.

“A wani lokaci cikin daren, sun tsaya a gidan mai inda bidiyo ya nuna Mahmood yana shakar wani iska daga cikin balan-balan yayin da yake zaune a kujerar fasinja.

“Sauran bidiyon da aka samu sun nuna Mahmood yana shakar iskar daga balan-balan yayin da Hussain ke tuki da gudun sama da mil 100 a awa, inda shi ma Hussain ya bayyana yana yin hakan.”

‘Yansandan sun ce hadarin ya faru da misalin karfe 4:36 na asubahin watan Maris 2026 a mahadar titunan Green End Road da Kingsway.

Marigayin Abayomi na kan hanyarsa ta zuwa aiki ne, kuma ya shiga mahadar ne bayan ya samu koren hasken hanya, yana tunanin yana da lafiya ya wuce. Sai dai wata mota kirar Bolkswagen Golf da Hussain ke tuka wa, wadda ta karya jan fitila cikin matsanancin gudu, ta bugi motarsa.

“Sylbester yana kan hanyarsa ta zuwa aiki kuma ya shiga mahadar ne da koren haske, yana ganin hanya lafiya ce. Daga nan ne motar Bolkswagen Golf da Hussain ke tuka wa ta buge shi bayan ta karya jar fitila cikin tsananin gudu,” in ji ‘yansandan.

Jami’an agajin gaggawa sun garzaya wurin hadarin, amma Abayomi ya rasu sakamakon munanan raunukan da ya samu.

Sanarwar ta kara da cewa bayan hadarin, mutanen biyun sun fara tattauna yadda za su tsere da kuma yadda za su boye wasu hujjoji.

Wani sakon gaggawa da agogon Apple Watch na Hussain ya aika kai tsaye bayan hadarin ya dauki hirarsu, inda aka ji suna tattauna yadda za su gudu daga wurin da kuma irin hujjojin da ya kamata su cire daga motar.

An kuma ji suna tattauna yiwuwar kai rahoton cewa an sace motar. Daga bisani, sun yi odar motar Uber domin tserewa daga wurin.

‘Yansandan Greater Manchester sun ce sun samu rahoton farko da karfe 4:37 na asubahin, kuma cikin mintuna 12 kacal jami’ansu sun gano inda mutanen biyu suke tare da kama su.

Bayanan da aka ciro daga motar Bolkswagen Golf sun tabbatar da cewa motar ta kai gudun mil 139 a awa a dakikun da suka gabaci mummunan hadarin da ya yi sanadin mutuwar Abayomi.

Nijeriya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Nijeriya Da Turkiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Haɗin Gwuiwa Don Bunƙasa Harkar Ma’adinai

Nijeriya Da Turkiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Haɗin Gwuiwa Don Bunƙasa Harkar Ma’adinai

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.