ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Suka Kan Mayar Da Nijeriya Jujin Jibge Kwantaina Da Ake Shigowa Da Su

by Abubakar Abba
1 month ago
Jujin

Ana ci gaba yin suka, kan yadda wasu kamfanonin ketare da ke shigo da Kwantaina da babu wasu kaya a cikinsu zuwa cikin kasar, wadanda  kuma ake jibgesu, a duk inda suka ka dama.

Wannan batun wanda a yanzu,  wasu kwararru a fannin sun fara  kira ga mahukunta a kasar, da sanya a fara gudanar da binciken kan jibge Kwantainar, ba bisa bin ka’ida da kamfanobin suka shafr shekaru suna yi, hakan ya sanya hukumar Kustam rasa samun kudaden shiga da suka kai yawan dala miliyan 600.

Wasu daga cikin kwararru a fannin hahada-hadar sufurin Jiragen Ruwa a kasar nan ne, suka bayyana hakan.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikinsu, Mista Okey Ibeke,  ya yi kira ga hukumar Kwastam ta kasa  da ta binciki yadda ake shigowa da Kwantainar daga waje tare da kuma sayar da su a cikin kasar nan.

Ibeke wanda ya bayyana haka a taron manema labarai a jihar Legas, ya yi gargadi da cewa, lamarin na janyowa hukumar rashin samun kudaden shiga.

LABARAI MASU NASABA

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

Ya buga misali da wasu rahotannin da ke nuna cewa, daya daga cikin irin wadannan kamfanonin da ke aikinsu a cikin kasar, na shirin fara saayar da wasu Kwantaina guda  2,500 da babu wasu kaya a cikinsu a kasar nan.

A cewarsa, an ruwaito cewa, kamfanin, zai sayar da kowacde daya, kan farashi daga dala 1,600 zuwa dala 2,000 ,inda masu sayen za su tura kudaden zuwa cikin wani Asusun kamfanin da ke a kasar Amurka.

Ya kara da cewa, wannan harkallar, na ci gaba da diga alamar tambaya, ta rashin bin ka’idojin hukumar Kwastam, kan shigo da irin wadannan Kwantaina da kamfanoni na kasar waje ke yi, zuwa cikin kasar nan.

” A bisa tsarin yarjejeniyar wucin gadi ta shigo da Kwantaina cikin kasar nan tare cire masu shinge, za a iya kara shigo da su ne kawai idan an yi amfani da su, gabanin a hukumance a fara sayar da su a cikin kasar, wanda kuma hakan, zai iya kasancewa, bayan hukumar Kwastam, ta tantance su da tsarin biyan kudade fito da kuma na biyan haraji, kan kayan, “A cewarsa.

” Duk wata hada-hadar da aka yi, ba tare da bin wadannan ka’idojin ba, tamkar take hukumarKwastam ta shekarar 2023 ne, musamman duba da cewa, shigo da su ba bisa ka’ida ba, na janyo zurarewa samar da kudaden shiga, da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta samu,’ Inji shi.

Ya ci gaba da cewa, hakan janyowa Gwamnatin Tarayya, asarar samun kudaden shiga na fito da suka kai daga dala 350 zuwa dala 400  da kuma kudaden haraji a duk Kwantaina daya.

Ya yi nuni da cewa, bisa rashin samar da kwakyawan tsari a kasar nan a hada-hadar kasuwanci, hakan na kara mayar da kasar, jujin jibge irin wadannan Kwantaina.

Kazalika, ya yi nuni da cewa, hakan zai kuma haifar da cikas, ga kokarin da Babban Bankin Nijeriya ke ci gaba da yi na kara karfafa darajar Naira a kasar nan musamman domin a rage dogaro kan kudaden musaya na kasar waje.

Ya bayyana cewa, ya kamata shugaban hukumar Kwastam na kasar, ya gaggauta dakatar da ci gaba da sayar da Kwantaina na wucin gadi tare da gudanar da cikakken bincike.

Ya bayyana cewa daukar matakai sune kawai mafita kan wannan matsalar, musamman domin a dakile yadda kudaden shiga na Gwamnatin Tarayya ke zurarewa zuwa wata hanya.

Jujin
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    “Mutunta Ƴancin Addinai Ita Ce Hanyar Wanzar Da Zaman Lafiya A Kaduna”

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tattalin Arziki

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN
Tattalin Arziki

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

June 27, 2026
Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani
Tattalin Arziki

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

June 26, 2026
Next Post
Kotu Ta Yi Gwanjon Kaddarorin Sani Sha’aban Bisa Taurin Bashi

Kotu Ta Yi Gwanjon Kaddarorin Sani Sha'aban Bisa Taurin Bashi

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.