ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Yekuwar Daukar Matakin Gaggawa Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida

by Yusuf Shuaibu, Sulaiman and Adamu Yusuf Indabo
4 months ago
Jarida

Gidauniyar ci gaban kafofin yada labarai ta Afirka (AMDF) ta yi yekuwar daukar matakin gaggawa kan take ‘yancin jarida, domin ta ce ‘yancin ‘yan jaeida na fuskantar babban barazana a yankin Afirka. 

Gidauniyar ta bayyana hakan ne a yayin bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta 2026, gidauniyar AMDF ta nuna damuwarta kan ci gaba da tabarbarewar ‘yancin ‘yan jarida a fadin Nahiyar Afirka.

Daga nazarin gidauniyar kan ‘yancin ‘yan jarida, ta bayyana cewa yanayin ‘yancin ‘yan jarida a Afirka na raguwa, inda ‘yan jarida ke fuskantar tashin hankali da danniya da hana gudanar da aiki kan tsari.

ADVERTISEMENT

Kiddigar ‘yancin ‘yan na gidauniyar AMDF a tsakanin 2025 zuwa 2026, sun nuna wasu daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali. A cewarta, a kasar Sudan ba kawai ta zama mafi yawan kisan ‘yan jarida a Nahiyar ba a 2025 ba, har ma tana da tarihin mafi yawan ‘yan jarida da suka bace. Ta ce wannan abin damuwar na nuna hadarin da masu aikin jarida ke fuskanta, musamman a wuraren da ake rikici da kuma wadanda ke cikin rashin kwanciyar hankali.

Binciken ya gano cewa, kasar Eritrea na ci gaba da zama kasar Afirka da ke tsare ‘yan jarida mafi yawa, inda ta kama ‘yan jarida ba bisa ka’ida ba tare da musguna musu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Kazalika, kiddigar a fadin yankin Sahel, musamman a Nijar da Mali da Burkina Faso da gwamnatocin sojoji ke jagoranta sun kara tsananta matakan kan ‘yan jarida masu zaman kansu, suna adawa yaduwar bayanai. A yankin manyan tafkuna, ciki har da Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo da Rwanda da Burundi, aikin jarida na kara zama laifi, inda ake tauye ‘yan jarida da cin zarafi da gurfanarwa a kotu da tsoratarwa.

Haka kuma a Yammacin Afirka, Nijeriya ta bambanta a matsayin daya daga cikin mafi hadari ga ‘yan jarida, tare da farmaki akai-akai daga gwamnatoci da masu zaman kansu. Wadannan al’amuran suna nuna wani babban yanayi da ‘yancin aikin jarida ke fuskantar matsin lamba.

Binciken AMDF ya gano kasashe biyar da ake tauye ‘yancin ‘yan jarida sosai, kasashen sun hada da Eritrea, Djibouti, Sudan, Habasha, da Rwanda. A cikin wadannan kasashen, aikin jarida na cikin kuntatawa sosai, kuma ‘yan jarida suna fuskantar hadarin kama su ba bisa ka’ida ba, ana azabtar da su wani lokaci ma har a kashe su.

“Shaidu daga nau’o’i daban-daban na bin diddigi, ciki har da namu, suna nuni da sakamakon guda daya, ‘yancin ‘yan jarida a Afirka yana karkashin barazana mai tsanani,” in ji AMDF.

AMDF ta kira ga gwamnatocin Afirka su kiyaye alkawuran kundin tsarin mulki da ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin ‘yan jarida.

Jarida
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
Jarida
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Jarida
Adamu Yusuf Indabo
+ posts Bio
  • Adamu Yusuf Indabo
    https://hausa.leadership.ng/author/adamu-yusuf-indabo/
    Marubutan Batsa Ku Ji Tsoron Allah -Emili
  • Adamu Yusuf Indabo
    https://hausa.leadership.ng/author/adamu-yusuf-indabo/
    Marubutan Da Akwai Hikima, Na Yanzu Sai Karyar Zuwa Waje – Amina
  • Adamu Yusuf Indabo
    https://hausa.leadership.ng/author/adamu-yusuf-indabo/
    Ba Nanaye Ko Rashin Da’a Nake Rubutawa Ba – A.S Aikawa
  • Adamu Yusuf Indabo
    https://hausa.leadership.ng/author/adamu-yusuf-indabo/
    Marubuta Tamkar Madubi Suke Ga Al’ummah – Zainab Salihu Yarima

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da ‘Ya’yansu Alkur’ani (2)

Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da 'Ya'yansu Alkur'ani (2)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.