ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yansanda Da ‘Yan Sa-kai Sun Ceto Shanu 245 Da Aka Sace A Kaduna

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Kaduna

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na sa-kai sun dakile yunkurin satar shanu da garkuwa da mutane guda biyu a kananan hukumomin Igabi da Kudan na jihar, inda suka ceto jimillar shanu 245 da aka sace.

Rundunar ta bayyana cewa an gudanar da wadannan ayyuka ne a ranar 31 ga Mayu bayan hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda, masu tsaron sa-kai da kuma al’umma.

A wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar ranar Litinin, ya ce da sanyin safiyar Lahadi wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani matsugunin Fulani da ke wajen kauyen Rubu a Karamar Hukumar Igabi, inda suka daure makiyaya uku da wasu masu gadi kafin su tafi da shanu masu yawa.

ADVERTISEMENT

Hassan ya ce shugaban kungiyar Miyetti Allah a Karamar Hukumar Igabi ne ya kai rahoton lamarin, wanda hakan ya sa jami’in ‘yansanda na Rigachikun Dibision ya tattara jami’ansa tare da masu tsaron sa-kai na Miyetti Allah da kuma mambobin Cibilian Joint Task Force domin gudanar da aikin ceto.

“Kungiyar hadin gwiwar ta bi sawun wadanda ake zargi tare da sanar da al’ummomin da ke makwabtaka da wurin da kuma matsa musu lamba sosai.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

“Saboda tsananin matsin lambar da aka musu, ‘yan bindigar sun yi watsi da shanun da suka sace da kuma mutanen da suka kama, sannan suka tsere zuwa cikin daji. An ceto fiye da shanu 200 cikin koshin lafiya, yayin da ake ci gaba da kokarin cafke wadanda suka tsere,” in ji sanarwar.

A wani lamari makamancin haka, rundunar ta ce an sake ceto wasu shanu 45 a wani samame da aka kai a Hunkuyi.

Rundunar ta bayyana cewa bayan samun rahoton satar shanu, jami’in ‘yansanda na Hunkuyi Dibision ya kaddamar da bincike da sintiri, wanda ya haifar da samun sahihan bayanan sirri cewa an boye shanun da aka sace a cikin wani daji da ke Hawan Mai Mashi a kan hanyar Zariya zuwa Kano.

Sanarwar ta ce an tura hadaddiyar tawaga ta jami’an ‘yansanda da ma’aikatan Jihar Kaduna Bigilance Serbice zuwa yankin.

“Da ganin jami’an tsaron, ‘yan bindigar masu dauke da makamai sun bude musu wuta. Jami’an tsaron sun mayar da martani da karfin wuta mafi karfi, lamarin da ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa da raunukan harbin bindiga, tare da barin dukkan shanun 45,” in ji Hassan.

Kakakin rundunar ya kara da cewa ana ci gaba da bincike domin cafke wadanda suka tsere da kuma rusa kungiyar masu aikata wadannan laifuka.

Ya kuma bayyana cewa Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya yaba da hadin gwiwar da ke tsakanin ‘yansanda, masu tsaron sa-kai na Miyetti Allah, Cibilian Joint Task Force, Kaduna State Bigilance Serbice da kuma al’umma, yana mai cewa nasarar ayyukan ta nuna tasirin amfani da bayanan sirri da kuma tsarin tsaro na hadin gwiwa da al’umma.

Muhammad ya bukaci mazauna jihar su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa yaki da ayyukan ta’addanci da sauran laifuka a fadin jihar.

Ya kuma jaddada aniyar rundunar na kare rayuka, dukiyoyi da dabbobi a dukkan sassan Jihar Kaduna.

Kaduna
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Hadimin El-Rufai Ya Zargi ICPC Da Hana Shi Samun Kulawar Likita

Hadimin El-Rufai Ya Zargi ICPC Da Hana Shi Samun Kulawar Likita

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.