ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabannin Ƙungiyoyin Mata 30 A Kaduna Sun Yi Alƙawarin Yaƙi Da Fyaɗe

by Abubakar Abba
1 month ago
kaduna

Shugabannin gungiyoyi mabiya addinin Kirista da ƴan’uwansu Musulmai a Jihar Kaduna, sun rattaba hannun yarjejeniyar yaƙi da yi wa ƴaƴa mata fyaɗe da kuma take ƴancin Ɗan’adam.

Sun rabbata hannun ne a taron kwana biyu da cibiyar sasanci tsakanin addinai (IMC) ta shirya tare da tallafin ofishin jakadanci na ƙasar Jamus da ke Abuja.

Matan an zaɓo su ne daga shiyya ta biyu da ke a Kaduna, wanda idan matan sun koma cikin al’umominsu za su zama jakadu na tabbatar da wannann manufar da taron ya cimma.

ADVERTISEMENT

A jawabinsa a wajen taron a madadin cibiyar, Mista Samson Auta ya ce manufar aikin shi ne, domin a daƙile yawan fyaɗen da ake yi wa ƴaƴa mata a jihar.

Ya ce ƙarin manufar rabbata hannun yarjejeniyar shi ne, domin matan su ƙara wa waɗanda aka yi wa fyaɗen ƙwarin giwa, su rinƙa fitowa fili suna faɗa wa hukumomin da suka dace, maimakon yin shiru, domin a ɗaukar matakin shari’a.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya ƙara da cewa ƙarin manufar shi ne, domin a daƙile nuna ƙyama da tsangwama da kuma kyara ga wanɗanda aka yi wa fyaɗen a cikin al’umomin da suka fito.

A nata jawabin, shugabar ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (FIDA) reshen Kaduna, Barrista Olufunke Bamikole ta ce, fahimtar muhimmancin ƴancin Ɗan’dam a tsakanin mahalarta taron, zai ƙara ba su damar sanin yadda za su kare ƴancin waɗanda aka ci zarafinsu ta hanyar fyaɗen.

Ta koka da cewa, rashin gazawar ɗaukar matakin gaggawa na wasu hukumomin a yankin Arewacin ƙasar, musamman a yankunan da ke karkara na hukunta waɗanda ake zargi, sun ci mutuncin ƴaƴa mata da yara ta hanyar fyaɗe.

Olufunke ta buƙaci gwamnatocin ƙasar, musamman na yankin Arewa da su ƙara ƙarfafa dokokin kare cin zarafin ƴaƴa mata da yaran da aka yi wa fyaɗe, musamman domin hukunta duk wanda aka kama, saboda ya zama darasi ga sauran masu aikata hakan.

Ita kuwa manajar Cibiyar Salama da ke duba lafiyar ƴaƴa mata da yaran da aka yi wa fyaɗe kyauta da ke asibitin ƙwararru na Yusuf Ɗanstoho da ke a Tudun Wada Kaduna, Barista Sidikat Bello Adegboye, ta yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma kan yadda za a daƙile aikata ta’asar.

Ita kuwa ɗaya daga cikin jami’an Cibiyar Salama da ke duba lafiyar ƴaƴa mata da yaran da aka yiwa fyaɗe kyauta da ke asibitin ƙwararru na Gwamna Awon a Kakuri, Nanak Ndam, ta yi nuni da cewa waɗanda aka yi wa fyaɗe na shafar rayuwarsu ta yau da kullum, inda ta ce akwai matuƙar buƙatar a ba su kulawar da dace.

Shi kuwa jami’in da ke lura da sashen bai wa yara kariya a hukumar Sibil Difence reshen jihar, Suleiman Maiyaki, ya nuna ɓacin ransa kan yadda wasu iyayen ke lalata shaidar da za a iya amfani da ita na waɗanda aka yi wa fyaɗen, wanda hakan ke zama ƙalubale na bi masu haƙƙinsu a shari’ance.

kaduna
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
kaduna

Ƙungiyar Ƙwadago A Kebbi Ta Nemi Mafi Ƙarancin Albashin Na ₦500,000

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.