Ministan Wajen Sin Ya Gana Da Mataimakin Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Iran
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, a yau Litinin ya gana da mataimakin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, Qadir Nizamipour, a birnin New Delhi. A yayin ganawar, Wang ya ce Sin tana maraba da kaddamar da fara tuntubar bayan taro tsakanin Iran da Amurka game da yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kasashen biyu suka sanya hannu a kai. Wang ya bayyana cewa Sin, a matsayinta na cikakkiyar abokiyar huldar Iran bisa manyan tsare-tsare, ta kasance ko da yaushe a turbar tabbatar da adalci kuma tana goyon bayan dukkan kokarin da ke taimakawa wajen samun zaman lafiya, tare da tallafa wa Iran wajen kare ‘yancinta, da tsaro da kuma martabar kasarta. A nasa bangare kuwa, Nizamipour ya ce Iran tana ba da fifiko sosai ga dangantakarta da kasar Sin kuma tana yaba wa muhimmiyar rawar da Sin ta taka a harkokin kasa da kasa da na yanki. Duka dai Wang da Nizamipour sun hallara a birnin New Delhi ne domin halartar taro na 16 na masu ba da shawara kan tsaron kasa da manyan wakilai kan tsaron kasa na kungiyar kawancen kasashen BRICS. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)



















