ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta yi tir da kakkausan harshe tare da bayyana damuwarta kan kisan gilla da ƙona wata mata ƙurmus da wasu fusatattun matasa suka yi a yankin Marabar Jos, sakamakon zargin satar yara da ba a tabbatar ba.

Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, da rashin tausayi, da kuma karan tsaye ga tsarin doka.

Bayanai sun nuna cewa, da misalin ƙarfe 10:00 na safe ne jami’an tsaro ƙarƙashin babban jami’in ƴansanda na yankin (DPO) suka ceci matar daga hannun dandazon jama’ar da suka far mata, inda aka kai ta ofishin ‘yansanda domin bata kariya da fara gudanar da bincike kan zargin da ake mata. Sai dai, daga baya ɗaruruwan mazauna yankin sun dira ofishin ‘yansandan.

ADVERTISEMENT

Fusatattun mutanen sun yi amfani da yawansu wajen fito da matar ta karfin tsiya daga hannun jami’an tsaro, inda suka yi mata dukan kawo wuƙa har ta ce ga garinku nan, sannan suka banka wa gawar tata wuta ta ƙone ƙurmus. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama, ciki har da Amnesty International, sun bayyana matar a matsayin Malama Ummulkhairi, mahaifiyar yara biyar, sannan sun yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.

Daga karshe, rundunar ‘yansandan ta tabbatar da cewa an riga an kama wasu daga cikin matasan da ake zargi da hannu a wannan ɗanyen aiki, kuma ana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka gudu. Kwamishinan ‘yansandan jihar ya gargaɗi jama’a cewa babu wani mutum ko ƙungiyar da ke da ikon ɗaukar doka a hannunsa, kuma za a gurfanar da dukkan waɗanda aka kama gaban kotu domin fuskantar hukunci mai tsanani.

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula

Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    NAF Ta Kai Hare-Haren Sama Kan Maboyar Ƴan Ta’adda A Borno
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar Jamus
  • Abubakar Sulaiman
    Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta
  • Abubakar Sulaiman
    Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

MASU ALAKA

Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula
Labarai

Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula

July 12, 2026
‘Lokaci Ya Yi Na Ɗaukar Mataki Kan Masu Yanke Hukunci Da Kansu’
Labarai

Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna

July 12, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Labarai

Ƴan Ƙwadago Sun Buƙaci Naira 300,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

July 12, 2026
Next Post
Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace, Sun Daƙile Hari A Kaduna Da Zamfara

An Kashe Fitaccen Kwamandan ’Yan Bindiga, Kachalla Sani Yellow A Zamfara

An Kashe Fitaccen Kwamandan ’Yan Bindiga, Kachalla Sani Yellow A Zamfara

July 12, 2026
NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli

NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli

July 12, 2026
2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Amince Da Jamilu Gwamna A Matsayin Gwamnan Gombe

2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Amince Da Jamilu Gwamna A Matsayin Gwamnan Gombe

July 12, 2026
NDLEA Ta Gargaɗi Masu Sana’ar Keke NAPEP Kan Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

NDLEA Ta Gargaɗi Masu Sana’ar Keke NAPEP Kan Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

July 12, 2026
inec

2027: INEC Ta Tsawaita Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara

July 12, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina

July 12, 2026
Annalena Baerbock: Kasar Sin Babbar Mai Goyon Bayan Tsarin Mabambantan Bangarori Ce

Annalena Baerbock: Kasar Sin Babbar Mai Goyon Bayan Tsarin Mabambantan Bangarori Ce

July 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.