ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Masu Ɓoye Gas Ɗin Girki

by Abubakar Sulaiman
3 months ago

Gwamnatin tarayya ta yi kashedi mai ƙarfi ga masu harkar iskar gas na girki (LPG) da su gaggauta daina ɓoye gas ɗin ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani. Ƙaramin ministan albarkatun man Fetur (Gas), Ekperikpe Ekpo, ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki na harkar, inda ya ce gwamnati tana da ƙwararan hujjoji na nuna cewa ana boye gas ɗin domin janyo ƙarancinsa da kuma haifar da tsadar farashi.

Ministan ya bayyana cewa, koda yake akwai matsaloli na raguwar shigo da gas ɗin daga ƙasashen waje, da tashin dalar amurka, da tsadar sufuri, amma babban abin da ke ƙara ta’azzara lamarin shi ne yadda wasu ‘yan kasuwa ke son janyo ƙaranci min kayan da gangan. Ya jaddada cewa babban burin ma’aikatarsa shi ne tabbatar da cewa gas ɗin da ake samarwa a cikin gida ya wadata amfanin mazauna ƙasar gabanin fitar da shi waje, sannan ya ba da umarnin cewa bayanan da yake samu sun nuna gas ɗin watan Yuni zai wadaci kowa idan har aka rarraba shi cikin adalci.

A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar NMDPRA, Rabiu Umar, ya bayyana cewa hukumar ba za ta lamunci ganin ana fitar da gas ɗin zuwa waje ba ana barin ‘yan kasa cikin wahala ba alhalin kasar tana da dumbin arzikin gas. Ya ƙara da cewa hukumar ta riga ta fara sanya idanu kan farashin kuma za ta hukunta duk wani dillali ko mai jigilar kaya da aka kama yana ƙara farashi ba tare da ƙa’ida ba, tare da bayyana cewa sabbin matatun gas da ke tafe, kamar ta Seplat, za su kawo sauƙin farashi gabanin ƙarshen watan Yuli.

ADVERTISEMENT

Daga ƙarshe, Babbar Sakatariya, Patience Oyekunle, ta buƙaci ɗaukacin masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen inganta harkar rarraba iskar gas ɗin tare da nuna gaskiya a farashi domin kare haƙƙin masu amfani da shi ba tare da gurgunta gwuiwar masu zuba jari ba.

Jami’an gwamnati sun tabbatar wa mahalarta taron cewa za su ci gaba da wallafa sunayen duk wani kamfani ko mutumin da aka kama da laifin ɓoye gas ɗin, kuma za a miƙa su ga hukumomin tsaro domin fuskantar hukunci.

LABARAI MASU NASABA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai
  • Abubakar Sulaiman
    Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku
  • Abubakar Sulaiman
    An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro
  • Abubakar Sulaiman
    Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

MASU ALAKA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai
Labarai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku
Labarai

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro
Labarai

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Next Post
Jam’iyyar APC Ta Tafka Asarar Mabiya A Gombe, Sun Bi Pantami PDP

Jam'iyyar APC Ta Tafka Asarar Mabiya A Gombe, Sun Bi Pantami PDP

LABARAI MASU NASABA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.