Sakon Kasar Sin Game Da Ingiza Tsarin Jagorancin Kare Hakkin Bil’adama
A kwanan nan an gudanar da dandalin kasa da kasa dangane da jagorancin kare hakkin bil’adama na shekarar 2026 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Dandalin da ya gudana bisa taken "Ci gaban bai daya, kare hakkin bil’adama na bai daya: Bikin cika shekaru 40 da amincewa da yarjejeniya mai nasaba da ikon samar da ci gaba da sabuwar mahangar jagorancin kare hakkin bil’adama na duniya". To ko me wannan dandali ya mayar da hankali a kai? Amsa ita ce samar da muhimmiyar kafa ga kasashen duniya, ta zakulo sabbin dabarun kare hakkokin bil’adama. Kazalika, dandalin ya aike da muhimmin sako ga sassan kasa da kasa, cewa Sin na goyon baya, kuma za ta ci gaba da hadin gwiwa, da aiki tare da dukkanin sassa wajen kara kyautata tsarin jagorancin kare hakkin bil’adama. Idan mun waiwayi baya ma, a shekarar 2023 mun ga yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga dandalin jagorancin kare hakkin bil’adama na duniya. Wadda a cikinta, ya jaddada matsayin kasarsa na aiwatar da kudurorin kare hikkin bil’adama ta fannin tsaro, da samar da ci gaba, da hadin gwiwar dukkanin sassa, bisa ruhin martaba juna da daidaito tsakanin kasashe daban daban. Ko shakka babu, idan mun kalli wadannan matakai na Sin za ku kara fahimtar sakon kasar, na amincewa da karfafa tsarin jagorancin kare hakkin bil’adama na duniya, da ingiza cimma nasarar kudurorin al’ummun duniya na kare hakkokin bil’adama. To amma yayin da kasar Sin ke daukar wadannan jerin matakai, da gabatarwa duniya matsaya, da mahangarta game da kare hakkin bil’adama, kamata ya yi al’ummun kasa da kasa su ma su tashi tsayi wajen kaucewar aiwatar da matakai na danniya, da amfani da batun kare hakkin bil’adama a matsayin makamin cimma burikan siyasa, ko yin fuska biyu a fannin. Ya zama wajibi a yi watsi da yada farfagandar kare hakkin dan’adam, da tsoma hannu irin na siyasa cikin harkokin jagorancin tsarin kare hakkin bil’adama, muddin dai ana son kare odar duniya, da cimma muradun kasa da kasa a wannan fanni na kare hakkokin bil’adama. (Saminu Alhassan)



















