Sin Ta Kaddamar Da Shirin Shekaru Biyar Na Bunkasa Makamashi Da Ake Iya Sabuntawa
Hukumar makamashi ta kasar Sin ko NEA a takaice, ta kaddamar da shirin bunkasa amfani da makamashi da ake iya sabuntawa, karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, wanda kasar ke aiwatarwa tun daga shekarar nan ta 2026 zuwa 2030. Kundin da hukumar ta NEA ta fitar da hadin gwiwar hukumar raya kasa da aiwatar da sauye-sauye a yau Alhamis a hukumance, ya nuna cewa ya zuwa shekarar 2030, jimillar karfin samar da makamashin da cibiyoyin da aka kafa na iya kaiwa kusan kilowat biliyan 3.5, inda a duk shekara ake hasashen samar da jimillar lantarkin da ta kai kusan kilowat-awa tiriliyan 6. Kazalika, adadin karfin samar da makamashi ta iska da hasken rana na iya haura kilowat biliyan 2.8, yayin da jimillar lantarkin da za a samar duk shekara za ta haura kusan kilowat-awa tiriliyan 4. Makamashi da ake iya sabunta amfani da shi na nufin wanda ake iya ci gaba da maimaita amfani da shi, da sake sarrafawa ta hanyoyin dabi’a cikin kankanen lokaci. Wadanda suka hada da wanda ake samu daga karfin ruwa, da iska, da hasken rana, da tururin halittu, da dumin karkashin kasa, da wanda ake samarwa daga teku. A daya bangaren kuma, sabbin makamashi na nufin wadanda ake iya samarwa daga sauran fannoni ban da ta karfin ruwa, kamar dai yadda kundin bayanin shirin ya fayyace. (Saminu Alhassan)



















