Kasar Sin Na Maraba Da Karin Kasashe Su Shiga Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya
A yau Litinin, 26 ga watan nan na Oktoba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, fasahar kirkirarriyar basira ta AI wani sabon fanni ne mai kunno kai a cikin harkokin jagorancin duniya, kuma gwaji ne na tantance inganci ga tsarin jagorancin duniya. Tsarin jagorancin duniya yana bukatar kokari na gaske don karfafa wakilci da fada-a-jin kasashe masu tasowa. Guo ya bayyana cewa, kwanan nan a yayin taron dandalin inganta jagorancin duniya na shekarar 2026 (wanda aka gudanar a Xiongan), kasar Sin ta fitar da rahoton ci gaban da aka samu game da "Tsarin gina karfin fasahar AI don amfani da ita ta hanyar da ta dace kuma ga kowa da kowa." Abu na gaba kuma, kasar Sin na maraba da karin kasashe su shiga cikin Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI ta Duniya domin binciko karin hanyoyin hadin gwiwar kasa da kasa wajen gina karfin fasahar AI, tare da karfafa ci gaban fasahar AI a duniya domin amfani da ita ta hanyar da ta dace kuma ga kowa da kowa bisa daukar kwararan matakai. Dangane da takardar da kasar Sin ta fitar kwanan nan game da matsayin kasar kan inganta jagorancin harkokin sararin samaniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan babban mataki ne da kasar Sin ta dauka domin aiwatar da abubuwan da ke kunshe a cikin manyan shawarwari na duniya guda hudu da ta gabatar, tare da zurfafa kokarin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga dan Adam a bangaren sararin samaniya. Kazalika, kasar Sin za ta ci gaba da aiki tare da dukkan bangarori bisa ruhin bude kofa da gina abubuwa masu ma’ana, domin tabbatar da cewa sakamakon ci gaban da aka samu a bangaren sararin samaniya ya zama mai amfanarwa ga daukacin bil’Adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















