Kasar Sin Ta Kafa Tarihi A Gasar Wasannin Asia Da Aka Yi A Ketare Da Lambobin Zinare 169
Tawagar kasar Sin ta kammala gasar wasanni ta nahiyar Asiya da jimilar lambobin yabo 341 da suka hada da zinare...
Tawagar kasar Sin ta kammala gasar wasanni ta nahiyar Asiya da jimilar lambobin yabo 341 da suka hada da zinare...
An kira taron ministocin kasuwanci na kungiyar G20 a birnin Milwaukee na kasar Amurka, daga ranar 30 ga watan Satumba zuwa ranar 1 ga watan Oktoba, inda ministocin kasuwanci ko wakilansu na kasashe membobin kungiyar gami da kasar Poland suka halarci taron. Wakilin kasar Sin a bangaren shawarwarin kasuwanci da kasashen duniya, wanda har ila yau shi ne mataimakin ministan kasuwanci na kasar, Li Chenggang ya halarci taron, tare kuma da gabatar da jawabi. Li ya bayyana cewa, sakamakon kalubalen ra’ayin nuna bangaranci, kasar Sin tana kira ga kasashe membobin G20 da su aiwatar da ra’ayin kara mu’amalar mabambantan sassa, da goyon-bayan tsarin kasuwanci mai kunshe da bangarori daban-daban karkashin jigon kungiyar WTO, da kiyayewa, gami da inganta ka’idar bai wa kasashe fifiko a matsayin tushe, da tabbatar da zaman karko da kyakkyawan fata ga kasuwancin duniya. Har wa yau, Li ya ce, samar da isasshen abinci na da alaka sosai da rayuwar dan Adam da zaman lafiya a kowace kasa, kuma kasar Sin ta bayar da gudummawa ga kokarin samar da wadataccen abinci ga duk duniya. Ya kara da cewa, ya dace kasashe membobin G20 su yi kokarin rage shingen cinikayya, da ba da tabbacin samar da isasshen abinci ba tare da wata matsala ba. Game da batun da ya shafi karfin samar da kayayyaki, ya ce ya kamata a yi nazari daga dukkan fannoni na duniya, da inganta shawarwari da hadin gwiwa maimakon yin fito-na-fito. Bugu da kari, ya ce kasar Sin tana adawa da daukar matakai na kashin kai da bin ra’ayin ba da kariya ga kasuwanci, bisa hujjojin da suka shafi tinkarar batun samar da kayayyaki fiye da kima, ko kawar da batun yin aiki ala-tilas. (Murtala Zhang)
Kwanan nan ne wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya zanta da Konstantin Novoselov, mai lambar karramawa ta Nobel a fannin ilimin fiziks. Novoselov wanda ya samu lambar karramawar lokacin da yake da shekaru 36 a duniya, ya ce, kaifin basirar dan Adam a ko yaushe, shi ne tushen gano kimiyya da tunanin kirkire-kirkire. Da yake bayyana yadda idanuwansa suka shaida ci gaban kimiyya da fasaha da kasar Sin ta samu karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, Konstantin Novoselov ya bayyana farin-cikin ganin an samu nasarorin fasaha na zahiri, sakamakon aiwatar da manufofin shirin. Yayin da hadin gwiwar nazarin kimiyya tsakanin kasa da kasa ke fuskantar kalubale daga siyasar duniya a halin yanzu, Konstantin Novoselov, ya ce ba za a iya raba mu’amala da hadin gwiwar kasa da kasa da ci gaban kimiyya ba, inda ya yi fatan ganin ci gaba da karfafar irin wannan hadin gwiwa a nan gaba. (Murtala Zhang)
Kafofin yada labarai na kasar Rasha sun ruwaito shugaban kasar Vladimir Putin na cewa, ganawar da zai yi da shugaban...
Kasar Sin ta hada cibiyar adana makamashin carbon dioxide da aka matse, mai karfin megawatt 100 irinsa na farko da...
Yayin da aka fara hutun bikin ranar kafuwar kasa gadan-gadan, kana matafiya ke zirga-zirga a fadin kasar Sin a rana...
Bukukuwan baje koli da dama da aka yi a watan Satumba, ciki har da na cinikayya da zuba jari na...
Yayin da ake hutun ranar kafuwar kasa, shigowa kasar Sin domin bude ido na kara samun tagomashi, inda karin masu ziyara daga kasashen waje ke zuwa domin gane wa idanunsu abubuwa masu ban sha’awa na al’adu da bude ido da yadda kasar Sin ke bude kofarta da sauye-sauyen da take samu. A cikin rabin farko na bana, adadin baki daga kasashen waje da suka shigo kasar Sin ya kai miliyan 22.914, karuwar sama da kaso 20 kan mizanin shekara-shekara. Daga cikinsu, adadin wadanda suka shigo ba tare da visa ba, ya karu zuwa kaso 30.6 a mizanin shekara-shekara. Cikin wani nazari da kafar CGTN ta gudanar, kaso 92.8 na masu bayar da amsa sun ce labaran da ake watsawa a kafofin sada zumunta game da tafiye-tafiye a kasar Sin sun kara masu sha’awar neman kara sanin kasar da son ziyartarta, yayin da kaso 87 suka ce ziyartar kasar Sin da kan su zai taimaka musu wajen samun cikakkiya da ingantacciyar fahimta game da al’adu da ci gaba da ma yanayin al’ummar kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)
Jiya ranar 1 ga watan Oktoba, an kunna fitilu masu kyan-gani a husumiyar Burj Khalifa, gini mafi tsawo a duniya,...
A ranar 17 ga watan Satumba ne, aka jefa kuri’a a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, dangane da kudurin tsawaita wa’adin rukunin kwararru mai kula da takunkuman da aka kakaba wa Iran da Amurka ta gabatar, inda Rasha da Sin suka jefa kuri’ar ‘na ki’, al’amarin da ya sa ba a amince da daftarin kudurin ba. A ranar 1 ga watan Oktoba kuma, babban taron MDD karo na 81 ya kira wani cikakken zama dangane da yadda kasashe masu kujerun dindindin suka yi amfani da hakkinsu na jefa kuri’ar na ki, inda zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD, Sun Lei ya bayyana cewa, ya zama dole a ki yarda da duk wani yunkuri na tsananta rikici da kawo illa ga shawarwari. Sai dai kuma, dole ne a mayar da hankali kan duk wata damar da ka iya sassauta halin da ake ciki gami da taimaka wa kokarin diflomasiyya. Sun Lei, ya kara da cewa, mawuyacin halin da batun nukiliyar Iran ya shiga, ya samo asali ne daga janyewar Amurka daga yarjejeniya ta dukkanin fannoni, gami da yadda ta yi bakin kokarin matsa wa Iran lamba, tare kuma da daukar matakan soja har sau biyu yayin da ake tsaka da shawarwari tsakaninta da Iran. A ganin kasar Sin, jirkita gaskiyar tarihin batun nukiliyar Iran, gami da kara kokarin farfado da sanya wa Iran takunkumi da kuma gabatar da daftarin kuduri da ka iya haifar da rikici, tabbas zai lahanta hadin gwiwa da kwarjinin kwamitin sulhu na MDD, da kuma taka birki ga kokarin diflomasiyya. (Murtala Zhang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.