Ofishin Jakadancin Sin Ya Yi Allah Wadai Da Matakin Jagororin Japan Na Ziyartar Haikalin Yasukuni
Wani mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar Sin dake Japan, ya yi matukar Allah wadai da matakan baya bayan...
Wani mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar Sin dake Japan, ya yi matukar Allah wadai da matakan baya bayan...
A yau Lahadi ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin Dushanbe domin fara ziyarar aiki a kasar Tajikistan, tare da halartar taro karo na 25 na majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice. Li Qiang, ya isa birnin Dushanbe ne bayan kammala ziyarar aiki a kasar Uzbekistan, inda ya zanta da firaministan kasar Abdulla Aripov a jiya Asabar. Yayin zantawar tasu, Li Qiang ya ce Sin a shirye take ta karfafa tsare-tsaren aiwatar da dabarun neman ci gaba tare da Uzbekistan, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin makamashi, da albarkatu, da fasahar AI, da noman zamani da sauran sassa. (Saminu Alhassan)
A yau Lahadi ne aka bude dandalin Liangzhu a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Dandalin karo na hudu, zai mayar da hankali ne ga tattauna batun tarin kalubale, dake tattare da kare gado da hanyoyin zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa. A shekarar nan ta 2026 ne ake bikin cika shekaru 90 da gano baraguzan Liangzhu. Kuma dandalin na bana na da take "Hade zamanin baya da mai zuwa: Kare gado domin zamaninmu". Kazalika, dandalin ya hallara jamiai, da masu aikin hako ababen tarihi da malamai daga sassa daban daban na duniya. Yayin wata ganawa da manema labarai, Zhang Ling, jamia a hukumar lura da gadon aladu ta kasar Sin, ta ce ana sa ran kwararru, da masana za su tattauna game da batutuwa da dama, tun daga wadanda suka jibanci wayewar kai ta zamanin dauri, zuwa bincike game da aikin hako kayan tarihi a tsaffin biranen da suka gushe. A daya hannun kuma, za a baje kolin sabbin sakamakon bincike da ci gaba da aka samu a wannan fage. A nata tsokacin kuwa, cikin jawabin bude dandalin da ta gabatar, ministar raya aladu ta kasar Girka Lina Mendoni, cewa ta yi ya zama wajibi jamaa su matsa gaba daga dabarun gargajiya, su rungumi masu wanzuwa, kana su rike tsarin gudanarwa mai samar da kariyam game da dukkanin bangarori da nufin kare aladu na gado yadda ya kamata. A bangarensa kuwa, cikin wani sako ta kafar bidiyo da ya gabatar, mataimakin babban daraktan hukumar UNESCO ta MDD Nayef Al-Fayez, cewa ya yi tsarin gudanar da yawon bude ido mai dorewa, zai taimaka wajen kare aladu na gado ta hanyar kara wayar da kayan jamaa game da muhimmancin gado domin zuriuin masu zuwa, da kyautata fahimtar aladu, da karfafa yanayin rayuwar alummu masu nasaba da hakan". (Saminu Alhassan)
Da yammacin yau Lahadi ne aka bude gasar wasannin Asiya ajin masu bukata ta musamman karo na biyar a birnin Nagoya na kasar Japan. Kasar Sin ta aike da tawagar yan wasan motsa jiki 312, wadanda za su fafata a rukunonin wasanni 335 a sassan gasar 17. (Saminu Alhassan)
Kwanan nan, Firaministar kasar Japan Sanae Takaichi, ta aike da hadaya zuwa haikalin Yasukuni, sannan ministan manufofin tattalin arziki da...
Jakadan kasar Sin kan harkokin kwance damarar makamai Li Chijiang, ya yi kira ga kasashen duniya su hada hannu wajen...
Da safiyar yau Asabar, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarta tare da gabatar da jawabi a bikin bude taron kasa da kasa na 2026 kan likitancin gargajiya a birnin Beijing. Li Qiang ya ce likitancin gargajiya na zaman wani karfi na musammam da ke kare lafiyar dan adam da bunkasa nasarar wayewar kai. Ya ce la’akari da shafe lokaci mai tsawo ana amfani da shi, likitancin gargajiya na Sin ya samar da wata hanya ta musammam ta samun ci gaba. Ya ce ya kamata kasashen duniya su karfafa hadin gwiwa da kuma amfani da albarkatun likatancin gargajiya na duniya da hada shi cikin tsarin kiwon lafiya, da aiki tare domin shawo kan kalubalen lafiya da dan adam ke fuskanta. A cewar firaministan, kasar Sin za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta iya karfinta da bayar da gudunmuwa wajen cike gibin kiwon lafiya da ake da shi a duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Fu Cong, zaunannen wakilin Sin da ke MDD, ya jaddada bukatar bin tsarin da kasashen Afirka ke jagoranta domin cimma mafita ta siyasa ga rikicin kasar Sudan. Fu Cong ya bayyana hakan ne jiya Jumma’a, yayin wani taron Kwamitin Sulhu na MDD kan nazarin halin da Sudan ke ciki. Fu ya ce, kasar Sin ta dade da rike matsayi mai adalci game da batun Sudan, kuma ta yi kira da a kawo karshen rikicin da wuri. Ya ce tun bayan barkewar rikicin, kasar Sin ta samar da tallafin kayayyaki iri-iri ga Sudan, wadanda suka hada da abinci, kayayayyakin likitanci, da kayayyakin ceton jama’a da sauransu. Kuma za ta ci gaba da bayar da taimako gwargwadon karfinta, tare da taka rawar gani wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan. A wannan rana kuma, a gun wani taro mai taken “Duniya a nan gaba: Sake gina aminci ta hanyar daukar matakai kan sauyin yanayi”, wanda shugaban babban taron MDD ya shirya, Fu Cong ya yi kira da a karfafa tsarin shugabancin yanayin duniya, tare da hanzarta aiwatar da sauyi zuwa tsarin muhalli mai tsafta. Ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka rawar gani wajen ingantawa da bayar da gudummawa ga ayyukan kula da yanayin duniya, inda ta shiga hadin gwiwa kan ayyukan kiyaye muhalli tare da kasashe da yankuna sama da 100, wanda hakan ya ba da muhimmiyar gudummawa wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayi. (Safiyah Ma)
Wata takardar bayani da kasar Sin ta fitar yau Asabar, ta ce a shekarun baya-bayan nan, tsarin ilimin sana’o’i na...
Shugaban kasar Botswana Duma Gideon Boko, ya ce akwai dimbin fasahohi masu kyau a fannin raya kasa da kasar Sin ta samu, wadanda suka cancanci kasar Botswana ta koya. Shugaba Boko ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi hira da wakilin kafar CGTN ta kasar Sin, yayin ziyarar da ya yi a kasar a baya-bayan nan. Ya kara da cewa, daga cikin fasahohin akwai kokarin raya bangaren masana'antu, don ganin kasa ta samu cikakkiyar kwarewar kirkira da samar da kayayyaki, ta yadda al'umma za su samu kwarin gwiwa kan makomar kasarsu. Ban da haka, a cewar shugaba Boko, asalin imanin Sinawa kan kasarsu shi ne dogon tarihi da dimbin al'adu masu ma'ana na kasar. Kuma sakamakon wadannan abubuwa masu daraja, kasar Sin ta fi dogaro da karfinta da hadin kan al'ummarta wajen daidaita matsalolin da take fuskanta, maimakon neman taimako daga sauran kasashe. Ya ce kasar Botswana ta yarda da ruhin Sinawa na hadin kai da jajircewa, kuma tana son koyon dabarar kasar Sin ta raya kasa. Sa'an nan, Duma Gideon Boko, ya tabo maganar huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, inda ya ce, kasar Sin ta kan nuna cikakken sahihanci, da kokarin tabbatar da girmama juna, yayin da take hulda da sauran kasashe. Kuma ba ta taba neman samun moriya ta wata hanya maras dacewa ba. A sabili da nagartacciyar halayyar da kasar Sin take da ita ne, ta gabatar da manufar yafe wa kasashen Afirka da suke da huldar diflomasiyya da ita harajin fito, wadda ta zama dama mai kyau ga kasashen Afirka, don su habaka bangaren ciniki, da kokarin magance radadin tasirin da yanayin rashin tabbas na kasuwannin duniya ke haifar musu, da karfafa imani a tsakanin bangarorin Afirka da Sin, da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa. (Bello Wang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.