Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Kafa Cibiyar Horar Da Ma’aikatan Jinya A Saliyo
An kaddamar da cibiyar horar da ma’aikatan jinya ta kasashen Sin da Saliyo, a asibitin sada zumunta na Saliyo da...
An kaddamar da cibiyar horar da ma’aikatan jinya ta kasashen Sin da Saliyo, a asibitin sada zumunta na Saliyo da...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Sin ta sha alwashin karfafa musaya da kasar Sweden a dukkanin fannoni, da amfani da fifikonsu, da ingiza hadin gwiwar cimma moriyar juna, da bunkasa dangantakarsu bisa turba mai nagarta, daidaito da dorewa. Wang Yi, ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin da yake zantawa da firaministan Sweden Ulf Kristersson a birnin Stockholm. Wang, ya kuma ce alakar Sin da Sweden ta gamu da wasu wahalhalu a shekarun baya-bayan nan, kuma wani abu mai matukar muhimmaci ga sassan biyu shi ne karfafa shawarwari, da bunkasa fahimtar juna, da gina aminci, tare da kara fahimtar juna yadda ya kamata. Kazalika, karuwar ci gaban kasar Sin zai amfani duniya baki daya, tare da samar da sabbin damammaki ga dukkanin kasashen duniya, ciki har da Sweden. Wang ya kuma yi fatan Sweden za ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata alakar Sin da Turai. A nasa bangare kuwa, mista Kristersson ya ce gwamnatin Sweden na nacewa manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma a shirye take ta karfafa tattaunawa, da fadada amincewa juna, da ingiza hadin gwiwar cimma moriya mai kyakkyawar makoma a dukkanin fannoni tare da Sin. Ya ce Sweden na goyon bayan Turai da Sin a fannin karfafa shawarwari, da inganta shawo kan sabanin dake tsakaninsu. (Saminu Alhassan)
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya miƙa cak na kuɗi da ya kai Naira biliyan 5.81 domin biyan bashin garatutin...
Yayinda kasar Morocco ta zama kasa ta farko a wannan gasar kofin Duniya ta bana da ta kai matakin zagayen...
Rundunar dakarun tsaron teku ta Sin ko CCG, na ci gaba da sintirin wanzar da doka a sassan yankunan ruwa...
Kwanan nan wasu matasa sama da 20 daga jihar Washington ta kasar Amurka, sun ziyarci lardin Sichuan na kasar Sin,...
An yi bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya na Sin karo na 4, wato CISCE a takaice,...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta yaba wa Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Alhaji Isma'il Abba Yusuf, bisa nasarar da aka...
Tawaga ta biyu ta kwararrun jami’an lafiya daga kasar Sin, ta sauka a birnin Kinshasa na janhuriyar dimokaradiyyar Congo a...
A madadin kasar Sin mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin He Wei, ya ziyarci birnin Tehran na...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.