An Gudanar Da Taron Makokin Wadanda Suka Rasu Sakamakon Zabtarewar Kasa A Gyirong
Da misalin karfe 10 saura mintuna biyar na safiyar yau Talata, daya ga watan Satumba, aka gudanar da taron makokin...
Da misalin karfe 10 saura mintuna biyar na safiyar yau Talata, daya ga watan Satumba, aka gudanar da taron makokin...
Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron koli na 26 na shugabannin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), a Bishkek na kasar Kyrgyzstan, inda ya gabatar da muhimmin jawabi. Xi Jinping ya bayyana cewa, yayin da ake kan wata gaba da ta shafi makomar bil adama, ya kamata kungiyar SCO ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, kuma ta yi yunkurin jagorantar muradunta, ta yadda za su kafa tarihi. Shugaban na Sin ya kuma gabatar da wasu batutuwa 4: na farko bayar da fifiko ga neman ci gaba da kirkiro damarmakin samun wadata ta bai daya. Na biyu, ya zama wajibi mambobin kungiyar su bayar da fifiko ga tsaro da samar da yanayin zaman lafiya na bai daya. Na uku, wajibi ne mambobi su nace wa ka’idar sanya muradun jama’a gaba da komai, tare da raya tubalin abota da za ta dore daga zuri’a zuwa zuri’a. Batu na hudu shi ne, dole ne mambobin kungiyar su rungumi tattaunawa da tuntubar juna, kuma su inganta tsarin shugabanci mai adaici, kuma bisa tsari. Shugabannin kasashe mambobin kungiyar sun rattaba hannu tare da fitar da “Sanarwar Bishkek ta Shugabannin Kasashen Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai,” wadda ta kunshi daftarorin sakamako 28 da suka shafi karfafa hadin gwiwar tsaro da tattalin arziki da al’adu da tsarin tafiyar da kungiyar. Taron ya kuma yanke shawarar Pakistan za ta karbi ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar daga shekarar 2026 zuwa ta 2027. (Fa’iza Mustapha)
A daidai lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai SCO na...
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce alkaluman yawan abubuwa da aka saya da ba na bangaren kere-kere ba, sun...
Tsohon mai neman takarar gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Captain Muhammad Bala Jibrin, fice daga cikin jam'iyyar, yana...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Kyrgyzstan Sadyr Japarov a yau Litinin. Yayin tattaunawar tasu, shugaba...
Sha'anin tafiyar da jagorancin duniya ya sake shiga wani "zamani na kungiyar SCO". A yayin gudanar da taron kolin Kungiyar...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa da jin labarin ceto mambobin NYSC 15 da wasu ’yan Nijeriya...
Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin, Xi Jinping, da Aigul Japarova, uwargidan shugaban kasar Kyrgyzstan, Sadyr Japarov, sun ziyarci gidan...
Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayi daban-daban na tsawon kwanaki uku, ciki har da rana,...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.