An Kai Kayayyakin Agaji Masu Yawa Zuwa Gyirong Na Yankin Xizang
An Kai Kayayyakin Agaji Masu Yawa Zuwa Gyirong Na Yankin Hukumar kai dauki da ba da agajin gaggawa ta yankin Xizang ta bayyana a jiya Alhamis cewa, an kai kayayyakin agaji masu yawa zuwa garin Gyirong na birnin Xigaze, ciki har da shinkafa tan 50 da garin alkama tan 20 da man girki tan 1, da kuma tantuna 1,122, da barguna 8,054, kana da injunan samar da wutar lantarki 14, da fakitin ruwan sha 15,500, da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Bayan haka, an tura kwararru 86 daga fannoni daban-daban kamar albarkatun kasa zuwa yankin da ibtila'in ya shafa, tare da kayan aiki na musamman, don karfafa bincike kan hadurran yanayin kasa a kewayen yankin, da kuma duba manyan wuraren dake da hatsarin abkuwar ibtila'i kamar tsaunuka da hanyoyi da gine-gine da sauransu, don rigakafin sake abkuwar wani ibtila’i ko kuma ibtila’i mai biyo baya. Ya zuwa yanzu, an kammala tsugunar da mutane 499 da ibtila'in zabtarewar kasa da laka ya shafa, kuma an kwashe masu yawon bude ido 555 da suka makale. Kazalika, hukumar ta kara da cewa, wannan ibtila'in zabtarewar kasa da laka a Gyirong na yankin Xizang, lamari ne mai sarkakiya wanda ya samo asali daga zabtarewar kankara mai tsayi a kasar Nepal, inda ya haifar da kwararar tarkacen kankara, sannan ya canja zuwa zabtarewar kasa da laka. (Amina Xu)



















