Majalisar Dinkin Duniya Ta Karbi Samfurin Bincike Da Kasar Sin Ta Gudanar A Duniyar Wata
A ranar Litinin da ya gabata, kasar Sin ta gabatarwa Majalisar Dinkin Duniya da ke da hedkwata a birnin Vienna samfurin kasa da ta debo daga sashe mai nisa na duniyar wata a binciken da kumbon Chang'e-6 ya gudanar. Samfurin kasar kuwa zai ci gaba da zama a MDD har abada domin a dinga nuna shi. An gudanar da bikin mika samfurin bisa taken “daga duniyar wata zuwa doron kasa, makomar cigaba ta bai daya ga kowa”, kuma ya samu halartar jami’an diplomasiyya, da jami’an MDD, da masana kimiyya da wakilai daga kungiyoyin duniya. Wannan samfurin kasa da aka debo daga sashe mai nisa na doron wata mai tazarar kilomita 380, 000 da doron kasa, aka kuma mika shi cibiyar harkokin diplomasiyya na kasa da kasa, ya zarce gutsuren kasa da aka gano kadai, maimakon hakan ya zamo wata alama ta nasarar biciken kimiyya, da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kuma yadda bil Adama ke raya makomar bai daya a sararin samaniya. A shekarar 2024, binciken da kasar Sin ta yi a duniyar wata ya haifar da nasarar samo samfurin kasa mai nauyin giram 1,935.3 daga sashe mai nisa na doron wata, wanda kuma ya zama karon farko da aka dawo da samfurin kasa daga duniyar wata a tarihin dan Adam. (Suleiman Suleiman)



















