Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Djibouti, Abdoulkader Houssein Omar, jiya Laraba a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce Sin na daukar dangantakar abota bisa manyan tsare tsare tsakanin Sin da Djibouti da muhimmanci, kuma a shirye take ta zurfafa wannan dangantaka da Djibouti, yana cewa, ya kamata bangarorin biyu su ba manufar Sin ta soke haraji da fa’idjojin kasa na Djibouti, cikakkiyar damar taka rawar da ta kamata. A nasa bangare, Abdoulkader Omar ya ce tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, Djibouti take ta raya dangantakarta da Sin bisa ka’idojin aminci da girmama muradun juna. Ya ce a shirye kasarsa take ta ci gaba da bunkasa muhimmiyar dangantakar abota bisa manyan tsare tsare tsakanin kasashen biyu. Ministoci biyu sun kuma yi musayar ra’ayi mai zurfi kan yanayin da yankin kahon Afrika ke ciki da tsaron hanyoyin jiragen ruwa a tekun Bahr Maliya tare kuma da fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kahon Afrika da tabbatar da tsaro a hanyoyin sufurin jiragen ruwa a tekun Bahr Maliya da gabar Tekun Aden. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)



















