Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya aika da sakon taya murna ga Jami'ar Jilin wacce take bikin cika shekaru 80...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya aika da sakon taya murna ga Jami'ar Jilin wacce take bikin cika shekaru 80...
A yau Talata ne aka bude taron karawa juna sani na kasa da kasa karo 5, dangane da tsarin cin gajiyar fasahar taurarin dan’adam na BeiDou, a birnin Zhuzhou na lardin Hunan. Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya halarci bikin bude taron ya kuma gabatar da jawabi. A cikin jawabin nasa, Zhang Guoqing ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin sassa, wajen kara inganta kirkire-kirkiren fasaha a tsarin aikin taurarin bayar da jagorancin taswira na BeiDou, da karfafa hade tsarin na BeiDou da fasahohi irinsu AI, da taurarin dan’adam na intanet, da kyautata tsarin jagorancin duniya mai nasaba da zayagen taurarin dan’adam, ta yadda hakan zai baiwa tsarin aikin BeiDou damar inganta hidimomin da yake baiwa duniya, da amfanar da daukacin bil’adama. Gabanin bude taron, Zhang Guoqing ya gana da firaministan kasar Madagascar Mamitiana Rajaonarison, wanda ya halarci taron. Taron na wannan karo na da taken "BeiDou domin duniya-Karfafa ci gaban duniya." Ya kuma hallara baki kimanin 900, ciki har da kwararru da masana, da manyan ‘yan kasuwa, da jami’an gwamnatoci na Sin da na kasashen ketare, da wakilan hukumomin kasa da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Kasar Sin ta yi nasarar harba taurarin dan’adam na ayyukan sadarwar intanet guda 10, ta amfani da rokar Zhuque-2E Y7,...
Tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da tafiya a turba mai kyau a watan Agusta, inda ci gabansa ya...
Gwamnatin Jihar Katsina ta fara rarraba keken adaidait guda 238 zuwa cibiyoyin kula da lafiya matakin farko a faɗin jihar,...
An rufe bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima ta kasa da kasa CIFTIS na shekara ta 2026 a ranar...
Rikicin da ya dabaibaye shugabancin Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF) ya dauki wani sabon salo a ranar Talata yayin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya bayyana cewa kwanan nan Sin ta baiwa MDD samfurin kasa wanda na’urar bincike ta Chang'e...
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta dakatar da mataimakin alkalin wasa Yakubu Aliyu har sai baba-ta-gani, bayan hukuncin da ya...
A jiya Litinin ne aka bude babban taro karo na 70, na hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA a birnin Vienna dake Austria. Da yake jawabi a yayin taron, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Sin Shan Zhongde, ya ce amfani da makamashin nukiliya cikin lumana ya shafi jin dadin dukkan bil’adama, wanda hakan ya sa ya fi muhimmanci ga dukkan bangarorin su tsaya tsayin daka kan goyon bayan ra’ayin cudanyar bangarori daban-daban, da kuma kara zurfafa hadin kai tsakanin su. Shan ya kara da cewa, Sin ta dage wajen bunkasa makamashin nukiliya cikin tsari da tsaro, kuma ta daidaita ci gaban da ke da alaka da kirkire-kirkire da tsaro, da kuma gudanar da hadin gwiwa a bude. A nan gaba, Sin za ta mayar da hankali kan muhimman fannoni guda hudu, na farko shi ne daidaita ci gaba, da tsaro don fadada sabbin fannoni, da nufin yin hadin gwiwar makamashin nukiliya. Na biyu kuma, za ta tabbatar da dorewar ci gaba cikin tsaro, don kiyaye tsaron nukiliya na duniya. Na uku kuma, za a bi tsari mai amfanar da mutane, don inganta kimiyya da fasahar nukiliya, ta yadda za su kawo alherai ga jama’a. Kana na karshe, za a aiwatar da manyan tsare-tsare guda hudu na duniya, don inganta tsarin shugabancin duniya. (Safiyah Ma)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.