ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bam Ya Kashe Matasa 4 A Garin Banki

by Abubakar Sulaiman
9 months ago
Matasa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Wani Bam da ya fashe a garin Banki na ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno, inda wani abin fashewa da aka ƙera a gida (IED) ya tarwatse wanda yayi sanadiyar kashe matasa huɗu. Lamarin ya faru ne a bayan tashar motar Banki a unguwar Wajari, kamar yadda rundunar ƴansanda ta tabbatar. Matasan sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke wasa da kayan da suka tsinta a daji, wanda daga bisani ya fashe.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce sun samu  rahoto daga wani mazaunin yankin da misalin karfe 1 na rana, abin da ya sa DPO da tawagarsa tare da kwararru kan kwance Bam (EOD) suka hanzarta zuwa wurin. Sun keɓe yankin domin bincike, tare da tabbatar da mutuwar matasa hudu, yayin da wani yaro mai shekaru 12, Mustapha Tijja, ya tsira amma ya samu munanan raunuka. An garzaya da shi asibitin FHI 360 dake Banki, inda yake karɓar magani.

  • Borno Ta Kashe Naira Biliyan 100 Kan Samar Da Tsaro A 2025 – Gwamna Zulum
  • Bashin Da Bankin AfDB Ya Bai Wa Nijeriya Ya Kai Dala Biliyan 5.1

Binciken farko ya nuna cewa Mustapha da abokansa huɗu sun shiga wani ɗakin da aka gina na wucin gadi a bayan tashar motar, inda marigayin ke wasa da na’urar fashewar da suka ɗauko daga daji. Sai ta fashe har ta kashe Awana Mustapha mai shekaru 15, da Malum Modu 14, da Lawan Ibrahim 12, da kuma Modu Abacha 12. Hukuma ta tabbatar da kwantar hankula da zaman lafiya a yankin, sannan tana ci gaba da gudanar da cikakken bincike.

ADVERTISEMENT

Kwamishinan ƴansanda, CP Naziru Abdulmajid, ya jajanta wa iyalan da abin ya shafa, tare da gargaɗin jama’a musamman yara da su guji taɓa wa ko wasa da duk wani abu da ba su sani ba, musamman waɗanda ake zargin na’urar fashewa ce. Ya buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoto nan take idan suka ga wani abu da suke shakku a kowane lokaci.

Matasa
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
  • Abubakar Sulaiman
    Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso
  • Abubakar Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

MASU ALAKA

Matasa
Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
Labarai

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Labarai

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Next Post
“Lokaci Ya Yi Da Arewa Za Ta Farka Daga Bacci”

Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Matasa

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.