Ƙaramar Ministar babban birnin tarayya Abuja, Mariya Mahmoud, ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai miƙa mulki ga wani ɗan takarar jam’iyyar APC idan wa’adinsa ya ƙare a shekarar 2031.
Ministar ta ce APC za ta ci gaba da kasancewa a kan karagar mulkin Nijeriya, tana mai bayyana cewa jam’iyyar na da damar lashe zaɓen 2027 da kuma ci gaba da mulki bayan wa’adin Tinubu.
A cewarta, nasarar da APC ke samu wajen samun goyon bayan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar na ƙara mata ƙarfi gabanin zaɓen 2027.
Ta kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu na aiwatar da manufofi da shirye-shirye da nufin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
Maganar ta zo ne yayin da ake ƙara fara tattaunawa da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen 2027, inda batun wanda zai iya maye gurbin Tinubu a 2031 ke fara samun muhimmanci a cikin siyasar APC.














