ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cibiyar IAR Ta Gudanar Da Ayyukan Bincike 140 Kan Sabbin Amfanin Gona 

by Abubakar Abba
4 months ago

Cibiyar binciken harkar noma ta Jami’ar Ahamadu Bello da ke Zariya (IAR), na gudanar da ayyukan bincike sama da 140 kan ayyukan noma.

Kazalika, cibiyar ta kuma gabatar da sabbin ayyuka 19, kan kakar aikin noma ta 2026, inda ayyukan suka kai jimillar 159.

Farfesa Ado Yusuf, Daraktan Cibiyar, ya sanar da haka ne yayin taron bita, wanda ya haɗa da na shiyya, wato REFILS, domin yin nazari kan binciken aikin na 2026 da aka saba gudanarwa a duk shekara.

ADVERTISEMENT

Taron, wanda ya gudana a cibiyar da ke jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru a garin na Zariya, Farfesa Nafi’u Abdu Yusuf, Mataimakin Daraktan Cibiyar ne ya wakilci Farfesa Ado Yusuf.

Ya yi nuni da cewa, a ɗaukacin faɗin duniya, ana ci gaba fuskantar ƙalubalen sauyin yanayi, ƙarancin ruwan sama da kuma saurin ɗaukewar ruwan sama.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Ya ƙara da cewa, saboda waɗannan matsalolin, akwai buƙatar a gudanar da binciken, domin lalubo da mafita a kan ƙalubalen.

Ya ci gaba da cewa, ayyukan binciken da cibiyar ta gudanar a 2026, cibiyar ta mayar da hankali ne a kan nauyin da aka ɗora mata kan yin binciken amfanin gona da nufin gano nau’ikan amfanin na gona da za su iya jurewa kowane irin yanayi.

A cewarsa, aikin zai taimaka wajen ƙara samarwa da manoman ƙasar nan kuɗaɗen shiga da kuma ƙara haɓaka samar da wadatacccen abinci a ƙasar.

Ya ce, cibiyar shekaru sama da goma da suka gabata, na ci gaba da ksancewa ɗaya tilo a ƙasar, wacce ta ci gaba da fitar da nau’ika amfanin gona ga manoman ƙasar.

“A 2026 kacal, cibiyar ta fitar da nau’ikan amfanin gona na farin wake guda huɗu da suka haɗa da SAMPEA 22, SAMPEA 23, SAMPEA 24 da kuma SAMPEA 25,” In ji Daraktan.

Ya ƙara da cewa, cibiyar ta kuma fitar da wasu nau’ikan na masara guda biyu, SAMMAZ 78 da kuma na Gyaɗa, SAMNUT 30, tare da ƙarin wasu nau’ikan na Auduga guda huɗu da na masara guda tara, waɗanda aka fitar ta hanyar haɗaka tsakanin ƙungiyar aikin noma ta ƙasa da ƙasa da kuma kamfanonin cikin gida masu sarrafa Irin noma.

Ya kuma yi na’am, kan damar da Gwamnatin Jihar Ribas ta bayar, na amincewa da kafa cibiyar gudanar da binciken aikin noma, domin amfanin ƴan jihar.

Daraktan, ya kuma miƙa ƙoƙon bara ga ɗaukacin gwamnatocin da ke Arewacin ƙasar, da su yi koyi da gwamnatin ta Ribas.

A nasa jawabin, Farfesa Adamu Ahmed, Shugaban Jami’ar ABU, ya buƙaci mahalarta taron bitar da cewa, ba wai kaɗai mayar da hankalai kan samar da wadataccen abinci a ƙasar ba, su tabbata sun lalubo da wasu hanyoyin ingancin abininci, ta hanyar gudanar da bincike wanda hakan zai amfani ɗaukacin al’ummar ƙasar.

Adamu, wanda Mataimakinsa Farfesa Bello Sabo, ya wakilta a wajen taron, ya yi nuni da cewa, za a iya daƙile yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki ne kaɗai a ƙasar, ta hanyar zuba hannun jari a ɓangaren gudanar da bincike.

“Ina mai kira a gare ku, ba wai kaɗai gudanar da bincke ba, domin wallafawa ba, amma akwai matuƙar buƙatar lalubo da mafita kan ragewa ƴan ƙasar matsin tattalin arziƙin da suke ci gaba da fuskanta, ta hanyar yin amfani da fasahar kimiyyar zamani,” a cewar Adamu.

Taken taron bitar shi ne, rage ƙalubalen sauyin yanayin da ke haifar da illa a fannin aikin noma tare da ƙarfafa samar da wadataccen abinci.

Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Zaɓen Fitar Da Gwani: APC Na Fuskantar Barazanar Tawaye

Zaɓen Fitar Da Gwani: APC Na Fuskantar Barazanar Tawaye

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.