ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaɓen Fitar Da Gwani: APC Na Fuskantar Barazanar Tawaye

by Yusuf Shuaibu
2 months ago

Jam’iyyar APC na fuskantar barazanar tawaye daga fusatattun ƴan takara da suka sha kaye a zaɓen fitar da gwani, jam’iyyar mai mulki na fuskantar yiwuwar wata tawaye ta cikin gida da za ta iya lalata mata damar cin nasara a zaɓen 2027.

Barazanar da APC ke fuskanta za a iya kwatanta ta a matsayin wanda za a yi zato ba. An bayyana cewa mafi yawancin fusatattun ƴan takara ba su amince da tsarin zaɓen fid da gwanin ba a ciki jam’iyyar.

A tsakiyar guguwar da ke tasowa akwai wani rukuni na masu neman takara waɗanda suka zuba kuɗaɗe masu yawa, a wasu lokuta, suna kashe miliyoyin naira wajen sayan fom na nuna sha’awar tsayawa takara, sai dai su tsinci kansu an cire su daga katara, an yi watsar da su ko kuma an kayar da su ta hanyoyin da suke ganin ba a yi masu adalci ba.

ADVERTISEMENT

Abin da ya sa suka shiga wannan yanayi shi ne, wani tarkon doka da suka faɗa ciki ba tare da sun fahimci tasirinsa ba. Dokar zaɓe da aka gyara ƙarƙashin sashe na 77 na dokar zaɓe ta 2026, kowane mutum da ya san yana riƙe da kasancewar mamba na jam’iyyun siyasa biyu a lokaci guda zai rasa matsayin amincewa a matsayin sahihin mamba na kowanne jam’iyya, har sai an daidaita bisa tanadin dokar.

Ga ƴan takara masu amfani da katin mambobin jam’iyyu biyu a baya a matsayin zaɓi na siyasa mai inganci, wannan doka ta rufe ƙofa da ba su sani ba.

LABARAI MASU NASABA

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

Yawancin majiyoyi sun tabbatar da cewa sun fahimci cikakken nauyin wannan takunkumi ne kawai bayan sun riga sun sanya kuɗinsu a cikin tsarin farko. Idan an fuskanci rashin wani zaɓi na siyasa mai yiwuwa, lissafin yawancin waɗannan ƴan takara masu ƙorafi ya canza daga neman arziki a wani waje zuwa neman ramuwar gayya.

Ayyukan cin amanar jam’iyya, wanda shi ne makaman siyasa na cikin gida, sun zama wani mataki na ƙarshe ga waɗanda suka yi rashin nasara kuma suna tunanin ba a yi masu adalci ba.

Girman yawan waɗanda aka soke takararsu na da ban tsoro. Sama da ƴan takara 180 na APC a faɗin ƙasar sun fice daga zaɓukan fid da gwani. Har ila yau, an dakatar da dama daga jam’iyya, saboda haka sun sami kwarin giwar neman haƙƙinsu a kotu kan abin da suka bayyana a matsayin tilasta wa ƴan takara.

A wasu jihohi da dama, akwai hannun gwamnoni wajen tantance sakamako zaɓe. Samfurin amfani da hanyar masalaha, wanda a fili yake a matsayin wata hanya ta samun yarjejeniya cikin tsari, a aikace ya zama kamar hanyar talasta wa ƴan takara, inda manyan jami’an jihar ke amfani da ikonsu na tsarin jam’iyya don zaɓar masu biyayya kuma su gabatar da sakamakon a matsayin an yi amfani da hanyar masalaha a tsakanin ƴan takara.

Shugaban jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya mayar da martani ga barazanar da ke ƙaruwa wanda bai gamsar da kowanne ɓangare na muhawarar ba.

A cikin wata sanarwa na baya-bayan nan da wasu masu lura da jam’iyya suka bayyana a matsayin kamar zuba gishiri a kan rauni, Yilwatda ya yi barazanar ga fusatattun ƴan takara take barazanar tayar da tarzoma ko cin amanar jam’iyya waɗanda za su iya raunana ingancin tsarin zaɓen farko fid da gwani.

“A cikin kowace tsarin dimokuraɗiyya, mutum ɗaya ne kawai zai samu nasara. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, ci gaba da aiki tare. Ina ƙarfafa duk masu neman muƙami su nuna dattaku, ƙaunar ƙasa da kyakkyawar zuciya ta hanyar rungumar sakamakon zaɓen fitar da gwani domin amfanin jam’iyya da dimokuraɗiyyarmu gaba ɗaya,” in ji shi.

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

MASU ALAKA

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci
Siyasa

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

July 8, 2026
ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo
Manyan Labarai

ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

July 6, 2026
Jam’iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya – Hajiya Khadija
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya – Hajiya Khadija

July 5, 2026
Next Post
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya

Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

LABARAI MASU NASABA

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

July 14, 2026
Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160

Kyawawan Manufofin Buhari Za Su Ci Gaba Da Yi Wa ’Yan Nijeriya Tasiri – Tinubu

July 14, 2026
Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026
Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

July 13, 2026
Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

July 13, 2026
Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.