ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Ilimi, Duk Abin Da Ke Ɓoye Ya Fito Sarari (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
4 months ago
Sarari

…ci gaba daga makon da ya gabata. 

in ya sauka (Annabi) daga ilimi ya koma halittarsa – dabi’ar danAdam, yanzu shaidan zai biyo ta wani waje ya cusa na shi a ciki da fadin ubangiji, “iza tamanna alkash shaidanu fi umniyyatihi, fayansakhullahu ma yulƙish shaidanu summa yuhkimmullahu ayatihi”. Imma Allah ya goge wannan abun da shaidan din ya cusa, sannan ya tabbatar da nasa, ko kuma ya goge duka biyun. Su ma’aika (Manzonni), ba sa sauka akan ilimi su bi son zuciya (tamanni), sabida an ajiye musu masu gadi gaba da baya, “fa innahu yasluku min baini yadaihi wa min kalfihi rasadan“.

Shi Manzon, kamar Alkali ne, dole ya bi ilimi, kamar kotu ce wurin shari’a. In Malami ya yi kuskure a dakin bincike, duk al’umma zai shafa.

ADVERTISEMENT

Sau da yawa ake cewa, dakin bincike ya kama da wuta sabida kuskure a gwajin wasu sinadarai. Wannan kuskuren, masu gwajin kawai zai shafa amma kuskuren alkali, akan wadanda yake zai kare. Ubangiji tabaraka wata’ala, ya ce, ya tsare manzonninsa ne don su isar don su isar da ingantaccen sakonsa ga bayinsa, kuma ya musu shaidar sun isar da ingantaccen sakonsa, “Liya’alama an kad ablagu risalati rabbihim”.

  • Sharuɗan Da Chelle Ya Gindaya Wa NFF Domin Cigaba Da Jagorantar Super Eagles 
  • Duk Da Barazanar Amurka, Iran Ta Jaddada Aniyarta Na Cigaba Da Tace Makamashin Nukiliya 

Annabi SAW yana cewa, “Balligu anni walau aya – ku isar min da sako na ga al’ummata ko da aya ce,” don haka, tun daga zamanin sa, isar da sako ake yi, duk wanda ya karantar da aya guda ma ya isar da sakon manzon Allah SAW, ko an gane ko ba’a gane ba, ko shi (mai karantarwa” ya gane ko bai gane ba. Tun daga wancan lokaci har yanzu, haddatar da Alkur’ani ake yi, isar da sakon manzon Allah SAW ake yi, Aramma ya gane ko bai gane ba, almajirin ya gane ko bai gane ba, an dai isar da sakon Annabi SAW, har wata rana wannan Kur’ani ya je wajen wanda ya fahimci sakon dake ciki. Ana cewa, “Rubba hamilu fikihin ila afkahu minhu – dayawa mai isarwa ya isarwa wanda yafi shi fahimta”. Ba laifi a yi ta mayar da Alkur’ani littafin addu’a, wata rana, Allah zai kawo lokacin da zai zo wajen wasu ‘yan zamani, wanda zasu ajiye shi a dakin bincike, su tafi da shi da tsarin ilimi don sun samu gwala-gwalan ilimin dake cikinsa.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

Da shi za su shugabanci duniya, a wannan lokacin muradin Allah ya cika, watakila wannan zamanin ne, zamanin mahadi da ake fada ko zamanin annabi isa da ake fada, wanda zai zo da ilimi, da birnanta ka, wanda Muhiddini bil Arabi ya fada.

“Kad Ablagu risalati rabbihim, wa a hada bima ladaihim, wa ahsa kulla shai’in ilma – lallai Manzonnin sun isar da sakon da suka amso, Allah yasan abunda yake garesu na ilimi, kuma komai a lissafe yake a wurin shi”. Komai na kididdige shi, (na bambance komai). Toh dan haka, duk inda kaga lissafi da kididdiga a Kur’ani, toh zaka ga zancen gaibu a wajen.

Don haka, zaka ji masanan wannan ilimi suna fadar abunda zai zo, da abin da ya buya, zasu fadi abubuwan da suka buya na halitta, zasu fadi abin da yake cikin mahaifa, zasu fadi ilimin yanayin sararin samaniya; lokacin ruwa, iska, sanyi, ko zafi, zasu fadi lokacin girgizar kasa tun kafin ayi girgizar kasan kuma kaga anyi, zasu fadi lokacin da dutse zai yi aman wuta tun kafin yayi kuma yayi, zasu fadi rana za tayi kusufi a lokaci kaza kuma tayi, zasu fadi wata zai yi kusufi a lokaci kaza kuma yayi, yau ya zama gaibu karewa take yi.

Don haka, ka kawar da kai ga jahili mai cewa, Annabinsa ma bai san gaibu ba wanda yau ga shi kusan kowa ya santa da ilimin da Annabin (SAW) ya zo da shi. Annabi SAW ya san duk wannan ilimin na lissafi.

Abun mamaki, ba wata ruwaya da za’ace sahabai sun tambayi manzon Allah SAW cewa, meye “alif lam mim”, kuraman baki? ma’ana suna sane da ita. Abin da aka rawaito mana da alif lam mim, shi ne, da ta sauka, Yahudawa da suka ji, sai suka ce ashe zamu huta da shi, ma’ana shekara sittin ne da nawa a kirgen su (Annabi SAW), sai suka ji kuma “tha sin mim” ta sauka sai suka ce yanzu abun yafi karfin hankalin mu.

Wannan ya nuna cewa, sun san ma’anar su tun da suma ahlul kitabi ne suna da littafi, “Awalam yakun lahum ayatan anya’alamahu ulama’u bani isra’il”. Misali, yanzu-yanzu wani ya dawo daga Amurka, sai yace jiya kamar yanzun ina USA amma yau kuma gani a Nijeriya.

USA, Amurka yake nufi, haka kuraman bakin nan, wanda ya sani, ya sani.

Don haka, wanda ya san wannan ilimi, zai san gaibu, don Allah, wanda bai san wannan ilimi ba, ya yi shiru da maganan gaibu.

Don haka, kasa tana samun daukaka da cigaba da Kur’ani, ma’ana tana cigaba in tana aiki da ummul kitabi muhukami mai adalci wajen shari’a. in dai kasa ta kula da ilimi da adalci, za ta daukakawa, kuma kowace kasa ce, musamman in aka ce ta ware mafi yawan kasafin kudinta a bangaren ilimi da binciken kimiyya, toh lallai wannan kasa ta kusa da ta zama kasar musulunci.

Kasa, in an ce ta zama kasar Musulunci, ba shi ne ta zama kasar fikihu ba, sai dai zancen yanke hannu, da jefe mazinaci, wannan dakikanci ne, duk kasar da tabi tsarin ummul kitabi, da adalci, to yanzu ta kusa da daular musulunci sabida ta kusa da Kur’ani, “… bal huwa ayatun bayyinat”.

Kasar da ta yadda da cigaban ilimi, lallai zata bunkasa wajen ma’aikatu, sabida in ilimi ya bunkasa, ma’aikatu sun bunkasa. Harkan noma zata bunkasa, tattalin arzikin zai habaka.

Kasuwanci zai bunkasa, dan ilimi yana daga cikin abin da yake kawo cigaban kasuwanci. Yanzu kasuwanci ma na fahimta ake yi, na ilimi, ba sai mutum ya kai hajoji kasuwa ba, wani kirkira Allah ya yassare masa, zai zo da ita, kuma ya yi mata farashi mai kyau, sannan a saya, nan da nan kaji kasashe suna rige-rigen saya, kafin wani lokaci, an tara makudan kudade, duk albarkar Ilimi.

Da binciken ilimi, likitanci ke bunkasa, sannan dukkan ayyuka ma zasu bunkasa.

Shehu Ibrahim Inyas (RA), yana cewa, in nace ilimi, ba fa ina nufin na tafsiri ko na fikihu ba, ina nufin duk wannan ilimin na halittar danAdam (Kimiyya da fasaha), inda ya kara da cewa, in zaku iya hawa duniyar wata ma, kuje ku hau, in zaku iya kaza da kaza duk kuje ku yi.

Amma abin da muka taso muka ganmu a kai, to har yau shi muke tafe a kai. Galibi, bare irin kasashen mu na Hausa, Malami shi ne kawai wanda ke karantar da Ilimin Shari’ar musulunci. Malamin da ke karantar da ilimin boko da kimiyya da fasaha, shi ma Malam ne, kuma mataki mataki ne, tun daga Malamin firamare, har zuwa Farfesa, kuma har ya tsallake ya tafi kasashen waje don gogayya da sauran takwarorinsa domin bincike a wani fanni na musamman, wanda daga nan, za a fara cewa, wane ne ya kirkiro sanin kaza da kaza.

Daga nan mutum zai san duk yadda ake kirkiro sabbin abubuwa, zai san halitta, zai san shi kansa danAdam, “anan nafsu wal afaku…”, sabida ilimi ya sabunta. Me ya hana mu mu musulmi mu cigaba? Me hana mu mu sabunta karatukan mu? sabida bamu yarda cewa nan gaba akwai fahimta ba. Duk abin da za a yi magana a kai, sai dai a ce a koma maganganun magabata, mu koma wato da cewa, fiyayyan karni karnin manzon Allah (SAW) sannan karnin da yake binsa sannan karnin da yake binsa kila karnin da yake binsa da shekara dari hudu. To duk abunda muke so, nan muke so mu koma, don haka, dole

zamu tsaya wuri daya.

Sarari
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Next Post
GORON JUMA’A 06-03-2026

GORON JUMA'A 06-03-2026

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.