ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Tabka Asarar Manoma A Noman Tattasan Rani Na Bana

by Abubakar Abba
5 months ago

Wasu daga cikin manoma da suka yi noman rani na tattasai, musamman nau’in da ake kira a turance ‘scotch bonnet habanero’, a Arewacin kasar nan, sun tabka mummunar asara mai yawa.

Kazakila, su ma wasu diloli na tattasan da suka saro shi daga wasu kasuwannin da ke yankin, asarar ta shafe su kai tsaye.

Hakan ya faru ne dai, biyan faduwar farashin tattasan, inda hakan ke ci gaba da jefa su cikin damuwa sakamakon asarar da suka tafka.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikin manoman nau’ikan tattasan, Alhaji Muhammed Sani Sulaiman, wanda yake zaune a Karamar Hukumar Saminaka ta Jihar Kaduna, ya sanar da cewa; mafi akasarin manoman, ba su samu wata riba ta a zo a gani ba, bayan sun kammala girbi.

Ya kara da cewa, ya kashe dimbin kudaden da suka kai kusan kimanin naira miliyan bakwai wajen  sayen takin zamani da man fetur, wanda ya zuba a injin ban ruwa domin yin noma da kuma takin gargajiya da sayen maganin kashe kwari, amma kuma farashin amfanin ya sai ya yi matukar raguwa.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Ya ci gaba da cewa, a baya kafin faduwar farashinsu, suna sayar da duk buhu daya na nau’ikan biyu a kan sama da naira 30,000, inda ya kara da cewa; amma a noman ranin da suka yi na bana, ko naira 200,000, manoman ba su iya samu ba bayan sun yi girbi.

Shi ma wani manomin mai suna Haruna Idris, ya bayyana cewa; a farko, duk buhu daya na nau’ikan biyu, ana sayarwa ne a kan naira 30,000, amma daga baya, farashin ya sauka zuwa naira 4,000.

Ya ce, ya san cewa; akwai wasu manoman da suka sayar da gonakinsu da gidajensu da sauran makamantansu, domin zuba jari a noman nau’ikan tattasan biyu, amma bayan faduwar farashinsu, sai suka tabka mummunar asara.

Kazalika, shi ma wani manomin mai suna Ibrahim Abubakar Aminu, wanda kuma shi ne, shugaban ‘yan kasuwa masu sayar da tumatir a kasar, wanda yake  zaune Karamar Hukumar Saminaka ya sanar da cewa; manoman sun fuskanci matsaloli daban-daban a kakar noman ranin ta bana.

A cewarsa, a shekarar da ta wuce, an sayar da duk buhu daya na nau’ikan a kan naira 50,000 zuwa naira 55,000, amma a kakar noman bana, farashin nau’ikan biyu, ya ragu daga naira  5,000 zuwa naira 7,000, inda hakan ya sanya manoman yin asara mai dimbin yawa.

Shi kuwa wani dan kasuwa mai suna Sani Zubairu Garko, a yankin na Saminaka cewa ya yi, su ma ba su samu wata ribar kirki wajen sayar da amfanin biyu ba.

Haka nan, shi ma wani mai suna Malam Ibrahim Zakariya Dan Kaduna, wanda dilan sayar da tumatir ne a yankin Saminaka, ya sanar da cewa; manoman sun fara fuskantar wannan matsala ce, tun kafin bikin Kirisimeti na bana.

“Mun kai buhunhunan tattasan zuwa kasuwannin da ke Jihar Legas, inda muka sayar da duk buhu guda a kan naira 1,000,“ in ji shi.

“Har yanzu, akwai wasunmu da ake bi bashi, domin mun ciwo bashi ne, don mu kara habaka hada-hadar kasuwancinmu, amma kuma sai muka tafka wannan asara,” a cewar tasa.

Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Sin Da Somalia Sun Kaddamar Da Cibiyar Bincike Game Da Salon Zamanantarwa Irin Na Sin

Sin Da Somalia Sun Kaddamar Da Cibiyar Bincike Game Da Salon Zamanantarwa Irin Na Sin

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.