ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussa Daga Ramadan Na (3)

by Nuhu Ubale Ibrahim
7 months ago
Darussa

A cikin watan Ramalana, mumini yana koyon miƙa dukkan buƙatunsa da burace-buracensa zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki, saboda girmansa, karamcinsa da yalwar rahamarsa.

Ramalana wata ne na kusanci da Ubangiji, wata ne da ƙofofin alheri suke a buɗe, kuma zuciya take samun tsarkaka, ruhi kuma ya sami wata irin nutsuwa, kuma addu’a ta fi kusa da karɓuwa. Allah Maɗaukaki Yana saka wa bayinsa da suka yi aikin alheri da sakamako mai,. matuƙar an yi aikin da ikhlasi yadda Manzon rahama (S.A.W) ya koyara. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ” Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan’adam nasa ne, sai dai azumi; domin azumi Nawa ne, kuma Ni ne Zan saka masa” Bukhari ne ya ruwaito.

  • Darussa Daga Ramadan Na (1)
  • Darussa Daga Ramadan Na (2)

Wannan hadisi mai girma yana nuna mana matsayin azumi a wurin Allah. Azumi ibada ce ta sirri, babu mai sanin haƙiƙanin gaskiyarta sai Allah. Saboda haka Allah Ya keɓe lada da sakamakonta gare Shi kaɗai, alamar girman darajarta da yalwar sakamakonta.

ADVERTISEMENT

Ramalana wata ne da ya kamata mu haɗa abubuwa uku:

1. Ikhlasi a aiki: watau yin ibada don neman yardar Allah kaɗai, ba don yabo ko gani na mutane ba.
2. Bin dokokin Allah: kiyaye umurninsa da nisantar hane-hanensa, domin ibada ba ta kammala sai da taƙawa.
3. Yawaita addu’a: domin Allah Ya fi kusa da bawansa a wannan wata mai albarka.

LABARAI MASU NASABA

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

Menene Hukuncin Yin Aure Da Cikin Shege?

Addu’a ita ce makamin mumini. A Ramalana, musamman a lokutan da ake azumi, lokacin buɗa baki, da lokacin yin sahur da cikin Laylatul-Ƙadri, ya dace mumini ya miƙa zuciyarsa gaba ɗaya ga Allah. Ya roƙi gafara, ya roƙi gyaran rayuwarsa, ya roƙi albarka a cikin iyalinsa, ya roƙi shiriya da tsayuwar daka kan addinin Allah Ta’ala.

Abu ne mai matuƙar muhimmanci mu fahimci cewa karɓuwar addu’a tana buƙatar tsarkin zuciya da ci da sha da tufafi na halal. Wanda ya tsarkake zuciyarsa daga hassada, riya da zalunci, ya nisanci haram, ya kuma dage da neman halal, to ya fi kusa da samun amsa addu’a.
Saboda haka, a yi aiki da ikhlasi. A gyara niyya. A riƙe azumi ba kawai da yunwa da ƙishirwa ba, har da azumin idanu, da kunne da harshe. A nisanci gulma da saɓo. A kuma miƙa buƙatu da cikakken yaƙini cewa Allah Mai jin ƙorafi ne, Mai amsa addu’a ne.

Kada mumini ya yanke ƙauna idan bai ga sakamakon addu’arsa nan take ba. Wani lokaci Allah Yana amsa addu’a ta hanyoyi uku: ko Ya ba ka abin da ka roƙa, ko Ya kawar maka da wata masifa makamanciyarta, ko Ya adana maka lada a Lahira. Duk waɗannan alheri ne.

Ramalana wata ne na fata da bushara. Wata ne da Allah Yake karɓar tuba, Yake gafarta zunubai, Ya kuma ɗaukaka darajoji. Don haka ka shiga Ramalana da zuciya mai tawakkali, da harshe mai ambaton Allah, da zuciya mai fatan rahama.

Allah Ya sa mu dace da yin azumi da ikhlasi, Ya karɓi addu’o’inmu, Ya kuma sanya mu cikin bayinsa waɗanda Yake alfahari da su a gaban mala’iku. Amin.

Darussa
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22

MASU ALAKA

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
Ta’aziyya

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

August 2, 2026
Yadda Jariri Ke Koyon Tsotsar Nonon Uwa Kafin Haihuwa
Fatawa

Menene Hukuncin Yin Aure Da Cikin Shege?

June 21, 2026
Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
Bakon Marubuci

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

May 27, 2026
Next Post
Karin Shugabannin Kasashe Da Na Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Mika Fatan Alheri Ga Sabuwar Shekarar Doki Ta Sinawa

Karin Shugabannin Kasashe Da Na Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Mika Fatan Alheri Ga Sabuwar Shekarar Doki Ta Sinawa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.