ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dawowar Ayyukan ‘Yan Kunar Bakin Wake

by Abubakar Abba
2 months ago
Wake

Lokacin da ‘yan Nijeriya suka fara tunanin ko sun yi bankwana da nau’oin Bama- Baman da suka auku a shekarun baya, kamar ba za su sake aukuwa ba, sai dai ina ba’a bar garin ba sai ga Kura. Litinin din da ta gabata a makon da ya wuce sai ga masu nasa Bama- Bamai da yawai sun kai hare- hare a Asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri sai kuma kasuwanni biyu, da Post Office da kuma kasuwar Mande inda suka kashe a kalla mutane 23 sai kuma 108 wadanda suka samu raunuka. Bom ya fashe ne a kofar shiga Asibitin, wato wurin da mutane suke zuwa domin neman magani can ne kuma wurin da ake rasa rayuwa.

Ga mu wadanda su ka kasance cikin lafiya, a tskanin shekarun 2011 kuma 2015, abubuwan da suka faru a Maiduguri makon da ya gabata abin da akwai zafi ya yi kuma kama da irin abubuwan da suka faru a wancan lokacin na ‘yan Boko Haram. Zuwa Coci ko Masallaci wani babban aiki ne mai wuyar tunkara. ‘Yan kasuwa mata suna yin addu’arsu kafin su fita daga gida domin sayar da Tumatir. Kare kofofin shiga zuwa wuraren addu’a sai abin ya zama an saba da shi ne.An rufe makarantu na  makonni a lokacin. Iyaye a Arewa maso gabashin Nijeriya tsoro suke yi na aiken ‘ya’yansu zuwa wani wuri. Sannu a hankali kuma, sai Sojoji suka samu damar murkushe ‘yan Boko Haram, suka sake karbar wuraren da aka kwace masu, amma masu kai kunar Bakin Wake sun ragu. Maiduguri ta dade bata samun irin harin Bom na shekarar 2021.’Yan Nijeriya na tunanin kamar ba zai sake aukuwa ba.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa ta tabbatar da yawan mutanen da suka mutu. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta Jihar Borno Nahum Kenneth Dasos ya tabbatar da cewa binciken da aka yi ya nuna hare- haren da aka kai ‘yan kunar Bakin wake nr su ka kai shi. Ana ci gaba da bincike sosai, don haka za mu bar su, su yiu aikinsu.

ADVERTISEMENT

Abin da ba za ayi gardama kan shi ba shi ne irin yadda aka kai shi harin.A watan da ya wuce kadai, kungiyoyin Boko Haram da (ISWAP) sun kai hare- hare a sansanonin Sojoji da ke Jihar Borno, suka kashe a kalla Sojoji 50 da kuma yin gaba da makamai. Sojoji hamsin lalle abin ba karamin abu bane.Yawan Sojojin da suka rasa ransu ya kamata ace a ci gaba da ganin  nambar a shafin farko a jaridu, amma si muka nuna abin bai dame mu ba,  amma sai muka zama wasu irin mutane wajen nuna abin bai dame mu ba, kai hare- haren da ake yi sashen Arewa maso gabas, domin kuwa lamarin mutuwar Sojojin abin ya dan karade kafafen sadarwa na zamani awa 24 ne kawai, kafin mu koma maganar gulma ko gutsuri tsoma.Kasar da bata nuna alhinin mutuwar Sojojinta sosai babu wani abin da za ta iya yi wajen nuna damuwa da alhinin rasuwar Sojojinta kamar yada ya dace, babu wani abinda da za su yi wajen nuna damuwa dangane halin da tsaro yake a kasar.

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi abin,a yaba ma shi, wajen daukar matakin da ya yi da sauri. Ya nuna rashin jin dadin sa, ya kuma mika sakon ta’aziyar shi, ya umarci manyan jami’an tsaro su koma Maiduguri domin yin abinda ya dace. Da kyau haka ake bukata. Dama abinda babban kwamandan askarawan soja ya dace ya yi ke nan. Sai dai kuma mun saba da jin irin hakan. Domin Shugabannin kasa sun ba da umarni ga manyan jami’an tsaro su koma wurin da lalacewar tsaro da ta’addanci abin ya fi kamari fiye da tunawar mutum. Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ma ya yi hakan lokutta masu yawa sai dai kuma duk da haka har yanzu muna kirga gawa ta wadanda aka kashe mu ke yi. Tambaya anan ita ce me ya ke faruwa ne bayan suka je wurin bayan yin kwanaki ba masu yawa ba, sai su koma Abuja. Za a ci gaba ne da maida hankali ne a wurin ko wuraren, ko amfani da dabarun asiri na Soja, ko kuma daga karshe zai kasance ne kamar yadda aka saba yi ko wane lokaci ne?‘yan Nijeriya sun gaji da lamarin hare- hare, bakin ciki, da zama cikin zullumi, tsugunnar damu ko maida mu zuwa wani wuri, mu kasance shiru,an manta da mu har sai kuma zuwa wani lokacin da Bom ya kara tashi.

LABARAI MASU NASABA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

Harin Bom ai kai shi kasa da awa 24 bayan da Sojoji sun murkushe wani harin da aka kai masu a wajen Maiduguri. Wannan na nufin cikin kwana biyu, Birnin da aka san ramkar wata mahaifa ce ta ‘yan kungiyar Boko Haram ta fuskanci abubuwa biyu da suke da nasaba da tsaro. Hakan na iya muna mana a fili cewa akwai wani abu domin su ‘yan  ta’addar ba karamin shiri suka yi ba, suna kuma da abinda ake kira da suna babu gajiya tattare da su bare wani lalaci ko yaushe a shirye suke.Har yanzu ba a samu wata babbar nasara kansu ba.Suna sake harhaduwa, samar da sabbin salon kai hare- hare domin sun gane wuraren da muke da nakasu.

Ga masu tunanin wasu abubuwa na iya faruwa ko a aiwatar da su.  Kamar yadda aka sa rai ruwan sama watan Yuli a Legas, wasu mutane sun fara maganar an shirya kai hare- haren Bama- baman ne domin a kunya ta mulkin Tinubu. Ko kuma a hana shi shirin tafiyar da yake son yi zuwa hadaddiyar daular Turawa.

Kamar yadda ‘yan adawa suke kallon lamarin tafiyar ta Tinubu zuwa London kamar za ta kara ma shi tagomashi nan da zabubbukan shekara ta 2027.Na ji abubuwa masu daure kai da ban dariya a matsayi na wanda na ke kula da lamurran da suka shafi siyasar Nijeriya, amma wannan ya dace a bada nambar girmamawa ta musamman.

Irin wannan tunanin ne ya ke damuwar wadanda abin ya samu tare da iyalansu.

Maganar gaskiya ce ta dace ayi domin kuwa duk wanda yake daukar nauyin ta’addanci saboda samun wani tagomashi na siyasa ya fi su masu yin ta’addancin. Dan ta’adda wani  mutum ne da wani ra’ayi ke jan hankalin shi ya yi hakan,  shi kuma wanda ke daukar nauyin yana da wata manufa ta daban. Idan akwai gaskiyar da za a dogara da ita mai nuna akwai wasu ‘yan siyasa da suke kafa wadannan kungiyoyin, na kuma ji wannan magana daga wata kafa ta tsaro a shekarun da suka gabata, don haka ne ma gwamnatin Tinubu babu wata afuwa da za ta nema ayi mata akan haka, kamata ya yi ya bi ta kansu. Kar a damu da ko wanene abin ya shafa.An dade ana ta maganar wadanda suke daukar nauyin ta’addabci tun zamanin mulkin Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

Masu daukar nauyin ta’addanci nawa ne aka kama?  Nawa ne kuma ala yanke masu hukunci? Nawa ne suke zama a gidan gyara halinka yanzu? Amsar ita ce babu kowa.

Wannan babbar matsala ce. Ba wai kawai a tsaya kan maganar wanda yake daukar nauyin ta’addancin ba amma a fada ba a cikawa hakan ma wani laifi ne, amma me ya sa kasar da ta yi asarar mutanen ta dubbai sanadiyar ta’addanci a shekaru sha biyar, amma har yanzu bata kashe ko da mutum daya ba daga cikin masu daukar nauyin.Kudaden da ake sayo makaman, motoci,da sauran kaya ai daga wani wuri suke zuwa. Abi hanyar da kudin ya shigo domin kama wanda ya biya. A hukumta su a gaban al’umma. Kamata ya yi ‘yan Nijeriya su san cewa da akwai doka dole ne kuma ta yi aikin kan duk wanda ya ki yakar zuciyar

Wake
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Hukumar FAO Ta Samar Da Shirin Kiwon Tarwada A Jihar Gombe
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilin Da Ya Sa Matatar Dangote Ta Kara Habaka Tura Man Fetur
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Manoma 67 Suka Amfana Da Horon Cibiyar  NIHORT
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilan Da Suka Sa Fannin Kiwo Ke Fuskantar Kalubale A Nijeriya —Gwamnatin Tarayya

MASU ALAKA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki
Bakon Marubuci

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

June 12, 2026
A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara
Bakon Marubuci

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

June 12, 2026
‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
Bakon Marubuci

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

June 5, 2026
Next Post
Yadda Rayukan Mutane Sama Da 86 Suka Salwanta A Kan Titin Nnamdi Azikiwe Da Ke Kaduna

Yadda Rayukan Mutane Sama Da 86 Suka Salwanta A Kan Titin Nnamdi Azikiwe Da Ke Kaduna

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Zaɓi Amaechi A Matsayin Mataimakin Atiku A Zaɓen 2027

ADC Ta Zaɓi Amaechi A Matsayin Mataimakin Atiku A Zaɓen 2027

June 15, 2026
Xi Jinping: Zan Sadaukar Da Rayuwata Don Bautawa Jama’a

Xi Jinping: Zan Sadaukar Da Rayuwata Don Bautawa Jama’a

June 15, 2026
Annobar Ƙwalara Ta Kashe Mutane Biyar, 11 Sun Kamu A Filato

Annobar Ƙwalara Ta Kashe Mutane Biyar, 11 Sun Kamu A Filato

June 15, 2026
Farashin Mai Ya Fadi Rigis Bayan Amurka Da Iran Sun Sasanta Kan Mashigar Hormuz

Farashin Mai Ya Fadi Rigis Bayan Amurka Da Iran Sun Sasanta Kan Mashigar Hormuz

June 15, 2026
An Daure Ɗan Gidan Gimbiyar Masarautar Norway Shekara 4 Kan Laifin Fyaɗe

An Daure Ɗan Gidan Gimbiyar Masarautar Norway Shekara 4 Kan Laifin Fyaɗe

June 15, 2026
An Yi Wa Mata 600 Gwajin Cutar Sankarar Mama, An Yi Wa 50 Tiyata A Katsina

An Yi Wa Mata 600 Gwajin Cutar Sankarar Mama, An Yi Wa 50 Tiyata A Katsina

June 15, 2026
Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Uku Yayin Zazzafar Musayar Wuta

Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Uku Yayin Zazzafar Musayar Wuta

June 15, 2026
Jamus Ta Sake Yi Wa Abokiyar Karawarta Ruwan Ƙwallaye 7 A Gasar Kofin Duniya

Jamus Ta Sake Yi Wa Abokiyar Karawarta Ruwan Ƙwallaye 7 A Gasar Kofin Duniya

June 14, 2026
Ministoci Da Gwamnoni Za a Koma Kai Wa Hari Nan Gaba – Buratai

Ministoci Da Gwamnoni Za a Koma Kai Wa Hari Nan Gaba – Buratai

June 14, 2026
Jigilar Hajoji Ta Jiragen Kasa Na Gudana Bisa Daidaito A Kasar Sin

Jigilar Hajoji Ta Jiragen Kasa Na Gudana Bisa Daidaito A Kasar Sin

June 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.