ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Ne Afirka Ta Zamanantar Da Sufurin Jiragen Ruwa —Ɗantsoho

by Bello Hamza
1 month ago
Ruwa

Afirka ba za iya cimma burinta na bunƙasa tattalin arziki, idan ba a samar da kayan aiki na zamani, a Tashoshin Jiragen Ruwa a nahiyar  ba.

Dakta Abubakar Ɗantsoho, Shugaban Ƙungiyar makuntan kula da hada-hadar sufurin Jiragen Ruwa ta Gabas da kuma Afirka ta Tsakiya wato PMAWCA, ya yi wannan gargaɗin.

Ɗantsoho wanda kuma shi ne, Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta ƙasa NPA, ya yi wannan gargaɗin ne, yayin rufe taron ƙungiyar ta PMAWCA, na tsakiyar shekara, da ya gudana a jihar Legas.

ADVERTISEMENT

Jiga-jiagan masu ruwa da tsaki a fannin sufurin Jiragen Ruwa da da suka halrci taron, na kwana biyu.

Wasu daga cikin batutuwan da suka tattauna, sun haɗa da, makomar ƙara bunƙasa fannin da kuma ƙara ƙarfafa hada-hadar kawunci, ta hanyar yin amfani da Tashoshin Jiragen Ruwa, a Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

Kazalika, Ɗantsoho ya sanar da buƙatar da a ci gaba da zuba jari a ɓangaren yin amfani da kayan zamani a fannin.

Ya ce, hakan zai bai wa Afirka damar yin gasa da sauran Hukomomin kula da sufurin Jiragen Ruwa na duniya.

Ɗantsoho  ya ci gaba da cewa,  a taron ɗaukacin ƙasashen da ke a Gabas da kuma Afirka ta Tsakiya.

A cewarsa, mahalarta taron, sun kuma cimma matsayar cewa, akwai buƙatar a zamantara da fannin wanda hakan, zai ƙara ƙarfafa zirga-zirgar Jiragen Ruwa, a cikin sauƙi.

Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa na Afirka, su ne, kan gaba wajen bunƙasa tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa, babu wata ƙasa a duniya, da za ta iya faɗaɗa tattalin arzikinta, ba tare da zuba jari, domin yin aiki da kayan zamani a Tashshin Jiragen Ruwa ba.

“Wannan fannin ne, da ke da buƙatar, a zuba jari, mai ɗimbin yawa na kayan aikin na zamani,” Inji  Ɗantsoho.

“Ba za iya samun wata cin nasara a fannin ba, matuƙar ana ci gaba da yin amfani da tsaffin kayan aiki,” Inji shi.

Ɗantsoho ya ci gaba da cewa, tuni ƙasashe da dama da ke a yankin, cikinsu har da Nijeriya, Ghana, Senegal, Côte d’Iɓoire, da kuma Jamhuriyar Benin, suka yi nisa wajen yin aikin zamanantar da kayan da ke a Tashoshin Jiragen Ruwansu.

Ya ƙara da cewa, sun yi hakan ne, bisa nufin ƙara inganta ayyukansu, bisa ƙoƙarin yin gasa da sauran na duniya.

A cewarsa, a yanzu haka, ana kan aikin yiwa kayan aiki na Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da Tin Can Island garanbawul.

Ya ce, ana yin hakan ne ta hanyar samar da ɗauki, na dogon zango, wanda hakan, zai ba su damar ruɓanya hada-hadar kasuwanci.

A yake buga misalai da aikin guraren sauka kaya kaya da kuma yin lodi da ke Tashar Lekki, ya  ce, an yi nisa a wajen aikin,.

Ya jaddada buƙatar da a ƙara bunƙasa wasu irin waɗannan guraren na saukewa da kuma yin lodin, musamman waɗanda za  a rinƙa sauke kaya masu yawa.

“A ƙasar Singapore, ana gina irinsu, tare da kuma keɓe wasu gurare da za a iya saukewa da kuma loda kaya, haka ƙasar Guinea na kan aikin gina ƙaramar Tasha kan dala biliyan 20,” A cewarsa.

“Irin wannan zuba jarin ne, ya kamata a fara yi a Afirka, mutuƙar, muna son mu yi gasa da sauran ƙasashen duniya,” A cewar Ɗantsoho.

Ɗantsoho ya zayyano wasu daga cikin ƙarin gudunmawar da kimiyyar zamani ke ci gaba da bayar wa, wajen ƙara inganta ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa kamar yin amfani da fasahar AI da sauransu.

Ya ce, NPA ta samu cimma kaso 90, a gudanar da ayyukanta ta a hanyar yin amfani da tsarin biyan kuɗaɗe da sauka kaya, a Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar wanda hakan, ya ƙara haɓaka ayyukanta.

“A yau za ku iya shiga cikin Tasahar Tasahar Apapa ku kuma fita, ba tare da wani ɓata lokaci ba, saɓanin yadda a baya, ake ɓata lokaci saboda tsagwaron cunkoson  da ake samu,” Inji Ɗantsoho

Ɗantsoho ya ƙara da cewa, a yau ana samun sama da kaso 70 na rage cunkosn Jiregen da ke shiga Tashishin da kaya, a Tashoshin Jiragen da ke a Gabas da Afirka ta Tsakiya, musammman waɗanda ke a ƙasashen Nijar, Chad, Mali, da Burkina Faso.

Ya jaddada buƙatar haɗaka a tsakanin yankunan da kuma ƙara samun ilimi, a ƙarƙashin ƙungiyar ta PMAWCA.

Ya ce, ƙasashen da ke a cikin ƙungiyar, na ci gaba da ƙara  yin musayar bayanai, domin domin a ƙara ƙarfafa inganta ayyukansu.

Ɗantsoho ya nanata cewa,  makomar  tattalin arzikin Afirka, ya dogara ne kachokam ga hada-hadar sufurin Jiragen Ruwa, musamman idan aka rungumi yin aiki, da kayan zamani

Shi kuwa a na sa jawabin Minitsna Bunƙasa Tattalin Arziki na Teku Dakta Adegboyega Oyetola, kira ya yi da a rungumi yin aiki da kayan zamani, domin a ƙara haɓaka ayyukan fannin a Afirka.

Oyetola, wanda Daraktan Sashen Gudanarwa na Sufurin Jiragen Ruwa Oyinloye Meshack, ya wakilce shi a wajen taron ya ce, taron ya nuna yadda ƙasashen da ke a cikin ƙungiyar, suka  ƙara mayar da hankali domin rungumar yin amfani da kayan aiki, na zamani, a fannin.

Ya yi nuni da cewa, hakan zai ƙara bayar da dama, wajen ƙara samar da alƙibla ga fannin da kuma ƙara haɓaka yin gasa a tsakanin Tashoshin da ke a Afirka da kuma ƙara bunƙasa tattalin arzikin da ke a fannin.

Oyetola ya kuma yi na’am, da irin shugabancin da ake gudanarwa a ƙungiyar ta PMAWCA, musamman a wajen ƙara ƙarfafa haɗin kai, a ɗaukacin Gabas da kuma a Afirka ta Tsakiya.

Oyetola ya buƙaci masu ruwa da tsaki a fannin, da su tabbatar da sun ƙara wanzar da shawarwarin da aka cimma, a taron.

Ya ce, yin hakan, zai ƙara ƙarfafa yin gasa, a tsakain Tashoshin Jiragen Ruwan da ke a yankin tare da buɗe wani sabon babi, na samun damar bunƙasa tattalin arziki na Teku.

Ya jaddada goyon bayan Nijeriya, wajen ci gaba da yin haɗaka, a yankin, inda ya ce, fannin ya dogara ne, ga samar da kayan aiki na zamani

Ruwa
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

MASU ALAKA

NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN
Tattalin Arziki

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

June 27, 2026
Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani
Tattalin Arziki

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

June 26, 2026
Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya
Tattalin Arziki

Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya

June 20, 2026
Next Post
Nijeriya Ta Yi Asarar Biliyoyin Naira Saboda Dakatar Da Shigo Da Motoci Ta Iyakokinta

Ministocin Da Suka Ajiye Muƙamansu Ba Su Samu Tikitin Takara Ba

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Mutane 80 Sun Rasu Sakamakon Rikicin Ƙabilanci

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Mutane 80 Sun Rasu Sakamakon Rikicin Ƙabilanci

July 7, 2026
Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

July 7, 2026
Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

July 7, 2026
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

ADC Ta Zargi Gwamnatin Tinubu Da Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 17 Cikin Yunwa

July 7, 2026
Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

July 6, 2026
Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

July 6, 2026
Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

July 6, 2026
Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

July 6, 2026
FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

Shugabannin Sin Da Montenegro Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

July 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.