ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministocin Da Suka Ajiye Muƙamansu Ba Su Samu Tikitin Takara Ba

by Sani Anwar
3 months ago
Ministoci

Lissafin siyasa tare da ƙarfin halin da wasu daga cikin Ministocin Shugaba Bola Tinubu suka yi gabanin zaɓen 2027, ya rikiɗe zuwa wani abu mai kama da caca, domin kuwa ya haifar da sakamako maras daɗi.

Bisa umarnin fadar shugaban ƙasa, wasu ministoci da dama sun yi murabus daga majalisar zartarwa ta tarayya, domin ci gaba da gudanar da zaɓukan fid da gwani na jam’iyyar APC mai mulki.

Sai dai, maimakon samun nasara a takarkarun, da dama daga cikin tsoffin ministocin, sun tsinci kansu a cikin halin ƙaƙa-na-ka-yi, inda suka rasa muƙamansu na majalisar ministoci da kuma burinsu na samun tikitin jam’iyya.

ADVERTISEMENT

Ya zuwa yanzu dai, biyu ne kaɗai daga cikin biyar da suka sauka daga muƙamansu, suka samu tikitin tsayawa takara a zaɓen fid da gwani.

Wasu kuma sun sha kashi na wulaƙanci, jayayya ko rashin tabbas, kan makomar siyasarsu.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Daga cikin waɗanda suka yi murabus ɗin, akwai tsohon ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu; tsohon ministan sufuri, Saidu Alkali; tsohon ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar; tsohuwar ministar kwadago da samar da ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha; da kuma tsohon ƙaramin ministan harkokin jin ƙai, Yusuf Sununu.

Yayin da Onyejeocha da Sununu suka yi nasarar samun tikitin jam’iyyar APC a Jihohin Abia da Kebbi, inda cikar burin siyasar sauran ta durƙushe ko kuma ta ci tura.

Adebayo Adelabu

Adelabu ya yi murabus a matsayin Ministan Wutar Lantarki, domin neman tikitin takarar gwamna a APC a Jihar Oyo. Sai dai, tsohon ministan ya sha kaye a hannun Sanata Sarafadeen Alli, a lokacin zaɓen fid da gwani.

Alli ya samu ƙuri’u 578,143, yayin da Adelabu ya samu ƙuri’u 19,193 kacal.

Jim kaɗan bayan ya yi murabus ne, ƴan jarida suka tambaye shi ko ya ji labari yana ta yawo cewa; Shugaba Bola Tinubu na mara wa Alli baya, sai tsohon ministan ya ƙaryata faruwar hakan.

“Duk wanda ya ce, ya yi ganawa da shugaban ƙasa kuma ya amince da shi ko yana goyon bayansa, ƙarya yake yi,” in ji shi.

Tsohon ministan ya ƙara da cewa, ya jinkirta yin murabus daga majalisar ministocin tarayya ne, domin samun ganawa da shugaban ƙasar, inda ya ce; a tattaunawarsu ta gudana a bayan fage, Tinubu ya ƙarfafa masa gwiwar ci gaba da burinsa na tsayawa takarar gwamna.

“Ya ce min, ‘Bayo, lokaci ya yi, ba zan hana ka wannan dogon buri naka ba, ka je ka yi murabus ka fara aiki tuƙuru,” in ji Adelabu.

A cewarsa, “Idan har shugaban ƙasa zai marawa wani baya, to ni ne”.

Bayan rashin samun nasarar da ya yi, Adelabu ya yi watsi da sakamakon, sannan kuma ya yi zargin cewa; an tafka kura-kurai tare da cin zarafi da kuma maguɗi a lokacin zaɓen fid da gwanin.

Sa’idu Ahmed Alkali

Tsohon Ministan Sufuri, ya sauka ne daga muƙaminsa na majalisar ministoci, domin neman tikitin takarar gwamna a Jam’iyyar APC, a Jihar Gombe. Sai dai, matakin ya kasa samar da sakamakon da ake sa ran za a iya samu, inda ya sha kaye a hannun Jamilu Gwamna, wanda ya samu goyon bayan Gwamna Inuwa Yahaya.

Daga baya, Alkali ya kauracewa tsarin, yana mai zargin rashin yin adalci da gaskiya a al’amarin.

Koda-yake, Alkali ya zo na uku ne a zaɓen na fid da gwani, bayan tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami. Yayin da Pantami ya samu ƙuri’u 12,120 a matsayin wanda ya zo na biyu, Alkali ya samu ƙuri’u 11,612 a matsayin wanda ya zo na uku.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin zaɓen, Sanata Abubakar Danladi, ya bayyana cewa; kwamitin ya samu rubutacciyar sanarwar janyewa daga Pantami da Alkali, sai dai ya ce; an miƙa wasiƙun janyewar ne, bayan da aka fara gudanar da zaɓen, inda ya ce; tuni sunayensu ya bayyana a rijistar zaɓe, don haka, sunayensu na nan rubuce a sakamakon zaɓen.

Yusuf Tuggar

Yayin da wasu ministocin suka jinkirta yin murabus ɗinsu, har ma suka kasa bin umarnin na ranar 31 ga Maris, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana matsayinsa a jajibirin cikar wa’adin, yayin da ya miƙa wa shugaban ƙasa takardar murabus ɗinsa a hukumance ta ofishin sakataren gwamnati, a ranar 30 ga watan Maris, 2026.

“A yau, na miƙa takardar murabus ɗina a hukumance a matsayina na Ministan Harkokin Waje na Nijeriya a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, bisa ga umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, da kuma tanade-tanaden dokar zaɓe,” ya rubuta.

Ya bayyana cewa, wannan lokacin ya kawo ƙarshen wani muhimmin babi na hidimarsa, sannan kuma ya gode wa shugaban ƙasar, “saboda amincewa da damar yin aiki a ƙarƙashin ‘Renewed Hope Agenda’, da kuma bayar da gudummawa ga ciyar da manufofin waje na Nijeriya ta hanyar ‘4D Doctrine’”.

Tuggar, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, an zaɓe shi a matsayin wakilin mazaɓar tarayya ta Gamawa a shekarar 2007.

Bayan shekara goma, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya naɗa shi jakadan Nijeriya a ƙasar Jamus. Ya riƙe wannan muƙamin daga 2017 zuwa 2023.

Har ila yau, ya rasa tikitin APC a hannun Mohammed Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi.

A cewar shugaban kwamitin zaɓen gwamnan APC na Bauchi, AIG John Bassey Abang (rtd), Abubakar ya samu ƙuri’u 57,517, inda ya doke Tuggar wanda ya samu ƙuri’u 26,001.

Ministoci
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Shekaru Uku Na Mulkin Tinubu Cike Suke Da Yunwa, Talauci Da Sace Mutane – Atiku

Shekaru Uku Na Mulkin Tinubu Cike Suke Da Yunwa, Talauci Da Sace Mutane - Atiku

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.