ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dubban Magoya Bayan ADC Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC A Sakkwato

by Sadiq
2 months ago

Dubban magoya bayan jam’iyyarADC) sun fice daga jam’iyyar tare da komawa APC a Garin Gorau da ke ƙaramar hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato.

Sauya sheƙar ta faru ne a yankin da Hon. Bashir Usman Gorau, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gada/Goronyo, yake da ƙarfin siyasa.

Ana kallon lamarin a matsayin babban koma baya ga ADC a Yankin Sanatan Sakkwato ta Gabas.

ADVERTISEMENT

An tarbi sabbin mambobin ne a wani taro da shugabannin APC da magoya bayanta suka halarta.

Mataimakin Shugaban APC na Shiyyar Sakkwato ta Gabas, Alhaji Muhammad Musa Sarkin Alaru, ya yi musu maraba tare da tabbatar musu da cewa za su samu dama iri ɗaya da sauran mambobin jam’iyyar.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Da yake jawabi a wajen taron, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan jihar Ahmad Aliyu, Alhaji Hussaini N. Umar Gorau, ya ce yawaitar sauya sheƙar da ake gani a jihar na da nasaba da ayyukan gwamnatin jihar a fannonin gina hanyoyi, bunƙasa karkara, noma da kuma inganta tsaro.

Shi ma Shugaban APC na ƙaramar hukumar Goronyo, Alhaji Sa’idu Muhammad Goronyo, ya buƙaci sabbin mambobin su kasance masu biyayya da haɗin kai domin ƙara ƙarfafa jam’iyyar.

A madadin waɗanda suka sauya sheƙar, Nasiru Mukhtar Gorau, ya ce sun shiga APC ne saboda ayyukan ci gaba da gwamnatin Gwamna Ahmad Aliyu ta gudanar, musamman wajen gina ababen more rayuwa da inganta tsaro.

An kuma karrama Ƙaramin Ministan Ayyuka, Barrista Bello Muhammad Goronyo, da Alhaji Hussaini N. Umar Gorau, da kuma ɗan takarar Sanatan APC na Sakkwato ta Gabas, Alhaji Umar Ajiya, saboda gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban al’umma da kuma bunƙasa jam’iyyar.

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Peter Obi Ɗan Kasuwa Ne Don Haka Bai Dace Ya Zama Shugaban Ƙasa Ba – Oshiomhole

Peter Obi Ɗan Kasuwa Ne Don Haka Bai Dace Ya Zama Shugaban Ƙasa Ba - Oshiomhole

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.