ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fadar Shugaban Kasa Ta Nemi A Sake Shigar Da Koyar Da Aikin Noma A Makarantu

by Abubakar Abba and Sulaiman
7 months ago
Noma

Domin samun nasarar samar da wadataccen abinci a daukacin fadin kasar nan, fadar shugaban kasa, ta bukaci a sake shigar da koyon aikin noma a makarantun kasar nan, musamman domin karfafa samar da abincin da kuma daidaita fannnin tattalin arzikin kasar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayar da wannan shawara a jawabinsa, a wajen babban taron kungiyar manoma ta kasa (AFAN) da aka gudanar a Abuja.

  • Hukumar RUWASSA Ta Kudiri Aniyar Samar Da Ruwa A Fadin Jihar Katsina
  • Jam’iyyar NNPP Tayi Ɓatan Dabo A Tarkadar Zaɓen Cike Gurbi Na Kano

Shettima, wanda babban mai taimaka masa a fannin kiwon lafiya, Uju Rochas-Anwukah ya wakilce shi a wajen taron, ya sanar da cewa; akwai bukatar shigar da koyon aikin noma a makarantun kasar, ba wai kawai a matsayin darasi ba, amma domin a karfafa tare da kwadaitar da dalibai rungumar aikin noma.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa, ya kamata a ware wurin yin noma a makarantun, domin a fara koyar da daliban yadda ake yin noma, musamman domin su dauki fannnian a matsayin hanyar samarwa da kansu kudaden shiga.

“Dole ne a sake shigar da koyon aikin noma a makarantun kasar nan a matsayin wani fanni na gargajiya, ba wai kawai darasin da ilimin aikin noma da aka sanya wa daliban a cikin manhajar karatunsu ba, “in ji Kashim.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

“Ya kamata ‘ya’yanmu su taso da sanin cewa, ana samun kudaden shiga da dama a fannin aikin noma,” a cewar tasa.

Haka zalika, ya yi kira ga shugabanni da kuma sauran cibiyoyin kasar nan da su sanya fannin aikin noma kai tsaye, duba da cewa; fanni ne da ya kamata a runguma a daukacin matakan kasar.

Shettima ya ci gaba da cewa, an jima a kasar nan, ‘yan kasar na daukar fannin aikin noma tamkar wani zaBi na karshe, maimakon su dauke shi a matsayin fanni mai dogon zango.

Koda-yake, Kashim ya sanar da cewa; wannan tunanin, ba wai abu ne marar kyau ba, amma dai fanni ne da ke samar da ayyukan yi kai tsaye da kuma kara daga martaba da darajar kasar.

Shi ma a nasa jawabin a wajen taron, babban ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai murabus ya sanar da cewa, manoman kasar nan na ci gaba da fuskantar kalubale na rashin tsaro.

Sai dai, ya ba su tabbacin cewa; gwamnatin tarayya na yin iya kokarinta, domin lalubo da mafita kan wannan matsalar, musamman domin a kare rayukansu.

Kazalika, ya bukaci manoman da su kai duk wani rahoto na barazanar rashin tsaro ga mahukuntan da suka dace, domin a dauki matakin kare rayukansu da kuma dukiyarsu, duba da cewa; suna bayar da gagarumar gundunmawa wajen noma amfanin gonar da zai wadaci kasar.

Shi kuwa, a nasa jawabin na maraba a wajen taron, shugaban kungiyar na kasa, Dakta Farouk Mudi, ya zayyano wasu daga cikin kalubale na sauyin yanayi da ke shafar fannin na aikin noma da tsadar kayan aikin noma, musamman da kuma rashin tsaro.

Kazalika, ya sanar da cewa; jinkirin saukar ruwan damina da ambaliyar ruwan sama da tsadar farashin takin zamani, na shafar fannin na aikin noman kasar.

Ya yi kira ga mahukuntan kasar, da su samar da ingantattun tsare-tsare da zuba jari, musamman domin a tsamo fannin daga durkushewa.

Ya kara da cewa, a shekarar 2025, an samu jinkirin saukar ruwan damina, wanda ya kai har kusan kwana 21, sai kuma aka samu ambaliyar ruwan sama, inda aka kiyasata cewa, ya lalata kadadar noma sama da 500,000 da aka shuka Shinkafa da kuma Masara.

A cewarsa, shekaru biyu da suka gabata, farashin takin zamani samfarin NPK, an sayar da buhu daya kan Naira 26,000; wanda kuma a yau ake sayar da buhu daya a kan sama da Naira 53,000.

Kazalika, ya sanar da cewa; farashin kayan feshin gona, sun karu zuwa kusan kashi 300 a cikin dari, ya kara da cewa; aikin noma ya yi tsada, sannan kuma dole ne mutane na bukatar abinci.

Bugu da kari, shugaban ya bayyana cewa; akwai kuma bukatar a kara haBaka fannin kiwon kasar, duba da irin kalubalen da fannin ke fuskanta.

“A Nijeriya, akwai dimbin dabbobi, inda ake da akalla Shanu miliyan 21, Tumakai miliyan 43 da Awakai miliyan 82, amma sai dai, kasar na kashe dala biliyan 1.5, kwatankwacin Naira tiriliyan 2.2, wajen shigo da Madarar Shanu cikin kasar,“ a cewarsa.

Sai dai, ya danganta wannan matsalar kan ci gaban da ake samu da afkuwar rikice-rikiece, a yankunan kasar da ake kiwon dabbobi.

Mudi ya ci gaba da cewa, a shekaru goma da suka gabata, saboda irin wadannan rikice-rikicen, musamman a tsakanin manoma da kuma fulani makiyaya, kungiyar ta kuma yi asarar rayuka sama da 10,000 da kadarorin da kudinsu ya kai na sama da Naira biliyan 500. “Mun kuma yi asarar sama da dabbobi miliyan uku da Barayin Shanu suka sace, tare da kuma yin asarar wasu da biyo bayan tafiya da su kiwon da ba a riga an tsara shi yadda ya kamata ba” in ji Mudi.

Kazalika, kungiyar ta kuma ayyana goyon bayanta ga tsaron fannin kiwon dabbobi na kasa wato, NLTP.

“Muna bukatar masu kiwon dabbobi a kasar, su rungumi yin kiwon na zamani, wato wanda ake killace dabbobin a waje daya, domin a kiwata su, ba tare da fuskantar wata barazana ta rashin tsaro ba,” in ji shugaban.

Ya kuma danga samar da tsaro a matsayin babban ginshikin da zai sanya fannin aikin noma ya kara bunkasa a kasar.

Shugaban ya kuma yi nuni da cewa, Nijeriya a duk shekara na kashe sama da dala biliyan goma, kwatankwacin Naira tiriliyan sha biyar, wajen shigo da kayan abinci zuwa cikin kasar nan, musamman Alkama da Siga da kuma Kifi.

Ya bayyana cewa, kamata ya yi a ce; wadannan kudaden na zuwa ne ga manoman kasar nan, inda ya buga misali da cewa; Nijeriya na shigo da tan da dama na Alkama a duk shekara tare da kuma shigo Siga da yawansa ya kai kashi 90.

Noma
Abubakar Abba
+ posts Bio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
Noma
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Binciken CGTN: Karin Haraji Mafi Yawa Ya Haifar Da Gibin Ciniki Mafi Girma Kana Manufar Harajin Trump Ta Wargaje

Binciken CGTN: Karin Haraji Mafi Yawa Ya Haifar Da Gibin Ciniki Mafi Girma Kana Manufar Harajin Trump Ta Wargaje

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.