ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 19, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro:Yadda Sabbin Matakan Gwamnati Ke Shafar Walwalar Al’ummar Jihar Katsina

by El-Zaharadeen Umar and Sulaiman
1 hour ago
Kawayen amarya

Sanarwar da gwamnatin Jihar Katsina ta fitar na cewa ta haramta duk wani ciniki da za a yi na man fetur a cikin jarka ko cikin wane irin abu ne a duk faɗin Jihar ta Katsina ta haramta shi baƙi ɗaya

Hakan dai ya biyo bayan, ƙazancewar matsalar tsaro da ke ci gaba da zaizaye zaman lafiya da aka fara samun a Jihar Katsina, sakamakon sulhu da ƴan barayin daji wanda gwamnatin ta ce al’umma ne suka kulla yarjejeniyar da ƴan bindiga

To, sai dai masana na kallon wannan sabon matakin a matsayin fargar jaji, domin a cewar su, an taba jaraba irin wannan matakin amma bai yi tasiri ba yadda ake so, daga ƙarshe a kan talakawa abin ya ƙare.

ADVERTISEMENT

Yanzu haka ma, suna da imanin cewa, wannan matakin ba zai yi aiki yadda ake so ba, sai dai yana iya sauƙaƙa abubuwan zuwa wani lokaci, amma da wahala kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Yankin Matazu da Musawa ya zama wani tarkon mutuwa, inda nan ne aka yi garkuwa da marigayi manjo janar Rabe Abubakar da matar sa Hajiya Amina da wasu mutane guda bakwai ƴan asalin ƙaramar hukumar Danja.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina

Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya

A hukumance an hana motocin gwamnatin Jihar Katsina bi ta wannan hanya, sannan duk wanda ya bi ta to don kanshi, musamman da Kachalla Muhammadu ya tsananta kai hare-hare da kisa da kuma yin garkuwa da mutane.

Sanya dokar ya biyo bayan wani taron gaggawa a kan harkar tsaro da gwamna Malam Umaru Raɗɗa ya yi da hukumomin tsaro da shuagabanin gargajiya inda a ƙarshen zaman aka bayyana sabbin matakan da suka haɗa da;

Bada umarnin rufe dukkanin wuraren da ake cajin waya da kuma wuraren hada-hadar kuɗi na POS a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.

A cewar gwamnatin Jihar Katsina ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi domin hana karkatar da man fetur zuwa wajen barayin daji, da suka addabi wasu yankuna na Jihar shekara da shekaru.

Kazalika gwamnatin Jihar Katsina ta hana yin acaba baƙi daya a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu domin kawo cikas a zirga-zirgar barayin daji a wannan yanki, amma mashinan da ba na acaba ba an amince da su cigaba da hada-hadar su.

A cewar gwamna Raɗɗa kare rayuka da dukiyoyi al’umma shi ne abinda gwamnatin sa ta sanya gaba a wannan lokaci da suke aiki tare da hukumomin tsaro wajen ganin an samu zaman lafiya a Jihar Katsina

Haka kuma ya yi kira ga al’umma da su ba da goyon baya domin samun nasarar da ake buƙata game da wannan matsala da ta taso, sai dai gwamnatin ta ce ba zata saurarawa duk wanda ya karya wannan dokar ba.

Shima a baƙin sa masanin tsaro, Dakta Yahuza Getso, ya bayyana cewa idan an ɗauki wannan mataki a ƙananan hukumomi, to za a yi waɗanda suke da makwabtaka da inda aka hana hawan babura da cajin waya da sayar da man fetur a jarkoki?

Dakta Yahuza Getso ya ce ɗaukar irin wannan mataki abin a yaba ne, abin ƙ arfafa gwiwa ne, musamman a kan sha’anin tsaro wanda ya addabi yankin Matazu da Musawa.

Sai dai ya yi tambaya, inda ya ce idan aka hana waɗannan abubuwa a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu wane makulli za a yi amfani da shi wajen rufe ƙananan hukumomi kamar su Charanci da Kankia da Dutsinma da Malumfashi da Ƙankara sauransu?

Ya ƙara da cewa, ya ya za a yi da masu gidajen man fetur da ƴan bindiga ke waya da su, inda ya ce akwai bara gurbi a cikin masu sayar man fetur ɗin a wadannan wurare.

Haka kuma ya yi fatan cewa Allah ya sa dalili wannan al’amari na marigayi manjo janar Rabe Abubakar ya zama wata silla ga hukumomi wajen ɗaukar mataki da yin abin da ya kamata a sha’anin tsaro.

Sai dai a cewar shugaban gamayyar ƙungiyoyin fararan hula na Jihar Katsina Abdurahman Abdullahi ya ce waɗannan dokoki ba sabbin abu bane, inda ya ƙara da cewa ƴan bindiga yanzu sun yi wayon da ba sai sun kai wayoyinsu caji a cikin gari ba

Ya ƙara da cewa, yanzu suna amfani da janareto da kuma na’urar mai amfani da hasken rana wajen samarwa da kansu mafita game da sha’anin canjin wayar su da sauran buƙatu.

A cewar sa, duk wanda aka kamawa ɗan uwa, idan an hana amfani da POS a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu, mutane ba za su ga nisan zuwa Jihar Kano ba domin samun kuɗaɗen da za su kai a saki ƴan uwan su ba.

Abdurahman Abdullahi ya bayyana cewa idan aka hana hawan babura mutanen gari aka hana ba ƴan bindiga ba, domin shi ɗan bindiga daman mai laifi ne a wajen gwamnati.

Ya ƙara da cewa irin hanya da matakin da sojojin Nijeriya suka bi wajen kubutar da matar marigayi manjo janar Rabe Abubakar ya kamata a bi domin kawo ƙarshen wannan matsala

Ko a gwamnatin baya da aka yi wannan dokar talakawa ne suka zama sha wuya, domin dai barayin daji babu abinda suka fasa yi na ayyukan ta’adanci da sauran manyan laifuka.

Yanzu dai abin jira a gani shine irin tasirin da wannan mataki zai yi wajen kawo ƙarshen matsala a yankunan da ke fama da wannan bala’in shekara da shekaru.

Tsaro
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Matsalar Tsaro: Manoma Sun Koma Gonakinsu A Katsina – Dikko Radda
Tsaro
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina
  • Sulaiman
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Sulaiman
    Majalisar Wakilai Ta Fara Yunƙurin Gyaran Dokokin Soja
  • Sulaiman
    Shekarar Musulunci: Tinubu Ya Yi Kira Da A Nuna Kyakkyawan Kishin Ƙasa

MASU ALAKA

Tinubu
Labarai

Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina

June 19, 2026
Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya
Labarai

Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya

June 19, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Fara Yunƙurin Gyaran Dokokin Soja

June 19, 2026
Next Post
Tinubu

Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma'aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina

June 19, 2026
Kawayen amarya

Matsalar Tsaro:Yadda Sabbin Matakan Gwamnati Ke Shafar Walwalar Al’ummar Jihar Katsina

June 19, 2026
Manzon Allah

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya

Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya

June 19, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Majalisar Wakilai Ta Fara Yunƙurin Gyaran Dokokin Soja

June 19, 2026
INEC Ta Kammala Shirye-shiryen Zaɓen Gwamnan Ekiti Da Zaɓukan Cike Gurbi A Jihohi 6

INEC Ta Kammala Shirye-shiryen Zaɓen Gwamnan Ekiti Da Zaɓukan Cike Gurbi A Jihohi 6

June 19, 2026
Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira

Shekarar Musulunci: Tinubu Ya Yi Kira Da A Nuna Kyakkyawan Kishin Ƙasa

June 19, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Siyasar 2027: Yadda Ƴan Adawa Ke Ƙara Shiga Tsaka-mai-wuya

June 19, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Cimma Yarjejeniya Tsakanin Amurka Da Iran Ta Fallasa Koma Bayan Tasirin Amurka A Harkokin Duniya

Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Cimma Yarjejeniya Tsakanin Amurka Da Iran Ta Fallasa Koma Bayan Tasirin Amurka A Harkokin Duniya

June 18, 2026
Kotu Ta Umarci DSS Ta Mutunta Umarninta Kan Shari’ar Filin Firo Na Bauchi

Kotu Ta Umarci DSS Ta Mutunta Umarninta Kan Shari’ar Filin Firo Na Bauchi

June 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.