ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gidan Tarihi: Gadar Da Ke Hada Wayewar Sin Da Afirka

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Tarihi

Ranar 18 ga watan Mayun kowace shekara ita ce “Ranar Gidan Tarihi ta Duniya”. Taken ranar ta bana shi ne “Gidan Tarihi: Gadar Da ke Hada Duniya”, wanda ke jaddada cewa gidan tarihi ba kawai ma’adanar abubuwan da suka gabata ba ne, har ma “gada” ce da ke hada al’adu daban-daban da kuma inganta cudanya tsakanin al’ummomi. Idan muka kalli nahiyar Afirka, za mu ga cewa gidajen tarihi da ke wasu kasashen nahiyar, ciki har da Morroco, Kenya, da Senegal, tamkar “gada” ce da ke bayyana ma’anar cudanyar al’ummu da musayar al’adu a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A cikin Gidan Tarihi na Ibn Battuta da ke birnin Tangiers da ke arewacin kasar Morroco, akwai samfurin jirgin ruwa na zamanin daular Yuan ta Sin da kwafin littafin “Tafiya ta Ibn Battuta”, wadanda ke nuna abubuwan da dan tafiya na kasar a karni na 14 ya gani a kasar Sin mai nisa, wato “Jirgin ruwan Sin kamar fada ce a kan teku”, “Tashar jiragen ruwa ta birnin Quanzhou cike da dubban jiragen ruwa, kasuwancin birnin Guangzhou ba ya hutawa dare da rana, kuma Hangzhou kamar lambun duniya”. Mai bayanin gidan tarihin ya ce yawancin yaran Morroco sun fara sanin Sin ne daga wajen Ibn Battuta. Har wa yau, a gidan tarihi na kasa na Kenya, an ajiye fasassun tangaran da yawa da suka fito daga kasar Sin. Alal hakika, a wuraren Lamu, Malindi na Kenya da Kilwa na Tanzaniya, masu binciken kayan tarihi sun gano kayayyakin fadi-ka-mutu da yawa da suka fito daga kasar Sin.

Wadannan “alamomin Sin” da suka warwatsu a kasashen Afirka, hakika sun shaida “musayar wayewa” tsakanin Sin da Afirka, wadanda suke bayyana mana cewa, huldar Sin da Afirka ba wai ta fara ne da hadin gwiwar tattalin arziki na zamani ba, tana samun tushe ne daga tsarin ciniki ta tekun Indiya da aka yi tun shekaru daruruwa da suka wuce. Dangane da dangantakar Sin da Afirka, gidan tarihi ya zama tamkar “madubi”, wanda ke nuna abubuwan da suka faru a baya da yiwuwar nan gaba.

ADVERTISEMENT

Gidan tarihi shi ne mai rikon gaskiyar tarihi. Lokacin da muka kalli kwano mai kyalli na zamanin daular Ming a gidan tarihin kayayyakin tangaran na birnin Alkahira na kasar Masar, abin da muke gani ba fasahar hada kayayyakin fadi-ka-mutu kawai ba ne, har ma da yadda aka yi musaya da wanzar da lumana a tsakanin Sin da Afirka a shekaru 600 da suka wuce. Kamar yadda Farfesa Farouk, masanin tarihi na Jami’ar Alexandria ta kasar Masar ya ce, ayarin jiragen ruwan babban mai tafiya a kan teku na Sin Zheng He na zamanin daular Ming ya bar wa Afirka “tangaran da siliki da shayi da kuma musayar al’adu”. A ganinsa, babban bambanci tsakanin Zheng He da ayarin jiragen ruwan Turawan mulkin mallaka na baya shi ne manufar tafiyarsu. “Zheng He bai zo da mulkin mallaka ba. Wannan tafiyar wanzar da lumana har yanzu yana da tasiri a kasashen Afirka da yawa.” Wadannan kayan tarihi sun kuma karyata maganar wai “Sin tana kafa sabon salon mulkin mallaka a Afirka”.

Gidan tarihi shi ne kuma mai sa kaimin musayar wayewar kai. Wadannan kayayyakin tangaran na kasar Sin da aka gano a gabar tekun gabashin Afirka, daga baya sun hade cikin al’adun gine-ginen Afirka. A wasu tsofaffin gidaje na garin Lamu da ke Kenya, har yanzu ana iya ganin farantin tangaran na kasar Sin da aka saka a cikin bango. Ba su kasance kayan abinci kawai ba, sun zama wani bangare na fasahar gine-ginen Afirka daga baya. Wannan tasiri a hankali shi ne babbar darajar “musayar al’adu”.Gidan tarihi har wa yau shi ne tushen hadin gwiwa a nan gaba.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Gidan tarihin wayewar bakaken fata na Senegal wanda gwamnatin kasar Sin ta taimaka wajen gina shi, yanzu haka ba wai alamar al’adu ce ta yammacin Afirka kadai ba, har ma da sabon dandalin musayar al’adu a tsakanin Sin da Afirka. Kamar yadda daraktan gidan tarihin Hamady Bocoum ya ce: “Musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka ba ta fara daga yau ba.” A zamanin da ake samun bunkasuwar sassa daban daban, gidajen tarihi za su taimakawa matasan Sin da Afirka su fahimci zurfin ma’anar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”.

Lokacin da muke kallon wadannan fasassun tangaran daga kasar Sin a gidan tarihi na birnin Nairobi, ko karanta littafin tafiya na Ibn Battuta a cikin gidan tarihinsa, a hakika muna shiga cikin cudanyar al’adu da ta ketare lokaci da sarari. Wannan, watakila ita ce kyauta mafi daraja da gidan tarihi ke ba mu: ganin tarihi, fahimtar abin da ya gabata, don mu kara dagewa wajen tafiya tare zuwa nan gaba.

Tarihi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Tarihi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman Hukuncin Shekaru 75 A Gidan Yari

EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman Da Ya Tsere

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.