ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gudunmawar Shehu Ibrahim Inyass (RTA) Ga Musulunci A Wayewar Zamani (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
5 months ago
Inyass

… ci gaba daga makon da ya gabata.

Shehu Tijani (RA) ya fada cewa, Faila zata zo, kuma duk an tabbatar, Shehu Ibrahim Inyass Kaulakh yake nufi.

Har ila yau, Shehu Usman dan Fodio (RA) a cikin wakokin sa na fulatanci, a littafin sa na Kanzul Auladi Wazzarari, har sunan Shehu Ibrahim Inyass Kaulakh ya fada, da cewarsa, “wa raida Ibrahimu Sharafuddeen,” ma’ana  “bayan mu kuma, akwai Ibrahim Sharafuddeen wanda addini zai daukaka a zamanin sa”, kuma shi ne “Usamuddeen”. Mun gode wa Allah, jikokin sa manya tun daga sarkin musulmi Abubakar na III wadanda suka yi zamani da shehu Ibrahim Inyass Kaulakh har ya zuwa ‘ya’yansa na yanzu, duk sun tabbatar da cewa wannan abu da kakansu ya fada, ilimin shehu Ibrahim Kaulakh yake nufi.

ADVERTISEMENT
  • Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji
  • Akpabio: Ba A Canza Komai A Cikin Sabbin Dokokin Haraji Ba 

To wannan haka waliyan, haka kasar Mali, haka shehu Umar Karaki – wali ne a Ghana da akayi, akwai gidan TB da aka sanya mata suna Umar Karaki TB, sabida kasaitarsa, shi ma ya fadi zuwan Shehu Ibrahim Kaulakh.

Mun gode wa Allah, wannan Shehun namu, Sahibul Faidati, yazo mana da wayewa da komai. Shi ya fara aiki da kayan turawan mulkin mallaka a addinin nan bayan tafiyar su. Wani abun mamaki, Shehu Ibrahim Kaulakh, akan yasa ayi karatu a cikin rediyo, sai da aka ce masa Kafuri a kasar nan tamu Nijeriya, sabida yace dole a saka karatun Alkur’ani a gidan rediyo, a lokacin da aka kafa sabon gidan rediyo na Jaji da ke Kaduna.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

Shehu Ibrahim ya fara wa’azi a cikin rediyo a Gambia, inda ya ke cewa a Diwaninsa, “wa lam tura mau’izatun tura’u, min kablihi yanshuruhul mizya’u – ba a taba ganin wa’azi, rediyo tana yadawa ba sai zamanin shehu Ibrahim”.

Wadansu suka ce, “mun gode wa Allah, Allah ya bamu wayayyen malami wanda ya nuna mana lallai mu yi amfani da kayan zamani”, wadansu kuma suka ce, “Riya kenan, a rasa inda za a je a yi wa’azin sai a gidan rediyo”, yanzu wanda ya ce riya ne, da zai zo wannan lokacin a ina ake wa’azin?

Shehu, shi ya nuna mana cewa, in kana da karatu, kuma baka fahimci zamaninka ba, rikici ya faru!

Shehu Ibrahim (RA), shi ya dauke Malamanmu daga reshe (furu’a) da ake cewa su tsaya a kai kawai. Mu malikawa ne, kuma a malikawanma sai malikancin dan Kasim wanda shi ne shehun mu na Afirka, shi ya kawo mana karatun Imam Malik zuwa Misra, don haka, za ka ga littafanmu na malikanci, na Misra ne, Iziyya da su Ishimawi duka ruwayoyi ne na Misra, sabida dan Kasim nan ya dawo. Almajiran Imam Malik suna da yawa, don haka sun dauko karatu kala-kala daga wurinsa, amma muce ba ruwan mu da karatun sai na dan Kasim dinnan, har a cikin mazhabar ma mun takura kanmu a wani waje guda, sannan Imam Malik ba shi kadai ne shugaba a cikin masu mazhaba ba: akwai Shafi’i, da Ahmadu bin Hambal, kuma dukkan su ahlus sunna ne, muce ba ruwan mu da duk karatun su ko da ga hujja tabbatacciya, muce sai Malikanci, to Shehu Ibrahim Kaulakh, shi ya tashi, yace, a’a, mu rika komawa center ta farko Alkur’ani, sannan mabiyinta, ingantacciyar sunnar manzon Allah SAW wacce bata yi karo da Kur’anin nan ba, sabida ba karo tsakanin Allah da manzon Allah SAW, sannan maganganun malamai da ba su yi karo da maganar Allah da manzon Allah ba. “A nasbu kilafun baina daha wa gairihi, ya rahu labibun gairi aini ama’i, – yanzu kace manzon Allah SAW yace kaza, amman kuma malam wane yace kaza, sai nace baka da hankali ne? Za ka hada Annabi SAW da maganar wani Malami, waye Allah ya aiko ma? To, Shehu Ibrahim Kaulakh, shi ya hori shehunnan mu da bin wannan ka’ida, sun sha wuya, musamman a wurin Sallar Kablu.

Mun gode wa Allah, ilimin tarihi na hakeken kasa (archeology) ya fahimtar da kowa ma yanzun, an tono hotuna da irin fasaha ta mutanen da, da annabawansu da Alkur’ani ya bamu labari wajen shekara dubu dari uku kafin haihuwar Annabi Isa (AS). an gano yadda suke Ibada da yadda suka sa hannu akan wani abun mamaki, duk Kur’ani ya gaya mana wannan abun.

Ba don Allah ne ya fada wannan ba, mutane ba za su yarda ba. To mun gode wa Allah.

Ba don kuri ba, wayewa da fahimtar addini cikin sauki, babu kamar almajiran Shehu Ibrahim Inyass Kaulakh. to wanda Allah ya basu wannan Shehi wayayye, dole su godewa Allah. Duk ‘yan adam suna murnar haihuwar wani da ya kawo musu cigaba a addini ko a rayuwa ko a siyasa ko a wayewa.

Mun gode Allah, da ya nuna mana wannan shekara mai alkhairai da yawa. Shekarar da Annabi SAW ya cika shekara 1,500 da haihuwa, duk al’umma suke murna akan haka da kuma zagayowar Maulidin maulanmu Sheikh Ibrahim Kaulakh a watan Rajab, wanda za a yi babban taro a babban gari, garin ilimi, garin sufanci, garin darikar Tijjaniyya, kuma garin Faila na manyan almajiran Sheikh Ibrahim Kaulakha.

Makasudin wannan Maulidi, shi ne godiyan Allah da Allah ya bamu Sheikh Ibrahim Kaulaha, ma’abocin failar Sheikh Tijjani Abul Abbasi wanda alkhairinsa ya game duk musulmi, ba sai sufaye kadai ba, ya game duk sufaye ba sai mu tijjanawa ba, duk masu addini, sun amfanu da albarkar Sheikh Ibrahim Inyass (RA). Sabida ta hanyarsa sufanci ya shiga ofisoshi, ya shiga hatta Saudiyya lokacin da tana kan tashan wahabiyanci.

Amma Allah tabaraka wa ta’ala ya sahhale musu Sheikh Ibrahim, Allah ya sahalewa Sheikh Ibrahim su, sarakunan nasu da komai dole sai da suka yarda da sufanci hatta muftin Saudiyya na wannan lokaci, Ali Sheikh, akwai hotonsa da Shehu yana nan ba daya ba ba biyu ba. To wannan muftin na Saudiyya, wani zance ya shiga tsakaninsa da Shehu Ibrahim Inyass, yake cewa Shehu, “mun gode Allah da muka ganka, yanzu mu ba sai mun sha wahalar zuwa Afrika don fitar da su akan kafurcin da suke yi na sufanci ba, kai dai kowa ya ganka, kowa ya jika ya san malami ne. To yanzu duk abin da kake so, ka bayyana, muna so mu dau nauyin ka da komai, kaje ka fitar da Afrika daga kafurcin da suke yi na darikokin sufaye balle Darikar Tijjaniyya”.

Daga nan, sai Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya ce masa, me cece Darikar Tijjaniyya? Sai yace wallahi ban santa ba amma dai na san kafurci ce. Sai yace waye Shehu Tijjani? Me Darikar? Sai yace ban san shi ba amma dai na san batacce ne wanda ya kafa bata. Sai Shehu Ibrahim Inyass yace masa, waye za a tambaya? Wanda ya sani ko wanda bai sani ba? Mufti ya ce, a Ilimance, wanda ya sani shi za a tambaya, sai Shehu (RA) ya ce, to ka ganni nan, na san Darikar Tijjaniyya da kyau, akanta aka haife ni, akanta nake, Mahaifina yana daga cikin mukaddamai manya a cikinta a Senegal kuma a Afrika duk gabaki daya. Sannan na san waye Shehu Tijjani, sharifi ne tun yana dan shekara bakwai ya haddace Kur’ani ya yi kaza ya yi kaza kuma Darikar Tijjaniyya: istigfari ce, da salatin Annabi, da kaza, da kaza.

Shehu ya fadi wannan hikayar ba a wuri daya ba, ba wuri biyu ba, har a hudubar Murtaniya.

Shehu ya ci gaba da yi wa Mufti tambayoyi, har zuwa inda ya ce masa, yanzu musulmi zai wa dan uwansa musulmi huduba cewa, ya bar istigfari ya bar salatin Annabi, yace a’a ba zai yiwu haka ba, sai Shehu yace wannan itace Darikar Tijjaniyya. Sai yace to ai mu ba haka aka gaya mana ba. To yi min littafi, ya gaya Sheikh Ibrahim, imin littafi ka gaya min me cece Darikar Tijjaniyya kuma waye Shehu Tijjani? Don na san ta. Sai Shehu yayi littafin Albayanu wattabiyin, fit Tijjaniyati wat Tijjaniyyina. Wannan littafi muftin Saudiyya ne yasa Shehu Ibrahim ya yi masa. Shehu Ibrahim ya yi wannan irin littafi a ilimance, a wayewa kuma a sufance.

To bayan addu’a Allah ya kawo mana sauran baki mahalarta wannan Maulidi lafiya, Allah yasa a yi taro lafiya kowa ya koma lafiya, Allah ya bai wa kasarmu lafiya, musamman arewacin Nijeriya, Allah ya bamu lafiya da bunkasar arziki, albarkar manzon Allah SAW.

Muna rokon ubangiji ya yi riko da hannun shuwagabannin mu a cikin abin da kasa za ta cigaba, da ‘yan kasa za su cigaba.

Muna kira da duk ‘yan uwanmu musulmi, musamman mabiyan Shehu Ibrahim da muka taru, mu rika koyi da halin Shehu Ibrahim Inyass Kaulakh ta hanyar wayewarsa, kwarewarsa cikin addini, rahamarsa, tausayin (RA) da karantarwarsa da fahimtar sa da zamanin sa.

Inyass
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Next Post
Shehu Sani Ya Yi Allah-Wadai Da Buƙatar Shugaban INEC Ya Sauka

Shehu Sani Ya Yi Allah-Wadai Da Buƙatar Shugaban INEC Ya Sauka

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.