ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Abba Yana Naɗa Garo A Mataimakin Gwamna Shari’arsa Ta Zargin ₦57.4bn Za Ta Dakata

by Muhammad
5 months ago
Garo

Masana harkokin shari’a sun bayyana damuwa cewa naɗa Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano na iya jinkirta shari’ar zargin almundahana ta naira biliyan 57.4 da ake yi masa, sakamakon kariyar doka da kundin tsarin mulki ya tanada ga masu riƙe da wasu manyan mukamai.

Bayan murabus ɗin tsohon mataimakin gwamna, Abdulsalam Gwarzo, sunan Garo ya riƙa yawo a matsayin wanda ake iya maye gurbinsa da shi. A halin yanzu, yana fuskantar shari’a tare da tsohon gwamnan Jihar Kano, Umar Ganduje, da wasu mutum biyu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati har naira biliyan 57.4.

  • Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo
  • 2027: Ɗan Buhari Ya Bayyana Sha’awar Tsayawa Takarar Majalisar Wakilai

Shari’ar, wadda Gwamnatin Jihar Kano ta shigar, ana kallonta a matsayin ɗaya daga cikin manyan shari’o’in cin hanci da rashawa mafi ɗaukar hankali a jihar a ‘yan shekarun nan.

ADVERTISEMENT

Da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Talata, wani babban lauya, Usman Bello, ya ce idan har Garo ya karɓi mukamin Mataimakin Gwamna, zai samu kariya a ƙarƙashin Sashe na 308 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, wanda ke ba wasu masu muƙaman gwamnati kariya daga gurfanar da su a gaban kotu yayin da suke kan mulki.

Ya ce, “Lokacin da ake maganar naɗin ya na da matuƙar muhimmanci, musamman idan aka yi la’akari da girman zarge-zargen da kuma matakin da shari’ar ta kai.”

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Haka kuma, Bello Abubakar Ginsau na ƙungiyar Kano Governance and Accountability Forum ya jaddada buƙatar yin taka-tsantsan.

Ya ce, “Ya dace a yi nazari sosai kan lokacin da ake yin irin waɗannan naɗe-naɗe a yayin da ake ci gaba da shari’a. Dole ne a tabbatar da cewa riƙon amana da gaskiya sun kasance ginshiƙai a duk wani mataki da za a ɗauka.”

Garo
Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Garo
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Jagoranci Wata Tawaga Domin Ziyartar Babban Yankin Sin

Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Jagoranci Wata Tawaga Domin Ziyartar Babban Yankin Sin

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.