ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Uba Sani Ya Tsawaita Shirin Sufurin Motocin CNG Kyauta Ga Al’ummar Jihar Kaduna

by Shehu Yahaya and Sulaiman
9 months ago
Uba sani

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da tsawaita Shirin Sufurin Motocin CNG kyauta ba tare da kakkautawa ba, sakamakon tasirin da shirin ya yi wa mazauna jihar na jigilarsu daga wurare dadan-daban.

A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kaduna Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce Gwamna Uba Sani ya amince da tsawaita shirin ne bayan duba rahoton na da ya samu game da yadda shirin ya gudana daga watan yuni zuwa Nuwamba 2025.

  • An Yi Barazanar Kashe Ni Bayan Komawa Manchester United – Rooney
  • Me Ya Sa Ya Kamata Kasashen Afirka Su Bunkasa Tattalin Arziki Tare Da Kare Muhalli?

A cewar sanarwar, manyan motocin CNG guda 100 da tashoshi 200 da ake amfani da su a fadin jihar sun ɗauki fasinjoji sama da miliyan 1.4 cikin watanni biyar, tare da adana wa al’ummar jihar Kaduna kimanin Naira biliyan 1.39 a kudin sufuri.

ADVERTISEMENT

“Wadannan ba lissafi kawai ba ne, Sun zama kudin makaranta da aka biya, abincin da ya shiga kima da kananan kasuwanni da suka ci gaba da aiki, da dubban ‘yan jihar da ke zirga-zirga ba tare da nauyin kudin mota ba.”

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ya kara da cewa shirin yana bawa sama da mutane 18,000 hidima a kullum, lamarin da ya tabbatar da mahimmancinsa a matsayin daya daga cikin fitattun shirye-shiryen tallafin jin kai a jihar.

Maiyaki ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani, wanda ya tausaya matuka bayan jin shaidun fasinjoji a lokacin ziyarce-ziyarcen sa, ya umarci ci gaba da gudanar da shirin ba tare da saka wa’adin karewa ba.

“Jin dadin jama’armu da murmushinsu, da godiyar da suke yi suna tuna mana cewa shugabanci dole ne ya rage wa talaka nauyi,” in ji Gwamnan.

“Saboda haka na amince da ci gaba da gudanar da Shirin Sufurin Jama’a na CNG kyauta har sai wani lokaci .”

Kwamishinan ya kara tabbatar da cewa gwamnatin ta jajirce wajen fadada sufuri mai aminci, da rahasu kuma mai kare muhalli ga dukkan mazauna jihar, a matsayin wani bangare na kudurin bunkasa jarin dan adam.

Uba sani
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
Uba sani
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Kakakin Rasha: Kisan Kiyashin Nanjing Ya Nuna Zaluncin Ra’ayin Nuna Karfin Soja Na Japan

Kakakin Rasha: Kisan Kiyashin Nanjing Ya Nuna Zaluncin Ra’ayin Nuna Karfin Soja Na Japan

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.