ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Kano Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi Ga Jami’o’in Jihar Biyu

by Abubakar Sulaiman
4 weeks ago

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin albashi ga dukkanin ma’aikata masu koyarwa da waɗanda ba sa koyarwa a jami’o’in jihar guda biyu; wato Aliko Dangote University of Science and Technology da ke garin Wudil, da kuma Northwest University da ke birnin Kano, a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2026.

Wannan muhimmiyar sanarwa ta fito ne ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, inda ya bayyana cewa an yi amfani da sabon tsarin ƙarin albashin ne daidai da wanda Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar a jami’o’inta da ke faɗin Nijeriya domin inganta jin daɗin ma’aikata.

Kamar yadda cikakken bayanin ya tabbatar, Gwamna Yusuf ya ɗauki wannan mataki ne biyo bayan karɓar rahoton wani kwamiti na musamman da Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta kafa, domin yin nazari a kan buƙatar jami’o’in guda biyu na daidaita tsarinsu da sabon ƙarin albashin ƙasa.

ADVERTISEMENT

A ƙarƙashin wannan tsari da aka amince da shi, za a fara lissafin sabon albashin ne tun daga watan Janairun 2026, yayin da za a fara raba kuɗaɗen a hukumance ga ma’aikatan a watan Satumbar 2026. Tsarin zai lashe jimillar naira miliyan 391.8 a kowane wata, wanda ya kama kusan naira biliyan 4.7 a duk shekara ga jami’o’in biyu.

Bugu da ƙari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudurinsa na tabbatar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikata, inda ya kuma bayar da amincewa wajen kafa kwamitocin ziyara (Visitation Panels) a makarantun biyu da sauran manyan makarantun jihar Kano, domin ƙarfafa bin ƙa’ida, da kyakkyawan shugabanci da kiyaye asusun makarantun.

LABARAI MASU NASABA

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Next Post
Girgizar Ƙasa Mai Ƙarfi Ta Yi Ajalin Mutane 111 A Colombia

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.