Ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya, NLC da TUC, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N500,000 ga ma’aikatan ƙasar. Ƙungiyoyin sun ce albashin N70,000 da ake biya yanzu ya rasa ƙima sakamakon hauhawar farashi da tsadar rayuwa.
An gabatar da buƙatar ne a taron “Nigeria Rights of Workers Summit” da aka gudanar a Birnin Kebbi. Mataimakin Shugaban NLC na Ƙasa kuma Shugaban NUT, Comrade Audu Titus Amba, wanda ya wakilci Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero, ya ce wa’adin yarjejeniyar mafi ƙarancin albashin N70,000 ya ƙare a watan Yuli.
Amba ya ce ya zama dole a fara sabuwar tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya, tare da tabbatar da cewa sabon albashin bai gaza N500,000 ba. Ya ƙara da cewa duk wani albashi da bai kai wannan adadi ba ba zai yi daidai da halin ƙuncin tattalin arziƙi da tsadar kayayyaki da ma’aikata ke fuskanta ba.
Ya jaddada cewa ƙungiyoyin ƙwadago ba sa neman faɗa da gwamnati, sai dai tattaunawa mai amfani domin daidaita albashi da halin tattalin arziƙi. Kusan wakilai 1,000 daga sassan ƙasar ne suka halarci taron domin tattauna matsalolin ma’aikata da hanyoyin inganta jin daɗinsu.
A nasa jawabin, Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya ce jihar ce ta fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin N75,000. Ya kuma yi alƙawarin gabatar da buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago ga Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya domin tattaunawa, yayin da shugabannin ƙwadago suka buƙaci Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin tattaunawa cikin gaggawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.














