ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Sayar Wa Da Manoma Takin Zamani Kan Farashi Mai Rahusa

by Abubakar Abba
4 months ago
Taki

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da cewa, a kakar noman bana ta 2026, za ta sayar wa da manoman jihar takin zamani a kan farashin naira 25,000 duk buhu guda.

Sayen takin dai a jihar, ya kasance wani babban kalubale da manoman jihar suke fuskanta, inda kuma a gefe daya, jihar ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro.

A kakar daminar 2026, manoman sun sayi takin a kan duk buhu daya naira 45,000, saboda samun inganta lamarin tsaro a jihar, wanda hakan ya sa manoman jihar suka yi noma mai yawa.

ADVERTISEMENT

Usman Abdul, wani manomi a Karamar Hukumar Kankia a jihar, ya danganta matakin da gwamnatin jihar ta dauka, na sayar wa da manoman jihar buhun takin zamani kan farashin naira 25,000, a matsayin samar da masu sauki ga sana’ar tasu.

Sai dai, ya nuna damuwarsa, a kan sake dawowar ayyukan ‘yan bidiga a wasu sassan jihar, wanda ya ce; hakan zai iya dawo da hannun agogo baya.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Kwamishinan ma’aiktar aikin noma na jihar, Aliyu Lawal Shargalle, ya bayyana cewa; majalisar zartwarwa ta jihar ce ta amince da sayo tan 20,000 na takin zamanin, wanda ya kai daidai da buhu 400,000.

Ya ce, takin ya hada da samfurin NPK 20:10:10, NPK 15:15:15, da urea, domin yin noman na 2026, inda ya kara da cewa; gwamnatin za ta sayar da takin ga manoman a kan farashi mai sauki.

“Gwamnatin ta samar da wannan daukin ne, domin tabbatar da ganin an samar da ingantaccen takin, kuma a kan lokaci tare da sayar musu da shi kan farashi mai sauki,” in ji kwamishinan.

Ya kara da cewa, hakan zai kuma sanya a kara samar da wadataccen abinci a jihar tare da kuma ci gaba da kokarin gwamnatin na kara inganta rayuwar manoman jihar.

Shi kuwa, shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar, wato AFAN, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ya bayyana cewa; kungiyar tare da hadaka da gwamnatin jihar, ta samar da tsarin da za a yi amfani da shi wajen rabar da takin, musamman domin tabbatar da an yi gaskiya da kuma bin ka’idar da ta dace.

 A cewarsa, za a rabar takin a mazabun da ke jihar, domin tabbatar da cewa; takin ya kai ga ainahin manoma na gaskiya.

Kazalika, Gwajo-gwajo ya sanar da cewa; kungiyar na ci gaba da nuna damuwarta, kan ci gaba da afkuwar hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

Koda-yake, ya kara da cewa; gwamnatin jihar ta bai wa manoma tabbacin cewa; za ta yi dukkan mai yiwuwa, domin kara bunkasa fannin tsaron jihar, musamman domin manoman su samu damar komawa su ci gaba da noma a gonakinsu.

Ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta kuma sayo ingantaccen Irin noma da za ta raba wa manoman jihar.

Ya ce, hakan na daya daga cikin kokarin da gwamnatin ke ci gaba da yi, na kara habaka fannin aikin noma na jihar da kuma kara samar da wadataccen abinci a jihar.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar, ta dauki matakan da suka kamata, domin ganin cewa; manoman sun yi amfani da daukin na takin yadda ya dace da manoman jihar, sun gamsu da matakan da gwamnatin jihar ke ci gaba da dauka.

Taki
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
An Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Wutar Lantarki Zuwa 400MW Da Gwamnatin Legas

An Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Wutar Lantarki Zuwa 400MW Da Gwamnatin Legas

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.