A wani yanayi da ba a saba gani ba na sauya shekar ‘yan siyasa zuwa jam’iyyu, jim kadan bayan rantsar da Majalisar Dokoki ta 10 a shekarar 2023, yanzu lamarin ya rikide zuwa wani sabon tsari na sauya sheka mafi girma a siyasa a tarihin dimokuradiyyar Nijeriya.
Daga Majalisar Dattawa zuwa Majalisar Wakilai, sama da ‘yan majalisa 120 na tarayya sun bar jam’iyyun siyasar da suka tsaya takara a karkashinsu suka ci zabe, lamarin da ya haifar da damuwa kan rashin aminci ga jam’iyya, rushewar akidar siyasa, da kuma raunana tsarin jam’iyyu da yawa a dimokuradiyyar Nijeriya.
Yayin da ‘yan majalisa da dama suka koma jam’iyyar APC mai mulki, wasu kuma sun sauya sheka tsakanin jam’iyyun adawa da suka hada da PDP, LP, NNPP, ADC, APP, AP da kuma sabuwar jam’iyyar (NDC).
Sai dai a makon da ya gabata, wani sabon salon sauya sheka ya sake girgiza Majalisar Dokoki ta Kasa. Duk da cewa yawancin ‘yan majalisar sun riga sun fice daga jam’iyyun da suka tsaya takara a karkashinsu suka lashe zabe, sun sake komawa sabuwar jam’iyyar NDC.
Lamarin ya biyo bayan sauya shekar tsoffin ‘yan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar ADC zuwa NDC.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar kuma sun yi sauya shekarsu ta farko zuwa sababbin jam’iyyun siyasa, lamarin da ya sanya Majalisar Dokoki ta 10 ta zama daya daga cikin majalisun da aka fi samun sauyin siyasa a tarihin dimokuradiyyar Nijeriya.
Yawaitar sauya shekar ta girgiza tsarin siyasar kasar, inda masu suka da dama ke cewa wannan al’amari na nuna yadda siyasar tsira da neman mafita ta fi rinjaye a Nijeriya.
Majalisar Wakilai
A Majalisar Wakilai, ‘yan majalisar da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai fama da rikice-rikice zuwa APC mai mulki sun hada da Oluwole Oke (Osun), Hussein Jallo (Kaduna), Adamu Tanko (Niger), Bictor Nwokolo (Delta), Julius Pondi (Delta), Thomas Ereyitomi (Delta), Nicholas Mutu (Delta), Ukodhiko Jonathan (Delta), da Ezechi Nnamdi (Delta).
Daga Jihar Akwa Ibom kuwa, Idem Uyime, Esin Etim, Paul Ekpo, Uduak Odudoh, Okon Bassey, Etteh Ikpong, da Mark Esset, duk ‘yan PDP tare da Emmanuel Ukpong-Udo na jam’iyyar YPP, su ma sun koma APC.
‘Yan PDP uku a Majalisar Wakilai, Ajilesoro Taofeek Abimbola, Omirin Olusanya, da Marcus Onobun su ma sun sauya sheka zuwa APC. Haka kuma, ‘yan majalisa hudu na NNPP daga Jihar Kano Kabiru Usman, Abdullahi Sani, Abdulmumin Jibrin, da Sagir Koki sun koma jam’iyyar mai mulki.
Dan majalisar PDP kadai daga Jihar Benuwe, Ojema Ojotu, shi ma ya koma APC, tare da Godwin Offiono da Akpanke daga Cross Riber, da Paul Nnamchi na LP daga Jihar Enugu.
A Jihar Kaduna kuwa, Abdulkarim Ahmed, Aliyu Abdullahi, da Sadik Abdullahi duk sun bar PDP zuwa APC. Haka kuma, ‘yan majalisar adawa shida daga Jihar Enugu da Daniel Asama daga Filato sun koma jam’iyyar mai mulki.
‘Yan PDP uku daga Jihar Katsina Balarabe Dabai, Iliyasu Abubakar, da Salisu Yusuf, su ma sun sauya sheka zuwa APC, yayin da Mansur Jega daga Kebbi ya fice daga PDP ya shiga APC.
Daga Jihar Ribers kuwa, Awaji Inombek, Boma Goodhead, Boniface Emerengwa, da dan LP Manuchim Umezurike su ma sun koma APC.
A zaman majalisa da aka gudanar a watan Disamban 2025, ‘yan PDP shida Robinson Dekor, Bob Solomon, Hart Cyril, Bictor Obuzor, Blessing Amadi, da Felid Uche sun sauya sheka zuwa APC.
A wannan shekarar kadai, ‘yan Majalisar Wakilai 27 sun sanar da sauya sheka zuwa sababbin jam’iyyun siyasa. Yayin da wasu suka shiga APC, wasu kuma sun sauya tsakanin jam’iyyun adawa.
Daga cikin su akwai Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye Aliyu Madaki, Ghali Tijjani Mustapha, Shehu Bello, Dankawu Idris, Hussain Hassan Shehu, Rabiu Yusuf, Garba Mohammed Ciroma, Tijjani Abdulkadir Jobe, da Ibrahim Mohammed, wadanda dukkansu suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC a Jihar Kano.
Sauran sun hada da Jaafaru Yakubu, Sadik Abbas Tafida, Ibrahim Mohammed, Bello Shinkafi, da Mohammed Bassi, wadanda suka bar PDP suka koma APC.
A bangarensu kuwa, Mataimakin Bulalar Marasa Rinjaye George Ozodinobi, Harris Okonkwo, da Seyi Sowunmi sun sauya sheka daga LP zuwa ADC. Haka kuma, Yaya Tongo, Mani Maishinko Katami, Abdussamad Dasuki, da Umar Yusuf Yabo sun bar PDP suka koma ADC. Akanni Clement Ademola da Oladebo Lanre Olomololaye su ma sun sauya sheka daga PDP zuwa Accord Party.
Sauran masu sauya shekar sun hada da Mustapha Abdullahi da Philip Agbese da suka bar APC zuwa ADC da LP bi da bi, yayin da Ikenga Ugochinyere da Nwogu Mathew suka fice daga PDP zuwa APP.
A watan da ya gabata kadai an sake samun sauya sheka da dama. ‘Yan majalisa uku sun shiga ADC, biyu sun koma APC, biyu sun koma Accord Party, yayin da daya ya koma PDP.
Wadannan sun hada da Abubakar Abdul Buba wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC; Sani Yakubu Noma wanda ya koma daga PDP zuwa ADC; Ibrahim Mohammed Bunza wanda ya shiga APC; Mudashiru Alani wanda ya sauya daga PDP zuwa Accord Party; da Olusoji Adetunji wanda shi ma ya koma Accord Party.
Sauran kuma sun hada da Thaddeus Attah wanda ya koma daga LP zuwa ADC; Bashir Usman Zubairu wanda ya sauya daga APC zuwa ADC; da Dabid Abel Fouh wanda ya bar APC ya koma PDP.
Har ila yau, a watan Afrilu, ‘yan majalisa bakwai sun sauya sheka daga NNPP da PDP zuwa ADC da APC bi da bi. Daga cikin su akwai Sani Adamu Wakil, Umar Mukhtar Zakari, Yusuf Umar Datti, da Abdulhakeem Kamilo Ado, wadanda suka koma daga NNPP zuwa ADC.
Sauran kuwa Emeka Chinedu Martin, Kabiru Ahmadu Maipalace, da Muhammed Jajere sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
A ranar Laraba, mambobi 18 na Majalisar Wakilai sun sauya sheka daga ADC zuwa NDC da APC. Yayin da 17 suka shiga NDC, dan majalisa guda daya ya koma APC. Wasu daga cikinsu sun riga sun fice daga tsofaffin jam’iyyunsu kafin sake yin wani sabon sauyi.
Daga cikin wadanda suka shiga NDC akwai Yusuf Datti, Harris Okonkwo, Sani Adamu, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Obiageli, Oluwaseyi Sowunmi, Peter Anekwe, Zakari Mukhtari, George Olawande, Murphy Omoruyi, Umezuruike Manuchim, Emeka Idu, Jese Onuakalusi, Ifeanyi Uzokwe, Afam Ogene, da Kamilu Ado.
Hon. Leke Abejide, mai wakiltar mazabar tarayya ta Yagba a Jihar Kogi, ya sauya sheka daga ADC zuwa APC, inda wannan ya zama karo na farko da ya sauya jam’iyya.
Kasa da sa’o’i 24 bayan haka, Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, shi ma ya sauya sheka daga APC zuwa ADC. Wannan ma shi ne karo na farko da ya canza jam’iyya.
A ranar guda kuma, Umar Ajilo da Suleiman Richifa sun sauya sheka daga PDP zuwa ADC, yayin da Kamilu Ado da Joshua Obika suka shiga NDC.
Da wadannan sababbin sauya shekun, APC yanzu tana da kujeru 283 a Majalisar Wakilai duk da rasa dan majalisa guda daya. PDP ta ragu zuwa kujeru 27, ADC ta karu zuwa kujeru 9, yayin da NDC yanzu ke da ‘yan majalisa 19.
Majalisar Dattawa
Majalisar Dattawa ma ta shaida irin wannan yawaitar sauya sheka tun bayan rantsar da ita a watan Yunin 2023.
A lokacin rantsarwar, APC tana da sanatoci 59, PDP na da 36, LP na da 8, NNPP 2, SDP 2, yayin da YPP ke da guda 1, wanda ya bai wa jam’iyyun adawa jimillar kujeru 50 idan aka kwatanta da kujeru 59 na APC.
Sai dai hukuncin kotuna da sauya sheka sun sauya fasalin majalisar cikin sauri. A watan Oktoban 2023, Kotun Daukaka Kara ta soke zaben Abubakar Ohere (APC, Kogi ta Tsakiya), lamarin da ya kai ga rantsar da Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP) a ranar 2 ga Nuwamban 2023.
Haka kuma, an maye gurbin Darlington Nwokocha na LP da Austin Akobundu na PDP bayan hukuncin kotu.
A wani babban sauyi kuma, marigayi Sanata Ifeanyi Ubah ya sauya sheka daga YPP zuwa APC, wanda hakan ya kawo karshen wakilcin YPP a Majalisar Dattawa.
A shekarar 2025, bayan jerin sauya sheka da dama, APC ta kara yawan kujerunta zuwa 75, yayin da PDP ta ragu zuwa 26, LP zuwa 4, APGA zuwa 2, yayin da NNPP da SDP suka rage da kujera 1 kowacce.
Sanatoci tara, ciki har da Aminu Tambuwal, Enyinnaya Abaribe, Bictor Umeh, da Ireti Kingibe, daga baya sun sauya sheka zuwa ADC, wanda hakan ya sake sauya tsarin ‘yan adawa a majalisar.
A ranar Larabar da ta gabata, Sanata Rufai Hanga ya sauya sheka daga NNPP zuwa NDC, yayin da Sanata Ibrahim Mustapha ya sauya daga PDP zuwa ADC. Dukkansu sun yi sauya shekarsu ta farko ne.
A wani sabon sauyi kuma, Abaribe da Umeh daga baya sun sake sauya sheka zuwa LP da NDC bi da bi.
Wannan al’amari ya tayar da hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, kungiyoyin fararen hula da masu sharhi, wadanda ke gargadin cewa karuwar rinjayen APC na iya raunana tsarin duba da daidaita iko a dimokuradiyya.
‘Yan majalisar adawa sun bayyana “sabani da ba za a iya sasanta shi ba” da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyunsu a matsayin dalilan sauya shekarsu, yayin da wasu kuma suka danganta hakan da goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Jagoran marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Kingsley Chinda, ya soki sauya shekar tare da kira da a ayyana kujerun wadanda abin ya shafa a matsayin wadanda babu kowa a cikinsu bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Yawaitar sauya sheka zuwa jam’iyya na barazana ga dimokuradiyyar Nijeriya
Kungiyoyin fararen hula, ciki har da Yiaga Africa da Cibil Society Legislatibe Adbocacy Centre (CISLAC), tare da masu sharhin siyasa da malamai, sun yi gargadi cewa yawaitar sauya shekar ‘yan majalisa a Nijeriya na barazana mai tsanani ga dimokuradiyya. Sun ce hakan na raunana adawa da kuma rage amincewar jama’a ga tsarin zabe.
Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, Enyinnaya Abaribe, ya bayyana wannan al’amari a matsayin mai hadari ga mulkin dimokuradiyya, inda ya ce yana iya haifar da wani nau’in mamayar siyasa. Ya ce: “Wannan na iya zama bala’i ga Nijeriya. Bambancin ra’ayi a siyasa shi ne ke tabbatar da dimokuradiyya.”
Haka kuma Yiaga Africa ta yi gargadi cewa sauya shekar na nuna raunin siyasar akida da kuma rashin ingantaccen tsarin cikin gida a jam’iyyu. Daraktan Zartarwa na kungiyar, Samson Itodo, ya shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa ci gaba da sauya shekar ‘yan majalisa da gwamnoni daga jam’iyyun adawa zuwa APC mai mulki na haifar da damuwa kan lafiyar tsarin jam’iyyu da dama a kasar.
Ya ce: “Jam’iyyu su ne kayan aikin dimokuradiyya, kuma idan ‘yan siyasa na sauya jam’iyya ba tare da dalilin akida ko manufofi ba, hakan na kara rage amincewar jama’a da raunana lissafin rikon amana. Sauya shekar na nuna cewa siyasa ta fi karkata ga muradin kai da cin moriya fiye da hidimar jama’a.”
Shugaban CISLAC kuma jagoran Transparency International Nigeria, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce sauya shekar na rage amincewar masu zabe da kuma raunana aikin sa ido na majalisa. Ya ce: “Idan ‘yan majalisa sun sauya sheka, suna tauye amanar da masu zabe suka ba su. Yana raunana sa ido, yana mayar da hankali daga yin dokoki zuwa neman tsira a siyasa, har ma yana iya mayar da majalisa tamkar ‘rubber-stamp’.”
Ya kara da cewa wannan yanayi na iya haifar da cin hanci, raunana jam’iyyun adawa, da kuma lalata amincewar jama’a da gwamnati.
Shi ma Daraktan CREAP Africa Initiatibe, Sylbanus Udoenoh, ya bayyana sauya shekar gwamnoni da sanatoci zuwa APC a matsayin alamar damuwa ga lafiyar dimokuradiyyar Nijeriya. Ya ce wannan na rage karfin adawa da kuma fadada rinjayen APC a majalisa.
Ya kuma soki kalaman da aka danganta da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, wadanda suka nuna farin ciki da rage yawan sanatocin adawa. Ya ce: “Rinjayen APC ba zai maye gurbin bukatar gasa da lissafin rikon amana ba. Sauya sheka ya kamata ya kasance bisa akida da manufofi, ba don tsira a siyasa ko neman gata ba.”
Sauya shekar jam’iyya a matsayin yaudarar siyasa
Daraktan Zartarwa na Grassroots Centre for Rights and Cibic Orientation (GRACO), Armsfree Ajanaku, ya bayyana sauya shekar ‘yan siyasa a matsayin hujja da ke nuna “siyasa ba tare da akida ba.”
Ya ce: “Daukar amanar da masu zabe suka ba wata jam’iyya a mika ta ga wata jam’iyyar daban ya zama yaudara ta siyasa. ‘Yan majalisa da ke sauya sheka suna shiga cikin rikicin dabi’a, kuma hakan na hana samun ingantaccen shugabanci.”
Sakataren Kasa na Coalition of United Political Parties (CUPP) kuma tsohon Shugaban Kasa na Inter-Party Adbisory Council (IPAC), Chief Peter Ameh, ya yi gargadin cewa karuwa rinjayen APC na iya raunana tsarin duba da daidaita iko da kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.
Ya ce: “Wannan rinjayen zai kara karfafa hadin kan APC, amma a zahiri zai iya lalata tsarin duba da daidaita iko a majalisa.”
A cewarsa, Majalisar Dokoki na iya rikidewa zuwa majalisa mai amincewa da duk abin da zartarwa ta kawo, idan aka ci gaba da raunana ‘yan adawa. Ya ce: “Da irin wannan rinjaye, Majalisar Dattawa na fuskantar barazanar rasa rawar ‘yan adawa wajen tabbatar da lissafin rikon amana, tattaunawa mai karfi da kuma sa ido kan zartarwa. Wannan na iya mayar da majalisa tamkar mai amincewa da umarnin gwamnati kawai.”
Ya kara da cewa: “Nijeriya na bukatar majalisa mai karfi wadda ke wakiltar mabanbantan ra’ayoyi kuma ke sa ido kan gwamnati.”
Shi ma malamin kimiyyar siyasa a Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, Dr. Christian Okeke, ya danganta sauya shekar da “siyasar bukatun yau da kullum”, wadda ta fi karkata ga muradin kai da neman riba.
Ya ce: “Rinjayen APC a Majalisar Dattawa za a iya fahimtarsa ta hanyar siyasar ‘bread-and-butter’ wato siyasar tsira da neman amfanin kai.”
Ya bayyana cewa ‘yan majalisa da ke sauya sheka don ribar kansu ba za su iya kalubalantar matakan da ke goyon bayan jam’iyyar mai mulki ba. Ya ce: “Ba zai yiwu ka shiga inda ake cin abinci saboda bukata, sannan ka fara girgiza teburin abincin ba. Tsoron rasa gata zai sa mutane su yi shiru.”
Okeke ya kuma nuna damuwa kan raguwar ingancin aikin majalisa, raunin tattaunawa da kuma rashin tsauraran sa ido. Ya ce: “Muna ganin al’amura masu damuwa inda tattaunawa ba ta da karfi, tantancewa ba ta cika ba, kuma rashin mutunta dokokin da aka zartar na karuwa.”
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tashi su kare dimokuradiyya tare da dora wa shugabanni alhaki, maimakon barin nauyin kawai ga kungiyoyin fararen hula. Ya ce: “Dole ne jama’a su fahimci cewa hadin kai da muryar jama’a ne zai iya ceton kasa, ba wai barin aikin ga wasu kalilan ba.”
Ya kara da gargadin cewa raunana jam’iyyun adawa na iya lalata shugabanci mai lissafi da amsawa. Ya ce: “Abin da ke faruwa yana rage ingantaccen shugabanci na gaskiya da amsawa, wanda shi ne ginshikin dimokuradiyya ta gaskiya.”















Discussion about this post