ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Albishir Na Cin Gajiyar Hannun Jarin Da Aka Zuba A Fannin Kiwo A Nan Kusa

by Abubakar Abba
9 months ago
Gwamnatin

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, bisa haɗar da ake ci gaba da yi da kuma zuba jari a fannin kiwon dabbobi a ƙasar nan, nan ba da jimawa za a fara samun sakamako mai kyau.

Wannan na zuwa ne, biyo bayan buɗe sabuwar majalisa ta ƙasa ta bunƙasa fannin kiwon dabbobi (NCLD) da aka gudanar a  Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Idi Mukhtar Maiha, Ministan Ma’aikatar Bunƙasa Fannin Kiwon Dabbobi ya shaida wa tawagar da suka fito daga fannin kiwon dabbobi da kuma sauran masu zaman kansu a fannin cewa, an faro wannan aikin ne a shekarar da ta gabata, wadda aka mayar da hankali, musamman a ɓangaren kasuwanci; domin samun riba a fannin samar da Madarar Shanu da kiwon Kajin gidan gona da sauransu.

ADVERTISEMENT
  • Jihar Zamfara Na Da Rinjaye A Fannin Noma, In Ji Gwamna Lawal A Taron AIF Na Morocco
  • Jihar Kaduna Ta Ƙulla Yarjejeniyar Dala Miliyan 200 Da Ƙasar Sin Don Bunƙasa Noman Zamani

Ya ce, tuni abokan haɗakar suka goyi bayan aikin samar da Madarar Shanu da ƙara ƙarfafa zaman lafiya da kuma rage ƙalubalen sauyin yanayi a ɓangaren kiwon dabbobi a ƙasar.

Ya ƙara da cewa, wannan ɗaukin ga fannin zai taimaka wajen ƙara samar da kuɗaɗen shiga ga waɗanda suke a fannin da ƙara kula da lafiyar dabbobi tare da kuma rage yawan afkuwar rikice-rikice a tsakanin manoma da Fulani Makiyaya a ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

Maiha ya ci gaba da cewa, sabuwar majalisar za ta kuma taimaka wajen ƙara ƙarfafa haɗaka da jawo ra’ayin masu zuba hannun jari da kuma ƙara samar da wadataccen abinci a ƙasar.

Shi kuwa a nasa jawabin a wajen taron, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da cewa; fannin kiwon dabbobi, ba sabon abu ba ne; don an jima ana yin sa a jihar, musamman domin haɓaka tattalin arziƙin jihar.

Fintiri, wanda Mataimakiyarsa Kaletapwa George Farauta, ta wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa; shekaru da dama jihar ta kasance tana da Ma’aikatar Kiwon Dabbobi.

Gwamnan ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wa Adamawa, kan ƙoƙarin da take ci gaba da yi na aikin samar da Rugar Kiwon Dabbobi na zamani.

Shi kuwa a saƙonsa a wajen taron, Farfesa Attahiru Jega, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman a ɓangaren samar da sauye-sauye a fannin kiwon dabbobi, ya yi fatan aikin zai taimaka wajen ƙara bunƙasa tattalin arziƙin masu kiwon dabbobi da kuma magance rikice-rikicen manoma da Fulani Makiyaya.

Jega, wanda Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Kiwon Dabbobi, Chinyere Ijeoma Akujobi, ta wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa; buɗe wannan majalisar ta ƙasa, tamkar buɗe wani sabon babi ne a fannin kiwon dabbobi a ƙasar.

Gwamnatin
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Next Post
Nazarin CGTN: An Bukaci Amurka Ta Sa Japan Ta Janye Kalaman Takala Da Ta Furta

Nazarin CGTN: An Bukaci Amurka Ta Sa Japan Ta Janye Kalaman Takala Da Ta Furta

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.