ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Yunƙuro Don Daƙile Ɓarkewar Sabuwar Cutar Da Ke Kama Shanu

by Abubakar Abba
5 months ago

Ma’aikatar bunƙasa kiwon dabbobi ta ƙasa, yunƙuro domin daƙile ɓullar wata mummunar cuta da a turance ake kiran ta da ‘Boɓine’ da ke kama shanu a ɗaukacin faɗin ƙasar nan. Ta yunƙuro ɗin ne, ta hanyar ƙaddamar wata tawaga da za ta mayar da hankali, wajen daƙile yaɗuwar cutar zuwa ga shanun da ke ɗaukacin faɗin ƙasar.

Babban ministan ma’aikatar, Idi Mukhtar Maiha, ya sanar da cewa; cutar ta kasance wata babbar annoba, wadda kuma ke ci gaba da shafar fannin bunƙasa kiwon shanu a ƙasashen duniya. A cewarsa, an ƙiyasta cewa; ta harbi shanu aƙalla miyan 54.5 a faɗin wannan ƙasa.

  • ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Kazalika, an gabatar da wasu alƙaluma da ke nuna irin mummunar ɓarnar da ta yi.

ADVERTISEMENT

A hukumance, aƙalla guda 131 ta ɓarke, inda ta bazu zuwa jihohi 17, inda alƙaluma suka nuna cewa; an samu bazuwar ɓarkewarta ne, sakamakon giɓin da aka samu na rashin sanya ido da kai rahoto ga tsarin gudanar da kiwon shanu a ƙasar.

Cutar dai, na rage ƙimar da ya kamata a samu daga shanu da kuma shafar samar da namansu da madara mai yawa, wadda kuma ke janyo mutuwar shanun da suka kamu da ita.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Maiha ya zayyano wasu daga cikin hanyoyin da ke sanyawa shanun ke kamuwa da cutar da suka haɗa da yadda suke bin hanyoyin da mutane ke wucewa, ƙarancin yi wa shanun allurar rigakafin kare su daga kamuwa da cututtuka da kuma rashin samar da tsarin saurin gano cututtukan da ke harbin shanun.

Ya yi gargaɗin cewa, idan har ba a samar da ɗauki a kan lokaci ba, cutar za ta ci gaba da yaɗuwa, wanda hakan zai haifar wa masu kiwon shanu a ƙasar nan babbar asara

Sabuwar tawagar da aka ƙaddamar, za ta samar da tsarin kare yaɗuwar cutar tare da tabbatar da ganin an samar da shirin yi wa shanu allurar rigakafin kare su daga kamuwa da cututtuka, musamman na zmani.

Ma’aikatar ta kuma buƙaci a yi haɗaka da ɓangaren kiwon shanu masu zaman kansu, musamman don cimma burin daƙile bazuwar cutar a matakin jihohi da kuma na tarayya.

A nata jawabin, babbar sakatariya a ma’aikatar, Chinyere Ijeoma Akujobi ta ce, an samar da wannan ɗaukin ne da nufin saita fannin kiwon dabbobi a ƙasar tare da kuma ƙarfafa wa masu kiwon shanu guiwa a dukkanin faɗin ƙasar.

Wasu daga cikin hukumomin kula da lafiya na ƙasa da ƙasa, kamar hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO), sun ayyana bayar da goyon bayansu, inda suka bayar da shawarar ƙarfafa sanya ido kan ɓullar duk wata cuta da ke harbin shanu a Nijeriya.

Sauran masu ruwa da tsaki a fannin kiwo da suka haɗa da Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Ƙasa, wato Miyetti Allah da kuma hukumar kula da Lafiyar Dabbobi ta Duniya, duk sun nuna sha’awarsu ta taimakawa, domin daƙile bazuwar cutar.

Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Yadda Abubakar Dantsoho Ke Bunƙasa NPA A Tsanake

Yadda Abubakar Dantsoho Ke Bunƙasa NPA A Tsanake

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.