ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gidajen Abinci Ke Wasa Da Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Ruɓaɓɓen Tumatir

by Idris Aliyu Daudawa
2 months ago

Amfani da ruɓaɓɓen Tumatari abin sai ƙaruwa yake yi a faɗin tarayyar Nijeriya duk da yake masana harkar lafiya sun jan kunnen mutane domin kuwa yin hakan na da babbar matsalar da za ta shafi lafiya.

Gaba ɗayan ƙasar Nijeriya, masu sayen abinci daga wajen masu dafawa da kuma masu sayar da kayan abincin, da gangan ne suke sayen Tumatarin da ya lalace, wanda ko waɗanda aka sayar da su a farashi mai rahusa.

Jaridar ƙarshen mako ta Daily Trust ta gano cewar da gangan ne waɗansu masu  sayen kayan miya lokacin da dare ya fara yi, inda za su saya da arha daga wurin masu sayarwa waɗanda su dama sun ƙosa su sayar da arha, saboda suna sayar da Tumatarin da zafi ya sa a fara lalacewa.

ADVERTISEMENT

Tumatarin da ya fara lalacewa na ɗauke shi ka shi biyu:  na farko waɗanda suka fara lalacewa kaɗan da kuma na biyu waɗanda sun daɗe eda lalacewa. Masu saye sun fi son wanda ya fi lalacewar domin ya fi atrha, musamman ma idan mutum zai saya da yawa.

Masu sayar da abinci na bakin titi da kuma ƙananan masu gidan sayar abinci sun fi son waɗancan nau’in Tumatarin da ya lalace.

LABARAI MASU NASABA

Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)

Wakilanmu a sassa daban daban na Nijeriya sun bankaɗo yadda aka maida hankali akan sayen Tumatarin da ya fara lalacewa suka kuma tattauna da masana,waɗanda su kuma suka yi jan kunne dangane da irin matsalar lafiyar da za a iya samu idan aka ci gaba da yin hakan.

A jihar Legas Wakilinmu ya bada rahoton yadda ake irin wannan mugun abu na sayen Tumatarin da ya fara lalacewa a kasuwar mil sha biyu, da ta kasance babbar kasuwa ta sayar da kayan abinci ta kuma kasance daga can ne ake rarraba kayan abincin a faɗin Nijeriya da kuma wasu sassa na yammacin Afirka.

Makon da ya gabata ne, aka saki wani bidiyo inda aka kama wata mata a kafar sadarwa ta zamani,da ake zargin tana ƙoƙarin ta niƙa ko markaɗa Barkono ko Tattasan da ke da tsutsotsi a cikin kasuwar.

Faruwar ko aukuwar hakan ce ta sa Gwamnatin Jihar Legas ta fitar da wani bayani na  jan kunnen al’umma da su daina amfani da Tumatarin da ya lalace kamar irin yadda wasu abubuwa suka fara rayuwa a kan shi,  wanda yin hakan na iya sa a kamu da cututtukan da suke da alaƙa da mu’amala da nau’oin Tumatarin.

Yadda ake samu ƙaruwar lalacewar Tumatari

A Legas da wasu sassan kudu maso gabas ,Tumataren da suka lalace ko  Barkonon da Atarugu da suka ruɓe ana kiransu  “esa.”

Kamar dai kayan da su kan iya lalacewa bayan sun ɗauki wani lokaci, Tumatari da Barkono suna fuskantar matsalar asara lokacin da suka nuna, ɗaya daga matsalolin da ke damu kayan amfanin gona kamar yadda kamar yadda hukumar (OTACCWA)ta bayyana, irin asarar da ake yi ta kai ta Naira Tiriliyan 3.5 kowace shekara.

Ba tare da wurin da za a ajiye su mai sanyi ba kamar cikin Firig kamar yadda ya dace, kaya masu saurin lalacewa kamar su kayan marmari da kuma ganye suna lalacewa da sauri,  kai har ma ya kasance amfani da su zai iya smar da cuta, su kuma rasa fa’aidar amfanin da za su iya yi.

Binciken da  Wakilinmu ya yi ya gano wasu Tumatari da Barkono idan har suka fara samun matsala lokacin da aka girbe su, tun daga wancan lokacin ne suke fara lalacewa a lmarin da akan kira su “esa”  a wasu wuraren da Yarabawa suke da suka haɗa da Legas.

A shekarun baya,irin su kayan da suka lalace ana yarda su ne, ko kuma a a sayarwa d gida da yafi  kowa talauci. Sai dai kuma saboda irin matsin halin da ake ciki sanadiyar llacewa tattalin arziki yana sam mutane da yawa suna amincewa da “esa.”

Bayan waɗanda su lamarin nasu kan  yadda ake amfani da shi  a wasu gidaje, an kama masu abincin sayarwa suna amfani da Tumatari ko kuma biya an kama hana su ne amfani ne da Tumatarin da ya ɓaci wani wari ya ke yi, ayi miya da su, lamarin da daga ƙarƙshe zai iya cutar al’umma.

Tsadar Tumatari Maikyau Wata abu ce

Wasu masu sayen Tumatarin da masu abincin sayarwa sun yi magana da Jaridar Trust ta ƙarshen mako sun ɗora alhakin yadda farashin Tumatari da Barkono suke  ta ƙaruwa saboda yadda suka maida hankalinsu wajen sayaen ruɓaɓɓen Tumatarin.

An samu bayanin cewa Buhun Tumatari mai kilo 50, wanda ake sayar da shi tsakanin Naira 35,000 zuwa Naira 40,000 watan da ya gabata,  yanzu ana sayar da shi tsakanin Naira 115,000 zuwa Naira 125,000.

A wasu wurare ne, ƙaaramin kwandon Tumatari  ana sayar da shi  Naira 2,000 a watan da ya gabata yanzu ana sayar da shi  Naira 6,000.

Waɗanda suka tattauna da Wakilanmu sun ce yawancin masu abinci yanzu suna sayen ruɓaɓɓen Tumatarin ne saboda kuɗin da suke dasu ba za su iya saiyen Tumatarin mai kyau ba yanzu suna sayen Tumataren da suka lalace.

“Mutane suna sayen shi hakan Muna ganinsu a Kasuwa. Mutanen da suke sana’ar sayar da abinci suna amfani da shi. Amma ni bani amfani da shi,” cewar wadda take abincin sayarwa, Mrs Desola Adelabi.

Mrs. Adelabi  ta ƙara jaddada cewa: “Lokacin da Tumatari da Barkono suka kasance da tsada, shi ma farashin esa yana ƙaruwa. Yana zuwa a nau’oi daban- daban.”

Sai dai kuma duk da hakan ta nuna rashin jin daɗinta,saboda lamarin na iya shafar lafiya musamman idan aaka yi amfani da Tumatarin da ya lalace wajen yin miya lokacin girkin abinci.

“Esa  bai da kyau idan ana buƙatar kula da lafiya ne.Saboda baya bada ɗanɗano mai armashi  masu sayen abinci ba za su sake dawo ba idan sun gane an yi amfani ne da kayan miyar da suka ruɓe wajen shirya abincin.

“Idan ka zo nan ka ci jar miya kana jin bata da ɗanɗano za ka sake dawowa kamar dai yadda ta yi tambaya’’.

Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Sarakunan Da Suka Yi Wa Turawan Mulkin Mallaka Turjiya A Nijeriya
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Kiwon Lafiya

Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina

July 11, 2026
Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)
Kiwon Lafiya

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)

June 20, 2026
Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)
Kiwon Lafiya

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

June 13, 2026
Next Post
Gwamnan Kwara Ya Roƙi Tinubu Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Zuwa Dubu Ɗari

Gwamnan Kwara Ya Roƙi Tinubu Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Zuwa Dubu Ɗari

LABARAI MASU NASABA

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.