ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu

by Idris Aliyu Daudawa
3 months ago

A duk yayin da mace ta ɗauki ciki, tana samun kanta a wani irin yanayi maras daɗi har sai ta haihu, don haka; batun juna biyu ba ƙaramin al’amari ba ne, sakamakon zuwa da ya ke yi da haɗari iri daban-daban.

Wasu matan, bayan sun ɗauki ciki ne suke haɗuwa da cututtuka da dama; kamar ciwon zuciya, ciwon siga, hawan jini da sauran makamantansu. Don haka, a nan ya kamata a sani cewa; babu yadda za a yi mace ta ɗauki ciki ba tare da jikinta ya canza ba.

Wannan dalili ne ya sa, idan nauyin mai juna biyu bai kai yadda ake buƙata ba, sai a ja hankalinta ta yi wasu abubuwa da za su sa nauyin nata ya ƙaru, haka nan; idan nauyin nata ya yi yawa, musamman ga mata masu ƙiba; nan ma a kan ja hankalinsu su yi ƙoƙari wajen rage nauyin nasu.

ADVERTISEMENT

Saboda haka, da zarar an ce mace na da ciki; abubuwa da dama na sauya yanayin jikinta, wata ta ƙara ƙiba, wata ƙuraje su feso mata a fuska, wata kalar fatarta ta canja; wani wajen ya yi fari wani ya yi baƙi, wasu su yi ta samun ƙananan cututtuka, wasu amai, wasu kuma saboda damuwa su yi ta faman kuka ba tare da an yi musu komai ba.

Don haka, ya zama wajibi maza su riƙa yi wa matansu uzuri a yayin da suke ɗauke da juna biyu da kuma bayan sun haihu. Misali, babu yadda za a yi a ce mace ta ɗauki ciki tsawon wata tara tana tare da shi, sannan bayan ta haihu a kuma yi tunanin cewa; wannan ciki nata zai dawo kamar yadda yake a baya.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Har ila yau, maza da dama na da irin wannan ɗabi’a ta tsangwamar matansu, sakamakon yadda jikinsu yake sauyawa bayan sun haihu, musamman ganin yadda cikinsu yake yin shaida ko tattarewa ko kuma girma ta hanyar samun tumbi.

Irin wannan tsangwamar da maza ke yi wa mata, ko kaɗan bai dace ba; domin kuwa wasu matan na shiga cikin mummunan hali tare da takurawa kansu, ta hanyar kashe kuɗaɗensu don ganin sun samu maganin wannan matsala, wadda babu yadda za a yi a iya magance ta, tunda halittar ce a haka; kamar shekaru ne duk yadda za ka yi, babu wata dabara da za ta iya ɓoye su.

Saboda haka, mata ya kamata ku kiyaye; ku daina zuwa kuna kashe kuɗaɗenku babu gaira babu dalili, amma babu wani magani da za a baki ki sha tumbinki ya tafi, wasu sai su sha magani su je su yi ta zawo haka kawai, wai don tunbinsu ya ragu.

A nan, muna ƙara jan hankalin maza; su ji tsoron Allah su riƙa tausaya wa matayensu, musamman bayan sun samu juna biyu sun haihu. Sannan ku tuna cewa, wannan ciki da yake canja wa mata wasu ɓangarori na jikinsu, ku ne kuke yi musu ba daga gidajensu suke zuwa da shi ba.

Daga rumbun Dakta Na’ima Abubakar

Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Next Post
Sin Ta Kalubalanci Kwamitin Sulhun MDD Da Ya Gyara Ko Soke Takunkumin Da Aka Kakabawa Sudan Ta Kudu

Sin Ta Kalubalanci Kwamitin Sulhun MDD Da Ya Gyara Ko Soke Takunkumin Da Aka Kakabawa Sudan Ta Kudu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.